Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba
Published: 25th, October 2025 GMT
Mahalifinsa, Chief Thomas Osen Ekpemupolo, da mahaifiyarsa, Mrs. Ewe Ekpemupolo, sun rayu cikin al’umma mai arziƙin mai a lokacin da ake tsaka da nema a yi wa yankinsu adalci. Daga cikin wannan rikicewar ya taso mutum wanda daga baya zai zama ɗan gwagwarmayar Niger Delta don neman daraja, adalci, da samun ikon gashin kai.
A tsakiyar shekarun 1990, arzikin mai na Nijeriya yana samu wadata a wasu wurare amma ya zama ana barin al’ummomi masu arziƙin mai cikin talauci, gurɓawa, da kuma rashin muryar magana. Ga matashin Tompolo, yin shiru wannan bai zama zaɓi ba.
Gwagwarmaya Da Juyin Juya Hali
A Ƙaramar Hukumar Kudu maso Yammacin Warri, daga Ogbe-Ijoh (garin Ijaw) zuwa Ogidigben (garin Itsekiri), an yanke shawarar da ta haifar da tashin hankali na ƙabilanci kuma ta ƙwace ikon alama daga wata ƙabilar baki ɗaya.
Tompolo ya sayar da kusan duk abin da yake da shi, gidaje uku, motar Mercedes Benz Ɓ-Boot, da jiragen ruwa da dama, don samar da kuɗi ga yakin neman gyara wannan rashin adalci. Jarumtarsa ta ja hankalin mutane, tana kuma haifar da tsoro.
A ƙarshe, a ƙarƙashin Shugaba Olusegun Obasanjo, gwamnatin tarayya ta janye shawarar, ta mayar da hedkwatar zuwa Ogbe-Ijoh. Wannan nasara ce ta farko a fili, ba ta tashin hankali ba, ta jajircewa.
A cikin shekarun da suka biyo baya, Tompolo ya fito a matsayin muryar jagoranci a gwagwarmayar Neja Delta. A matsayin wanda ya kafa ‘Moɓement for the Emancipation of the Niger Delta’ (MEND), ya ƙalubalanci tsarin tarayya wanda ke ƙwace biliyoyi daga ƙasar yankin amma ba ya mayar da komai. Saƙonsa yana da sauƙi amma mai ƙarfi ne: “Ba mu nemi yaki ba; muna neman adalci ne.”
Lokacin sauyi ya zo a shekarar 2009, lokacin da ya amince da Shirin Afuwa na Shugaban Ƙasa da marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya ƙaddamar. Duk da cin mutuncin wasu da shakku, ya ajiye makamai, yana ƙarfafa wasu su yi haka. Wannan ɗaya daga cikin ayyuka ya taimaka wajen kawo ƙarshen shekaru na tashin hankali da buɗe ƙofa ga gina zaman lafiya da tattaunawa mai tsari. Wannan shi ne farkon sauyi na mutum ɗaya da yankin baki ɗaya.
Daga Mai Ta Da Ƙayar Baya Zuwa Mai Tsara Ɗorewar Zaman Lafiya
Hannayen da da suka taɓa jagorantar jiragen yaƙi yanzu suna kula da wani sabon nau’in jiragen ruwa na ƙirƙira, samar da ayyukan yi, da kiyaye zaman lafiya. Ta hanyar Tantita Security Serɓices Nigeria Limited (TSSL), tare da haɗin gwiwa da Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL), Tompolo ya zama mai tsaron muhimman kadarorin Nijeriya: bututun mai da tashoshin ruwan gabar teku.
Tsarin Tantita ya haɗa tsarin sa ido na zamani da bayanan sirri daga cikin al’umma, wanda hakan ya rage satar mai da aikin tace mai ba bisa ƙa’ida ba (“Kpo-fire”) a faɗin Niger Delta. Waɗannan ƙoƙari sun taimaka wajen ƙara yawan fitar da man fetur na kullum a Nijeriya, haɓaka kuɗaɗen shiga na gwamnati, da kuma dawo da amincewa da tsaron da al’umma ke jagoranta.
Amma ribar tattalin arziki rabin labari ne kawai. Fiye da mutane 3,000 daga cikin tsofaffin masu tayar da ƙayar baya da matasan yankin sun samu aikin doka mai ɗorewa ƙarƙashin kulawar Tantita.
Da yawa daga cikin waɗanda da suka ɗauki tawaye a matsayin hanya ɗaya ta samun muhimmanci, yanzu suna sanye da kayan aikin da ke da ma’ana. A cikin rafukan da da ake jin ƙarar bindigogi, yanzu ana jin ƙarar injinan jiragen ruwa masu ɗaukar ƙungiyoyin masu sa ido — hujja ce cewa zaman lafiya na iya kawo riba.
Faruwar Samun Nasarar Jin Ƙai
Nasarar da ta fi kowace girma ga Tompolo ita ce ta aikin jin ƙai cikin natsuwa.
Ta hannun Tompolo Education Foundation, yana ba da tallafin karatu da horas da malamai ga ɗaruruwan ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi a faɗin yankin Neja Delta.
A watan Maris 2025, cibiyar ta ƙaddamar da shiria gina ƙwarewa ga ‘yan NYSC a yankin Warri domin ƙarfafa sababbin malamai da za su koyar a al’ummomin da ba su da wadatattun malamai.
Lokacin da Jami’ar Kiwon Ruwa ta Nijeriya (Nigeria Maritime Uniɓersity), Okerenkoko, ta gudanar da bikin yaye ɗalibai na farko, Tompolo ta hannun cibiyarsa ya ba da kayan ɗaki masu darajar Naira miliyan 30 don ƙarfafa muhalli na koyo.
Wannan ba taimako kawai ba ne, wani yanayi ne da ya tabbata: Tompolo ɗin da a da ake kira ɗan tawaye, yanzu shi ne ke zuba jari a cikin sabunta ilimin zamani.
Jin Ƙaunarsa Ta Kai Har Ga Fannin Kiwon Lafiya
A shekara ta 2012, ya biya kuɗin gyaran asibitin Okerenkoko guda ɗaya da darajar kuɗin suka kai naira miliyan 20.
Haka kuma, yayin ambaliyar ruwa ta shekarar 2022, Tompolo ya ba da kayan tallafi na darajar ta kai Naira miliyan 150 ga waɗanda ambaliyar ta shafa a jihohin Bayelsa da Delta, da Riɓers.
A gefe guda, Cibiyar Al’adu ta Izon (Izon Cultural Heritage Centre – ICHC) da Ƙungiyar Ayyukan Al’umma ta Izon (Izon Community Serɓice Ɓolunteers – ICSƁ) sun zama tushen farfaɗo da al’adu da ƙarfafa hidima ga al’umma.
Ta hanyar waɗannan ƙungiyoyi, Tompolo yana tunatar da matasan Ijaw cewa hidima ita ce mafi muhimmanci, kuma asalin bayyana kai ba wani tsohon abu ba ne tushen rayuwa ne mai ƙarfi da ci gaba.
Girmamawa Daga Jami’ar Maritime
Sauyin da ya samu daga kasancewa kwamandan ’yan tawaye zuwa zama mai daidaita ƙasa ya jawo masa yabo daga ko’ina.
A shekarar 2023, Jami’ar Maritime ta Nijeriya ta ba shi digirin girmamawa saboda gudunmawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.
A shekara ta gaba kuma, Ƙungiyar Mutanen Ijaw ta Birtaniya da Ireland (Ijaw People’s Association – IPA) ta ba shi kyautar “Izon-Ebi Dou Keme” wato “Jagora mai kishin ci gaban al’ummar Ijaw.”
A yayin bikin ba da lambar girmamawar, Francis Akpanari, shugaban IPA, ya bayyana shi a matsayin “halattaccen ɗan Ijaw, wanda ya zama wata gada tsakanin rikici da haɗin kai.”
Amma wataƙila gaskatacciyar girmamawa ta fito ne daga al’umma kanta.
A cikin wata buɗaɗɗiyar wasika da ta bazu a kafafen sada zumunta, Oyinke Preye Tales, wata matashiya daga kogunan yankin, ta rubuta da motsin rai:
“Ba kawai shugaba ba ne kai, babban Cif ne kai, ƙarfi ne na yanayi, mai kare mutanen Ijaw da yankin Neja Delta.
Ka tsaya tsayin daka lokacin da da yawa suka durƙusa. Ka ɗauki nauyin fafutukar mu har da haɗarin rayuwa.
Saboda kai, ina tafiya ina ɗaga kai da alfahari.”
Wannan yabo ne na bazata daga sabon ƙarni wanda ba ta ganin yankin Neja Delta a matsayin wurin baƙin ciki da lalacewa, sai dai a matsayin wurin farfaɗo da sabuwar rayuwar abin da aka samu, a wani ɓangare, saboda zabin da ya yi da jagorancin da ya nuna.
Rayuwa Tasa, Manufa ta Jama’a
Duk da shahararsa da tasirinsa a siyasa, Tompolo har yanzu yana rayuwa cikin sauƙi da tawali’u. Yana zaune cikin natsuwa a Jihar Delta tare da matarsa Ɓictoria da ’yarsa Mary, yana guje wa nuna isa da shahara, yana fifita tunani da tunawa.
Masu kusanci da shi suna bayyana shi a matsayin mutum mai cike da natsuwa, wanda har yanzu yake ɗauke da raunukan yaƙin da ya shuɗe, amma yana samun warkewa ta hanyar zaman lafiya da ya taimakawa wajen gina al’umma.
A Wajen Mutanensa, Shi Ne Ibe-Ebidouwei Na Al’ummar Ijaw “Wanda Ke Kawo Alheri Ga Jama’a.”
A wajen Nijeriya kuma, shi hujja ce cewa sasantawa ba rauni ba ce, kuma cewa tuba da aka haɗa da manufa na iya zama babban arzikin ƙasa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: yankin Neja Delta zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba
Tom Barrack jakadan Amurka na musamman a kasar Siriya ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta yi kokarinkifar da gwamnatin JMI a baya har sau biyu amma ta kasa yin haka.
Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Barrack yana fadawa wani kamfanin dillancin labaran UAE a ranar jumma’an da ta gabata, ya kuma kara da cewa daga shekara ta 1946 ya zuwa yau gwamnatin Amurka ta yi kokarin kifar da gwamnatoci 93 biyu daga cikinsu a kasar Iran ba tare da samun nasarara ba. Amma akwai da dama wadanda suka sami nasara.
Ya ce kafin Trump ya hawo kan kujerar shugabancin Amurka mun yi kokar kifar da gwamnatin kasar har sau biyu ba tare da samun nasara ba. Barrack dai har’ila yau shi ne jakadan Amurka a kasar turkiyya.
Wannan bayanin yana zuwa ne watanni 6 da yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka kaiwa kasar wato daga ranar 13 ga watan Yuni zuwa 24 ga watan. Inda sukakashe Iraniyawa 1,064 suka kuma kaiwa fararen hula da dama hare-hare.
A cikin yakin ne gwamnatin Amurka ta kai hgare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran a fordo Naqtanz da kuma Esfahan.
Iran ta sami nasara a wannan yakin ne bayan ta kai hare-hare masu karfi kan HKI da dama, hare-haren dasuka tabbatar da cewa Iran zata iya shafe HKI da yayin ya ci gaba. Haka ma Iran ta kai hare-haren kan sansanon sojojin Amurka mafi girma a gabas ta tsakiya dake Al-udaita na kasar Qatar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa December 7, 2025 Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya December 7, 2025 Venezuela: Ba Mu Tsoron Kaudin Amurka Na Wuce Gona Da Iri December 7, 2025 Iran Ta Zama Zakaran Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21 December 7, 2025 Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi December 7, 2025 Dubban Mutane Suna Guduwa Daga Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada December 7, 2025 Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan December 6, 2025 Iran Da Masar Sun yi Kira Da Kawo Karshen Keta Hurumin Gaza da Labanon da Isra’ila ke yi December 6, 2025 Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba December 6, 2025 Gwamnatin Najeriya Za ta Karbi Sabon Bashin Dala Miliyan 500 A Bankin Raya Kasashen Afrika December 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci