Aminiya:
2025-10-26@18:55:56 GMT

Tanka ta kife yayin da man fetur ya zube a kan titi a Neja

Published: 26th, October 2025 GMT

Wata tanka ɗauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lambata zuwa Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja, lamarin da ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin.

An gano cewa tankar, wadda ta taso daga Legas tana kan hanyarta na zuwa Kano, ta kife ne da sassafe a garin Takalafiya da ke Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja.

Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode

Wani mazaunin garin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya shaida wa Aminiya cews lamarin ya faru kimanin kilomita biyu daga garin Lapai.

Ya ce kwanan nan aka gyara hanyar NNPCL, amma hanyar ta fara lalacewa cikin ƙanƙanin lokaci.

Wani ganau mai suna Mohammed Hassan Sonmaji ya ce, saurin zuwan jami’an kashe gobara na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBUL) tare da na Hukumar Tsaro ta NSCDC ne ya taimaka wajen kauce wa mummunan hatsari a hanyar.

Ya ƙara da cewa jami’an ƙungiyar NUPENG reshen Lapai, sun isa waje don taimakawa wajen shawo kan lamarin.

An zagaye wani ɓangare da man ya zube domin gujewa aukuwar hatsari.

Da aka tuntubi Daraktan Sashen Bayani da Harkoki na Musamman na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dokta Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da cewa babu abin zai auku.

Ya bayyana cewa tankar ba ta kama da wuta ba, kuma motocin kashe gobara na jami’ar IBBUL suna tsaye a wajen don shirin ko-ta-kwana.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Faɗuwa Hatsari

এছাড়াও পড়ুন:

An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutum 25 da ake zargi da shirya auren jinsi a samamen da ta kai wani wurin shagali a jihar.

A cewar hukumar, an kama mutanen ne da yammacin Asabar a wani wurin taro da ke kan titin Hotoro Bypass a ƙaramar hukumar Tarauni.

Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno NSCDC ta yi alhinin mutuwar Kwamishinan Tsaron Gombe

Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar Hisbah mai kula da ayyuka na musamman, Sheikh Dokta Mujahid Aminuddeen Abubakar, ne ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa samamen na zuwa ne bayan bayanan sirri da hukumar ta samu daga wani mai kishin al’umma.

Ya bayyana cewa bayanan sirrin sun nuna cewa wani mai suna Abubakar Idris yana shirin auren wani matashi, lamarin da ya sa jami’an Hisbah suka bazama zuwa wurin da taron ke gudana.

Ya ƙara da cewa daga cikin wadanda aka kama akwai maza 18 da aka bayyana a matsayin ’yan daudu, da kuma mata 7 daga unguwanni daban-daban ciki har da Sheka, Yar Gaya da Kofar Nasarawa.

Dokta Mujahid ya ce a halin yanzu duk ababen zargin suna hannun hukumar, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Ya yi kira ga iyaye da su kula wajen inganta tarbiyyar ’ya’yansu, tare da roƙon jama’a da su rika sanar da hukumar Hisbah ko hukumomin tsaro idan sun ga wani abin da ke da ɗaukar hankali.

Mataimakin kwamandan ya sake jaddada ƙudirin hukumar na ci gaba da tabbatar da ɗabi’a ta gari da kare mutuncin Kano a matsayin jihar da aka sani kan ginshiƙin ladabi da ƙa’idojin addinin Musulunci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnonin Arewa Sun Jajanta Wa Jihar Neja Kan Fashewar Tankar Mai
  • Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode
  • An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a Kano
  • An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa 
  • Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI
  • Hukumar NASENI
  • ABU ta musanta zargin ƙera makamin nukiliya a ɓoye
  • Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa
  • Gobara Ta Ƙone Fiye da Rumbuna 500 a Kasuwar Kano