Bangarorin Falasdinawa Sun Amince Da Shirin Gudanar Da Zirin Gaza Nan Gaba
Published: 25th, October 2025 GMT
Bangarorin Falasdinawa sun amince a birnin Alkahira kan yadda za a tafiyar da Gaza a nan gaba
Bangarorin Falasdinawa da suka yi taro a birnin Alkahira a ranar Juma’a sun sanar da amincewarsu kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi gudanar da yankin Gaza da kuma ci gaba da tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, da kuma abu mafi muhimmanci na kafa kwamitin da za a mika masa ikon wucin gadi na tafitar da al’amuran Falasdinawa a Gaza.
Wata sanarwa da bangarorin suka fitar a karshen tarukansu a babban birnin Masar ta bayyana cewa, bisa gayyatar Jamhuriyar Larabawa ta Masar, karkashin jagorancin Shugaba Abdul Fattah el-Sisi, da kuma ci gaba da kokarin ‘yan uwa masu shiga tsakani a Masar, Qatar, da Turkiyya na dakatar da yakin Gaza da kuma magance illolinsa, a kwanan nan sakamakon taron zaman lafiya na Sharm el-Sheikh da aka gudanar a watan Oktoban 2025, wasu bangarorin Falasdinawa sun yi taro a babban birnin Masar, Alkahira, domin tattauna ci gaban da aka samu a batun Falasdinawa da kuma mataki na biyu na shirin Shugaba Trump na dakatar da yakin Gaza. Wannan taron wani bangare ne na shirye-shiryen tattaunawa ta kasa baki daya don kare aikin kasa da kuma dawo da hadin kan kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nawwafa Salam: Yin Mu’amalar Diplomasiyya Da “Isra’ila” Ba Shi Alfanu October 25, 2025 Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Watsi Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Masa October 25, 2025 Kungiyar Kwallon Kafa Ta Futsal Ta Matan Iran Sun Sami Nasara Akan Kasar Bahrain October 25, 2025 Antonio Gutrress: MDD Tana Bukatuwa Da A Yi Ma Ta Kwaskwarima October 25, 2025 Lebanon: An Sami Shahidai 3 Sanadiyyar Hare-haren HKI A Kudancin Lebanon October 25, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Isra’ila Kan Kasar Lebanon October 24, 2025 Rasha Ta Jaddada Cewa: Kasashen Turai Sun Taka Doka Kan Batun Makamashin Nukiliyar Iran October 24, 2025 Ayatullahi Khatami Ya Ce: Shugaban Kasar Amurka Trump Dan Ta’adda Ne October 24, 2025 Shugaban Amurka Ya Ce: Za Su Dauki Matakin Soji Kan Kasar Venezuela Nan Gaba Kadan October 24, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Yi Allah Wadai Da Mamaye Yankin Yammacin Kogin Jordan Na Falasdinu October 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MِِِِDD: Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya
Wakiliyar musamman ta majalisar dinkin duniya kan yankin falasdinu da aka mamaye Francesca Albanese ya bayyana irin halin da ake ciki a yankunan falasdinu da isra’ila ta mamaye a matsayin babban bala’I, ta ce kuma shi ne kisan kare dangi na farko da ya tada hankali duniya sosai.
Da take bayani wajen rufe taron da aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a jiya lahadi ta bayyana cewa kusan komai ya lalace a yankin, wanda hakan ke nuna kusan rushewar harkokin siyasa da tarbiyar alumma,
Wannan ba shi ne kisan kare dangi na farko a tarihin dan Adam ba, wannan shi ne kusan karo na 3 na kisan kare dangi idan bai zama na 4 ko na 5 ba da ya faru a tsawon rayuwata, amma wannan shi ne kisan kare dangi da ya farkar da alummar duniya kuma ta mayar da martani akai, falasdinawa sun bamu damar mu ga yadda doka take a hannu masu karfi.
Babbar kotun duniya mai hukumta laifukan yaki tuni ta riga ta bayyana a fili cewa Isra’ila ta kawo karshen mamaya, kuma ta janye sojojinta ta kuma rusa matsugunnan yahudawa yan share wuri zauna, da kuma dakatar da lalalata muhimmman gine-gine na falasdinawa, wannan shi ne Adalcin da ake bukata .
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Duk Wani Rikici December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025 Macron Na Faransa Ya Yi Wa Najeriya Alkawalin Taimakawa Akan Matsalolin Tsaro December 8, 2025 Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka Teke Fuskanta December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci