Aƙalla shugabanni 15 na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Zamfara sun sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC).

 

An gabatar da waɗannan waɗanda suka sauya shekar ne a gaban Ministan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Dr. Bello Mohammed Matawalle, a Abuja ranar Laraba, ta hannun Shugaban APC na Jihar Zamfara, Alhaji Tukur Umar Danfulani, tare da Sanata Tijjani Yahaya Kaura da Alhaji Lawal M.

Liman.

 

A cewar wata sanarwa da Mai Magana da yawun jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, Minista Matawalle ya tarbi sabbin ’yan jam’iyyar da farin ciki, inda ya tabbatar musu da daidaito da damar ci gaba da aiki a cikin jam’iyyar.

 

Dr. Matawalle ya bayyana matakin da suka ɗauka na komawa APC a matsayin abin jarumtaka kuma daidai da lokaci, tare da nuna farin ciki kan yadda jam’iyyar ke ƙara samun karɓuwa a Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya.

 

Ya yaba wa shugabannin jam’iyyar a matakin jiha bisa jajircewar su wajen tuntuba da wayar da kan jama’a, wanda ya ce hakan ya ƙarfafa martabar APC a sassan jihar.

 

Da yake gabatar da waɗanda suka sauya sheka, Shugaban APC na Jihar Zamfara, Tukur Umar Danfulani, ya bayyana cewa sabbin ’yan jam’iyyar sun haɗa da manyan shugabanni 15 na PDP a matakin jiha da yankuna, waɗanda suka shiga APC domin shirye-shiryen zaɓen 2027.

 

Ya ce an karɓe su tun da farko ta hannun Sanata Tijjani Yahaya Kaura, a madadin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar.

 

 

Daga cikin fitattun waɗanda suka sauya sheka akwai: Isiyaka M. Dabo, Shugaban Matasa na PDP; Nasiru Mohammed Anka, Ma’ajin Yankin Zamfara ta Yamma; Junaidu Magaji Kiyawa, Sakataren Shirye-shirye na PDP na Zamfara ta Arewa; Musa Halilu Faru, Mataimakin Sakataren Shirye-shirye na Zamfara ta Yamma; Alhaji Lawali Aliyu Shinkafi, Sakataren Yanki na Zamfara ta Arewa; da kuma Hajiya Rabi Bakura da Hajiya Amina Duniya, waɗanda duka Ex-Officio ne na PDP a matakin jiha.

 

Sauran sun haɗa da Bashar Mohammed Dogon Kade, tsohon ɗan takarar majalisar jiha ta Kaura Namoda South, da Rilwanu Bello, tsohon ɗan takarar kansila.

 

Shi ma Sanata Tijjani Kaura, ya bayyana wannan sauya sheka a matsayin babban abin farin ciki ga APC, yana mai cewa sabbin mambobin za su ƙara ƙarfafa ginin jam’iyyar da kyautata damar ta a gaban zaɓen 2027.

 

Ita kuwa Hajiya Amina Duniya, wacce ta ce ta shafe shekaru 25 a jam’iyyar PDP, ta yi alkawarin jawo ƙarin magoya baya zuwa APC tare da kira da a tabbatar da adalci da daidaito ga kowa.

 

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan APC da suka haɗa da: Hon. Lawal M. Gabdon Kaura, tsohon shugaban APC; Alhaji Kabiru Balarabe, tsohon Sakataren Gwamnati; Hon. Yazid Shehu Danfulani, Manajan Darakta na NIAC; Barr. Aminu Junaidu, tsohon Kwamishinan Shari’a; Alhaji Sha’ayau Yusuf Talata-Mafara; Hon. Ibrahim Maigandi Danmalikin Gidan Goga, mai ba Minista shawara kan harkokin siyasa; da Malam Yusuf Idris Gusau, Mai Magana da yawun jam’iyyar, da sauransu.

 

Aminu Dalhatu

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Siyasa Zamfara a Jihar Zamfara waɗanda suka a jam iyyar sauya sheka

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya naɗa sabon Minista

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa sabon Minista a gwamnatinsa.

Karin bayani na tafe..

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna
  • Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana
  • Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 
  • Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja
  • Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja
  • Tinubu ya naɗa sabon Minista
  • An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba
  • Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC
  • Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a