Aikin hakar ma’adinai a Ivory Coast na fuskantar tsaiko yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4
Published: 24th, October 2025 GMT
Sashen haƙar ma’adinai na Cote d’Ivoire da ke samun ci gaba cikin sauri zai fuskantar matsala da tsaiko kafin zaɓen shugaban ƙasa na ranar Asabar, yayin da Shugaba Alassane Ouattara ke neman wa’adi na hudu.
A cewar Reuters, haƙar ma’adinai muhimmin ɓangare ne daga cikin ayyukan da Ouattara yake mayar da hankali a kansu, don haɓaka tattalin arzikin kasar wadda ita ce ta farko wajen samar da koko a duniya.
Tun lokacin da ya hau mulki a 2011, ayyukan samar da zinare suka habaka daga kimanin tan 10 na metric a 2012 zuwa fiye da tan 58 a 2024, tare da burin kaiwa tan 100 nan da 2030.
Majiyoyi uku na masana’antar haƙar ma’adinai sun ce masu hakar ma’adinai suna daukar matakan da ba a saba ganin irinsu ba, domin tsoron abin da zai kai ya komo a lokacin dambarwar zaben.
Majiyoyin sun ƙara da cewa ana adana kayayyakin aiki a cibiyoyin da ke yankin arewa kamar Korhogo da Odienne.
Ganin yadda rashin tsaro ke ƙaruwa da kuma tsauraran matakan tsaro a yankin Sahel na Yammacin Afirka, ƙasar Côte d’Ivoire ta zama matattarar zuba jari a fannin hakar ma’adinai, wanda hakan ya jawo hankalin manyan kamfanoni kamar Barrick, Perseus, Endeavour, Fortuna, da sauransu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Shugaban Amurka Ya Soke Shirin Ganawa Da Takwaransa Na Rasha October 23, 2025 Venezuela Ta Sanar Da Mallakar Makamai Masu Linzami Samfurin “ Igla-s” 5,000 Domin Kare Kanta October 23, 2025 Jagora: Allamah Na’ini Ya Kasance Ma’abocin Ilimi Da Sanin Siyasa October 23, 2025 Kimanin Bakin Haure 40 Ne Suka Mutu A Kokarin Ketarawa Turai Ta Tekun Mediterranean October 23, 2025 Hamas Tayi Maraba Da Karyata Ikirarin Isra’ila da Kotun Duniya ICJ Tayi Kan UNRWA October 23, 2025 Alkalai Sun Yi Watsi Da Karar Da Yan Adawa Suka Shigar Kan Zargin Magudi A Zaben Kamaru October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Putin Na Rasha Ya Ce; Kasarsa Da India Za Su Kara Girman Kasuwancinsu
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin wanda ya kai ziyarar aiki kasar India ya bayyana cewa kasar tasa da kuma abokiyar kawancenta India za su bunkasa kasuwancinsu.
Ziyarar ta shugaban kasar Rasha a Indiya, tana a karkashin taron da kasashen biyu suke yi ne daga lokaci zuwa lokaci wanda wannan shi ne karo na 23 da ya kunshi ayyukan tattalin arziki, siyasa da al’adu.
A yayin taron, kasashen biyu sun cimma matsayar bunkasa girman kasuwancinsu da zai kai dalar Amurka biliyan 100 daga nan zuwa 2030.
A nashi gefen Fira ministan kasar India, Modi ya ce, duk da fadi tashin daake samu,amma alakar kasashen biyu India da Rasha tana nan daram.
Taron na kasashen biyu dai ya damu Amurka tana mai zargin India da cewa tana taimaka wa Rasha da kudaden da take tafiyar da yakinta na Ukirania.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Na’im Kassim Ya Yi Suka Akan Shigar Kasar Cikin Kwamitin Tattaunawa Da “Isra’ila” Kai Tsaye December 6, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda December 6, 2025 Limamin Tehran: Idan Abokan Gaba Su Ka Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa December 6, 2025 Iran Da Pakisatan Sun Amince Da Farfado da Layin Dogo Tsakanin Istambul, Tehran Zuwa Islamabad December 5, 2025 Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya December 5, 2025 Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo December 5, 2025 Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu December 5, 2025 Shin Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump? December 5, 2025 Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha December 5, 2025 Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump December 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci