Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu
Published: 24th, October 2025 GMT
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauke Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Babban Hafsan Tsaron Kasa.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sunday Dare, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, ya fitar a ranar Jumma’a.
An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — WikeA cewar sanarwar, an nada Janar Olufemi Oluyede, wanda shi ne Shugaban Sojin Ƙasa, a matsayin Sabon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa.
An kuma naɗa Manjo Janar W. Shaibu a matsayin Shugaban Sojin Ƙasa, Air Vice Marshal S.K. Aneke a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Sama, da Rear Admiral I. Abbas a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Ruwa.
Manjo Janar E.A.P. Undiendeye, wanda shi ne Shugaban Sashen Leken Asirin Tsaro (Defence Intelligence), zai ci gaba da rike mukaminsa.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan sauyi na cikin shirin gwamnati na inganta tsaron a Najeriya.
Shugaba Tinubu, ya gode wa tsohon Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, da sauran tsoffin hafsoshi bisa gudunmawa da jagorancin da suka yi.
Ya kuma bukaci sabbin hafsoshin da su nuna ƙwarewa, jajircewa, da haɗin kai domin inganta tsaro a Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babban Hafsan Tsaro Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
Sanarwar da aka fitar a karshen taron ta bayyana cewa, matakin na daga cikin kokarin da ake yi na karfafa hadin kan jam’iyyar da tabbatar da daidaiton wakilcin yanki a cikin tsarin shugabancin jam’iyyar PDP.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA