Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki.

 

Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa.

 

Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar noma, inda ta ce, manoma mata da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da wadanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000.

 

Shemau ta kuma mika godiyarta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin kokarin da take yi na bunkasa noman mata a Jihar Zamfara.

 

Sauran hukumomin da kungiyoyin da suke tare da NAWIA sun hada da Zamfara Chambers of Commerce, ACRESAL, NG-CARES, LIPAN, LP PRESS da kuma Nigeria Export Promotion Council (NEPC).

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa October 16, 2025 Labarai Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara October 16, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi, bayan wani taron gaggawa da Majalisar Koli ta ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar.

Shugaban NARD, Muhammad Suleiman, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya bayyana cewa an dakatar da yajin aikin ne na tsawon makonni huɗu, domin bai wa gwamnatin Tarayya damar aiwatar da muhimman buƙatun da suka gabatar.

Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku Kuɗin Cizo ya tilasta rufe fitacciyar sinima a Faransa

Ya ce an cimma matsayar ne bayan saka hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da ta ƙunshi ci gaban da aka samu kan manyan buƙatu 19 na ƙungiyar, ciki har da biyan bashin albashi da alawus-alawus da sauran haƙƙoƙinsu.

Suleiman ya ce Majalisar Koli ta dakatar da yajin aikin ne a matsayin wata alama ta kyakkyawan fata, domin a ci gaba da sa ido kan yadda gwamnati za ta aiwatar da alƙawuran.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta yi amfani da wannan wa’adi na makonni huɗu domin ƙara faɗakar da ’yan Najeriya da kuma ci gaba da tattaunawa da gwamnati.

Yajin aikin ƙungiyar ya bar asibitoci 91 cikin mawuyacin hali, kasancewar likitoci 11,500 — waɗanda su ne manyan ginshiƙai da ke kula da marasa lafiya a ƙasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 
  • Sojoji sun ceto ’yan mata 12 da ISWAP suka sace a Borno
  • Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa
  • An yi gangami a fadin duniya a zagayowar ranar Falasdinu
  • Najeriya :  Sojoji sun kubutar da yan mata 12 da mayakan ISWAP
  • Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki
  • Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe
  • Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano
  • Yadda ’yan mata ke kufancewa da kasuwancin fara a Kano
  • Sarakuna sun goyi bayan Gwamnatin Gombe kan yaƙi da cin zarafin mata