Aminiya:
2025-12-11@10:27:43 GMT

Saukar Farashin abinci: Manoma da gwamnati na nuna wa juna yatsa

Published: 27th, October 2025 GMT

Duk da saukar farashin abinci a kasuwanni a sassan Najeriya, manoma na kokawa cewa sun shiga damuwa saboda asarar da suka tafka na kuɗaɗen da suka kashe wajen noma gonakinsu, lamarin da suka ce ya rage musu ƙwarin gwiwa su ci gaba da sana’ar.

Wasu daga cikin manoman da wakilinmu suka zanta da su sun ce sun adana amfanin gona tun shekarar bara suna jiran farashi ya tashi, amma hakan bai faru ba, illa ƙara faduwa da farashin ya yi.

A watan Satumban 2024 Gwamnatin Tarayya ta buɗe ƙofa na kwanaki 150 don shigo da hatsi kamar shinkafa, dawa, masara da alkama daga ƙasashen waje ba tare da biyan haraji ba, domin rage tsadar abinci.

Amma wannan shigo da kaya ya haifar da faɗuwar farashin hatsin cikin gida ƙasa da kuɗin da ake kashewa wajen samar da su.

NAJERIYA A YAU: Shin Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Ta’dda A Najeriya? Ɗalibi ya kashe abokinsa, ya binne gawarsa a rami a Filato Gwamnati ta ce tana ɗaukar mataki

Ministan Aikin Noma da Tsaron Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce gwamnati tana sane da matsalar, kuma tana ɗaukar matakai don rage tasirin da hakan ya yi ga manoma.

Ya ce burin gwamnati shi ne tabbatar da cewa abinci ya wadatu, yana samuwa kuma farashinsa ya kasance mai sauƙi. “Idan abinci ya samu amma bai yi araha ba, to ba za mu ce akwai tsaron abinci ba,” in ji shi.

Manoma na kuka da asarar kudi

Wata manomiya, Blessing Janaru, ta ce tana da buhunan masara da gero tun girbin 2024 da ba ta sayar ba saboda idan ta sayar yanzu “asara ce kawai.”

Haka ma wasu manoma da dama sun ce sun yi asarar miliyoyin naira sakamakon faɗuwar farashin amfanin gona.

Shugaban Cibiyar Bincike ta NAERLS, Farfesa Yusuf Sani Ahmad, ya shaida wa Ministan Noma cewa “manoma suna kuka, sai masu saye ne ke jin daɗi.”

A Jihar Nasarawa, wani manomi, Alhaji Sani Abdullahi, ya ce ya kashe Naira miliyan 6 wajen noman shinkafam amma ya samu ƙasa da rabin kuɗin da ya kashe.

Haka kuma Shugaban Ƙungiyar Manoman Masara ta Najeriya (MAAN) reshen Jihar Kaduna, Mohammed Kabir Salihu, ya ce tsadar taki da magungunan kashe ciyawa ta yi mummunar illa. “Taki na urea yanzu N50,000 ne, DAP kuma N70,000 zuwa N80,000 — ta yaya ƙaramin manomi zai iya?” in ji shi.

Manoman rogo ma na cikin matsala

Manoman rogo sun ce sun shiga cikin halin ƙunci bayan shigo da gari daga kasashen waje wanda ya fitar da nasu daga kasuwa.

Wasu kamfanonin sarrafa rogo ma sun rufe saboda faɗuwar farashin, inda yanzu manoma suka koma sayarwa ga masu yin garin kwaki, a farashi mai rauni.

A Jihar Kogi, wani manomi, Ben Ameh, ya ce ya kashe Naira 16 a gonar rogons mai daɗin kadada 40, amma ya kasa samun ma rabin abin da ya kashe saboda farashin ton ya faɗi daga N170,000 zuwa N45,000.

Tsadar noman kadada ɗaya

A cewar wani manomi a Kano, yanzu kudin noma kadada ɗaya na masara ko shinkafa ya kai kusan Naira miliyan biyu, wanda a baya bai wuce N600,000 ba.

Wani jami’i a Ma’aikatar Noma ta Tarayya ya tabbatar da cewa farashin taki da magunguna ya ninka fiye da sau biyu tun farkon daminar bana.

Shugaban AFAN na kasa, Akitet Kabiru Ibrahim, ya gargadi cewa tsadar taki na iya barazana ga burin ƙasar nan na cimma isasshen abinci.

Halin kasuwa a yanzu

A yawancin kasuwanni, buhun masara kilo 100 ya kai kimanin N22,000; shinkafa shanshera N35,000; dawa N20,000; gero N35,000; wake N65,000.

Manoma da dama sun ce farashin ya yi ƙasa, kuma suna zargin shigo da hatsi daga ƙasashen waje da rashin tallafin gwamnati ne ke kashe musu gwiwa.

Wani manomi a Jihar Taraba, Haruna Saidu, ya ce: “Mun kashe miliyoyi amma ba mu samu riba ba. Gwamnati tana hana noma ta hanyar shigo da hatsi da ƙin tallafa mana.”

Wasu kuma sun fara barin noma zuwa sana’o’i daban saboda rashin riba, abin da ake ganin zai iya haifar da matsalar abinci a gaba.

Fargabar yiwuwar rashin rbinci

Masana harkar noma na gargaɗin cewa idan gwamnati ba ta daidaita tsarin tallafi da farashi ba, ana iya fuskantar karancin abinci a shekarar 2026.

Sun ce manoma da dama sun riga sun rage yawan kadada da suke nomawa saboda rashin riba, kuma hakan na iya tasiri ga samar da abinci a gaba.

Manoma sun roƙi gwamnati ta ƙara tallafa musu ta hanyar rage haraji a kan kayan noma, samar da ingantaccen tallafin taki da magunguna, da kuma hana shigo da abinci daga waje idan akwai isasshen cikin gida.

“Ba ma son a hana mutane abinci, amma idan za a shigo da kaya daga waje, to a kula kada hakan ya hallaka manoma,” in ji wani shugaban ƙungiyar manoma a Minna.

Gwamnati ta musanta batun sako hatsi daga waje

Ministan Noma ya ƙaryata ikirarin cewa hatsi da aka shigo da shi shi ne ya haddasa faduwar farashi.

Ya ce, “abincin da aka shigo da shi ma ba a sako shi ba tukuna.”

Ya ce faɗuwar farashi ta faru ne saboda ƙarin samar da abinci a cikin gida da kuma lokacin girbi.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati na raba taki da kayan noma kyauta ga ƙananan manoma domin rage musu kuɗin noma.

Sa’annan ya tunatar da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarni a saki buhunan taki miliyan 2.15 a bara domin tallafa wa manoma.

Daga Sagir Kano Saleh, Vincent A. Yusuf (Abuja), Abubakar Akote (Minna), Magaji Isa Hunkuyi (Jalingo) da Ibrahim Musa Giginyu (Kano)

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: masaram farashi faɗuwar farashi wani manomi gwamnati ta

এছাড়াও পড়ুন:

DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan kare dangi ga Najeriya.

Ko wannan ziyarar da tawagar Amurka ta kawo zai kawo karshen matsalar tsaron da Najeriya ke ciki?

NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPC
  • Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa.
  • Karamar Hukumar Agwara ta Jinjinawa Gwamnati Bisa Tabbatar da Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Jama’a
  • Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Ta Taya Oluremi Tinubu Murnar Nadin Sarauta a Ile-Ife
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu
  • DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • Saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya soya qwaqwalwarta 
  • Yara masara zuwa makaranta barazana ne ga kasa — Shettima
  • Kasashen Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Duk Wani Rikici
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato