2025-10-24@10:30:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10635

«tsarin zabe»:

    ‘Yan sandan kasar Ghana sun sanar da cewa tserato da wasu ‘yan Najeriya 57 da aka yi faskwaurinsu, haka nan kuma wasu mutane 5 da suke aikata laifuka ta hanyar sadarwar na “Internet” Jami’an ‘yan sandan sun kwace nau’ra mai kwakwalwa 77 da wayoyin hannu 38, sai kuma wasu motoci 2, akwatin talbijin 3, da kuma wasu na’urori da suke amfani da su a yaudarar mutane. A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an ‘yan sandan kasar ta Ghana su ka sanar da kai farmakin a birnin Accra a ranar Laraba 22 ga watan nan na Oktoba. Shekarun mutanen da ake amfani da su wajen yaudarar mutane ta hanyar internet suna a tsakanin 18 zuwa 26,tuni kuma an kai su...
    Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sanar da bayar da tallafin naira miliyan ɗaya ga duk iyalin da ya rasa ɗan uwa a gobarar tankar man da ta faru a garin Essa, Karamar Hukumar Katcha. Haka kuma, ya ba da tallafin naira dubu ɗari biyar ga kowanne daga cikin waɗanda suka jikkata a lamarin. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin da abin ya shafa, inda ya tantance tare da ganawa da shugabannin al’umma da mazauna yankin. Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027 NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas? Wannan sanarwa ta fito ne daga Sakataren...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da kawi karshen tattaunawa da kasar Canada dangane da batun kasuwanci Shugabann a kasar Amurka ya  zargi Canada da yin amfani da kalmomin tsohon shugaban kasar Amurka Ronald Regan ta hanayar da ba ta dace ba a cikin wasu tallace-tallace akan kudaden fito, inda ya bayyana cewa; ” Saboda  la’akari da halayyarsu an kawo karshen tattaunawar kasuwanci da kasar Canada.” Shugaban kasar na Amurka ya ci gaba da cewa; Cibiyar Ronald Ragan ta sanar da cea, Canada ta murguda zancen Regan yana Magana akan illolin kudin fito, kuma an yi hakan ne domin yin tasiri a cikin matakin da kotun koli ta Amurka za ta dauka akan batun da ake jiran ta fitar...
    MDD ta bayyana cewa a tsakanin kowadanne mutanen Gaza  4, daya daga cikinsu yana fama da yunwa. Mai Magana da yawun kungiyar Agaji ta tarayyar turai, May Musa Sayegh, ta yi ta’aliki akan wannan adadin na masu fama da yunwa a Gaza, inda ta ce; Wannan shi ne hakikanin abinda yake faruwa a kasa, kuma ya shafi mata manya da ‘yan mata da kuma kananan yara masu yawa.” May Musa Sayegh ta fada wa tashar talabijin din aljazira cewa; Sakamakon hare-hare na tsawon shekaru biyu da kuma rashin samun damar shigar da kayan agaji,musamman a arewacin Gaza aka fada cikin wannan halin. Sayegh ta kuma ce; ta fuskar kiwon lafiya, al’amurra suna kara tabarbarewa, domin mutane suna rayuwa cikin bakin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala October 24, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Tafka Ɓarna A Kasuwar Shuwaki, Ta Ƙona Fiye da Rumfuna 500 A Kano October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu October 24, 2025
    Kungiyar ‘yan wasan kokawar Iran na gargajiya na matasa ‘yan kasa da shekaru 23, ta lashe kambun duniya bayan da ta samu lambobin yabo mafi yawa. Kungiyar ta Iran ta sami lambobin zinariya 3, da azurfa 1 da kuma tagulla 2. ‘yan wasan da Iran da su ka sami kyautar zinariyar sun hada Iman Muhammadi mai ajin nauyi kilio 72, da Gulam Ridha Farakhi mai ajin nauyi kilo 87 da kuma Fardin Hidayati mai ajin nauyi 130. Wanda ya  sami azurfa kuwa shi ne Sajjad Abbaspur mai ajin nauyi kilo 60, sai kuma wadanda su ka sami tagulla da su ne Ahamd Ridha Muhsin Najad mai ajin nauyi 67,sai Abul Fadal Muhmadim ai ajin nauyi 82. Kungiyar ta Iran ta...
    “Shirin gwamnan na aiwatar da sabon tsarin albashi duk da ƙalubalen tattalin arziki ya nuna tausayinsa, gaskiya, da girmama kimar ma’aikata,” in ji shugabannin kungiyoyin.   Kungiyoyin sun kuma yaba da kokarin gwamnatin wajen gyara da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya inda suka bayyana gyaran da sabunta azuzuwan karatu a dukkan kananan hukumomi 23, amincewa da tsarin ritaya bayan shekaru 65 ko shekaru 40 na aiki ga malamai, da kuma dawo da sama da naira miliyan 500 na ajiyar ( ENDWELL) da aka rike a baya, a matsayin muhimman nasarori.   Ma’aikatan sun kara jinjina wa dawowar tsarin biyan gudunmawar adashin gata na malaman makaranta wato (ENDWELL) na kowane wata, inda suka bayyana cewa tsarin yana taimakawa wajen inganta...
    Ɗan takarar jam’iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, ya shaida wa BBC cewa a shirye yake ya kare abin da ya bayyana “nasara ƙarara” da ya samu. Yayin da al’ummar ƙasar ke ci gaba da dakon sakamakon zaɓen da za a bayyana a ranar Litinin mai zuwa, Bakary, wanda shi ma tsohon jami’in gwamnatin Paul Biya ne, ya ce zai amince ne kawai da sakamako na gaskiya. Wannan kalami nasa dai zai ƙara rura wutar zaman ɗarɗar da ake yi a ƙasar ta yankin tsakiyar Afirka. Tun daga farkon makon nan ne mutane, musamman magoya bayan Bakary suka riƙa fita kan tituna domin yin gangamin kira...
    Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa matasa dubu ɗaya (1,000) za su samu horo kan tsaron yanar gizo (cyber security) da fasahar binciken dijital (digital forensics) ta hanyar Cibiyoyin Koyon Fasahar Dijital ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) a Jihar Nasarawa. Uwargidan Shugaban Ƙasan ta bayyana haka ne yayin bikin kaddamarwa da miƙa Cibiyar Koyon Fasahar Dijital (Digital Learning Center) a Lafia da wasu jihohin ƙasar. Sanata Oluremi Tinubu ta ce, shirin horon matasan wanda za a rika gudanarwa a kowane mako daga yanzu har zuwa watan Disamba na shekara mai zuwa, yana da nufin yakki da laifukan yanar gizo (cyber crimes) da kuma ƙarfafa matasa su samu ƙwarewa ta yadda za su dogara da kansu a...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ƙara zuba jari a manyan cibiyoyin ilimi domin shirya ɗalibai su zama masu iya fafatawa a matakin duniya. Shugaban Ƙasan ya bayyana hakan ne a yayin bikin karrama masu kammala karatu na shekara ta 40 na Jami’ar Ilorin (UNILORIN) da ke Ilorin, Jihar Kwara. A jawabinsa, wanda Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya Akure (FUTA), Farfesa Temidayo Oladiji, ya karanta a madadinsa, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin ƙarfafa ƙirƙira, bincike, da ilimin da ke gina ƙwarewa (skill-based education) a dukkan jami’o’in Najeriya. Ya yaba wa jami’ar bisa tsayin daka da ladabi da kuma ingancin ilimi da ta dade tana nunawa tun daga kafuwarta. Shugaban Ƙasan ya kuma sanar da cewa Jami’ar...
    Uwargidan Shugaban Ƙasa ta Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da Dijital E-Learning Library a Gusau, Jihar Zamfara — ɗaya daga cikin jihohi goma da aka zaɓa a faɗin ƙasar domin aiwatar da wannan muhimmin aiki ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da haɗin gwiwar Hukumar bunkasa ayukkan fasaha ta kasa (NITDA). A yayin bikin kaddamarwar, Sanata Tinubu ta bayyana cewa wannan aiki ba wai game da fasaha da kwamfuta kawai ba ne, amma yana nufin ƙarfafa matasa, rage gibin fasaha (digital divide), da kuma buɗe sabbin ƙofofin ilimi da ƙirƙira ga al’ummar Zamfara da ma Najeriya baki ɗaya. Uwargidan Shugaban Ƙasa, wacce Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta wakilta, ta bayyana cewa ilimi shi ne...
    Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince a rika sauya kuɗaɗe da aka ware wasu wurare zuwa swasu idan can ya fi na farko amfani ga al’umma (virement) na naira biliyan 526 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025. Shugaban taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 12 na bana, Gwamna Ahmad Aliyu, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na da cikakken ƙuduri wajen gina Jihar Sokoto mai ingantaccen tattalin arziki ta hanyar aiwatar da muhimman sauye-sauye da shirye-shiryen ci gaban al’umma. Gwamna Aliyu ya bayyana cewa wannan sauyin kasafi an tsara shi ne domin ƙarfafa zuba jari a fannoni masu muhimmanci kamar gina manyan ayyukan raya kasa, inganta ayyukan jin kai, da haɓaka tasirin gudanar da ayyuka — ba tare da ƙara girman...
    Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa gobara ta lalata rumfuna 529 daga cikin rumfuna na wucin gadi a Kasuwar Shuwaki da ke ƙaramar hukumar Gari, Jihar Kano. Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kano. A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa misalin ƙarfe 3:25 na rana daga Abdulmalik Muhammad na ofishin kashe gobara na Gari, yana sanar da aukuwar gobara a kasuwar. Ya bayyana cewa, da zarar sun samu bayanin, hukumar ta aika jami’ai da motocin kashe gobara zuwa wurin domin kashe wutar tare da hana ta yaduwa zuwa sauran sassan kasuwar. Saminu ya ce yankin kasuwar yana da fadin kimanin...
    Shirin karfafa ilimin ‘ya’ya mata a jihar Kano ya shirya taron tattaunawa da malamai da limaman masallatan Juma’a domin ƙarfafa haɗin gwiwa da shugabannin addini wajen inganta goyon bayan al’umma ga ilimin ’yan mata a fadin jihar. Taron, wanda yake ɗaya daga cikin dabarun haɗin kai na masu ruwa da tsaki na AGILE, yana da nufin ƙara samun damar karatu, tsayawa da kuma kammala karatun ’yan mata ta hanyar daidaita ayyukan shirin da dabi’u da imanin al’umma. A jawabinsa, Shugaban Shirin AGILE na Jihar Kano, Malam Mujtapha Aminu, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin fayyace wasu rashin fahimta da ake da su game da shirin, da kuma tabbatar da fahimtar juna tsakanin shugabannin addini. A cewarsa, “Shigar malamai...
    Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) ta amince da shirin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu na sake fasalin da kuma zamanantar da cibiyoyin horar da jami’an tsaro a faɗin ƙasar. Wannan mataki ya biyo bayan taron majalisar na 152 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya gabatar da jawabi kan dabarun cimma burin Shugaban Ƙasa na samar da tattalin arzikin da ya kai darajar dala tiriliyan guda. An kafa kwamitin da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ke jagoranta don tsara cikakken tsari na gyaran da sabunta cibiyoyin horar da jami’an ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro cikin wata guda. Mambobin kwamitin sun haɗa da gwamnonin jihohin...
    Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Har ila yau, shirin nan nata Mata A Aikin Noma, ya bai wa matan karkara sama da 20,000 tallafi da horarwa da ƙara samun kuɗin shiga ga iyalai da kuma wadatar da al’umma. Kazalika, shirin Tallafin Ilimi, ya samar wa fiye da ɗalibai 3,000, guraben karatu, kwamfiyutoci da kuma jagoranci na gari. Ga tsofaffi kuma, Asusun Tallafa wa Tsofaffi ya bai wa tsofaffi 5,000 alawus-alawus da kula da lafiyarsu tare kuma da maido da martabar musamman waɗanda aka yi watsi da su, aka kuma manta da su. Lokacin da iftila’i ya afku a Jihohin Filato da Benuwe a tsakiyar 2025,...
    Baya ga haka, sabon ginin ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Zamfara da aka sake ginawa da kuma sabon ginin kwalejin fasaha da kimiyya na Jihar Zamfara (ZACAS) da aka gyara, sun yi matuƙar haskaka Gwamnatin Dauda Lawal. Har ila yau, jihar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar zuba jari, wajen gyarawa da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin jihar.  A ƙoƙarinsa na rage mace-macen mata masu juna biyu da mace-macen jarirai, an ɗauki ma’aikatan kiwon lafiya tare da horar da su da sayen magunguna da kayan aiki da ɓullo da ayyukan kula da lafiyar mata da ƙananan yara kyauta. Sannan, an gyara asibitin ƙwararru na...
    Baya ga haka, sabon ginin ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Zamfara da aka sake ginawa da kuma sabon ginin kwalejin fasaha da kimiyya na Jihar Zamfara (ZACAS) da aka gyara, sun yi matuƙar haskaka Gwamnatin Dauda Lawal. Har ila yau, jihar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar zuba jari, wajen gyarawa da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin jihar.  A ƙoƙarinsa na rage mace-macen mata masu juna biyu da mace-macen jarirai, an ɗauki ma’aikatan kiwon lafiya tare da horar da su da sayen magunguna da kayan aiki da ɓullo da ayyukan kula da lafiyar mata da ƙananan yara kyauta. Sannan, an gyara asibitin ƙwararru na...
    Kazalika, har yanzu batun tsohon shugaban Majalisar Wakilai wato Salisu Buhari, na 1999, na yin amfani da Takardun karatu na bogi da ya yi iƙirarin ya samo daga Jama’iar Toronto, baƙalar na ci gaba da kafa babban misali, a ƙasar. Badaƙalar ta sa, ba ta tsaya nan ba, ya kuma ƙaryar shekarun na haihauwa, domin kawai, ta tsaya takarar siyasa, a wancan lokacin, wanda kuma ya nuna turjiya daga sauka daga muƙamin na nsa duk da ɗimbin hujjojin da suka bayyana a kansa, inda bayan komai ya bayyana ƙarara, ya sauka daga kan muƙamin shugabancin Majlisar a 2000, ya kuma ɓarke da kuka a Majalisar, ya amsa cewar, Takardunsa na bogi ne. Haka ita ma, tsohuwar ministan kuɗi Kemi Adeosun,...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci takunkumin maimakon mika wuya ga manufofin ‘yan mulkin malla. “Mun cimma yarjejeniya da bangarori na Turai, amma ra’ayin Amurka ya bambanta, kuma abu ne na hankali kan cewa Iran ba zata mika wuya ga dukkanin abin da Amurka take bukata ba, domin hakan ya yi hannun riga da maslahar Iran. Amurka da kawayenta, wadanda ake kira da E3, sun  ki amincewa da wani daftarin kuduri daga Rasha da China, wanda ya nemi jinkirta aiwatar da tsarin dawo da takunkumai kan Iran a karkashin yarjejeniyar nukiliya ta  JCPOA. Pezeshkian ya kara da cewa Amurkawa “suna son mu ba su dukkan sinadarin uranium da aka tace, wanda ba za...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Amurka na shirin fara kai hare-hare ta kasa a kan kungiyoyin da ya kira masu safarar miyagun kwayoyi a Venezuela. “Kwayoyin da ke shigowa ta teku sun kai kashi 5% a shekara daya da ta gabata, in ji Trump, a lokacin wani taron manema labarai kan batutuwa da suka shafi siyasarsa kan kasashen waje. Trump ya kuma ba da shawarar cewa Sakataren Yaki Pete Hegseth ya yi wa Majalisa bayani kan matakin soja da ke tafe. A farkon wannan makon, Hegseth ya bayyana cewa Amurka ta kai hare-hare biyu masu muni kan jiragen ruwa a gabashin Pacific da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a kudancin Caribbean. Da yake amsa tambayoyi game...
    Sashen haƙar ma’adinai na Cote d’Ivoire da ke samun ci gaba  cikin sauri zai fuskantar matsala da tsaiko kafin zaɓen shugaban ƙasa na ranar Asabar, yayin da Shugaba Alassane Ouattara ke neman wa’adi na hudu. A cewar Reuters, haƙar ma’adinai muhimmin ɓangare ne daga cikin ayyukan da Ouattara yake mayar da hankali a kansu, don haɓaka tattalin arzikin kasar wadda ita ce ta farko wajen samar da koko a duniya. Tun lokacin da ya hau mulki a 2011, ayyukan samar da zinare suka habaka daga kimanin tan 10 na metric a 2012 zuwa fiye da tan 58 a 2024, tare da burin kaiwa tan 100 nan da 2030. Majiyoyi uku na masana’antar haƙar ma’adinai sun ce masu hakar ma’adinai suna...
    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man shi na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun jarinta a kasuwar hannun jari ta Najeriya. Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da S&P Global, inda ya ce ana sa ran sayar da hannun jarin a cikin shekara mai zuwa. Dangote ya ce wannan mataki kwatankwacin irin yadda aka gudanar sayar da hannun jarin kamfanononin siminta da suga na Dangote ne. “Ba ma son mu riƙe fiye da kashi 65 zuwa 70 cikin 100,” in ji shi. Ya ƙara da cewa za a sayar da hannun jarin a hankali, gwargwadon sha’awar masu zuba jari da ƙarfin kasuwa. Hamshakin dan kasuwar...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, ya rantsar da Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN), a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) na shida da aka tabbatar da shi. An gudanar da wannan gajeren bikin rantsarwa ne a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas? An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato Bayan rantsarwar, Shugaba Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC da ya yi aiki da gaskiya da amana, ba tare da wata matsala ba. “Naɗa ka da kuma tabbatar da kai da Majalisar Dattawa ta yi, alama ce ta ƙwarewarka da amincewar da bangarorin zartaswa da...
    Sakatare-Janar na kwamitin hadin gwiwa na yankin Gulf Jassim Al-Badawi  ya yi kakkausar suka kan amincewa da wasu kudirori guda biyu a majalisar Knesset ta Isra’ila da ke da nufin kakaba ikon Isra’ila kan yankin yammacin kogin Jordan da ta mamaye. A rahoton talabijin ta Aljazeera, Jassim Al-Badawi a cikin wata sanarwa a jiya Alhamis ya jaddada cewa, matakin da majalisar Knesset ta Isra’ila ta dauka, wani mataki ne da ya saba wa kudurorin kasa da kasa, da kuma kawo cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi na samun zaman lafiya mai dorewa. Haka nan kuma ya jaddada cewa ayyukan gina matsugunan da gwamnatin sahyoniyawan suke yi a fili take ga hakkokin tarihi na al’ummar Palastinu da dokokin kasa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare.   Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati. Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da dabaru irin na soji da kuma kayan yaki na zamani. Wannan lamari ya jawo tambaya daga al’umma: shin wannan karin hare-hare alama ce ta dawowar kungiyar Boko Haram da...
    Mutanen da yawansu bai wuce kashi 1 cikin dari a duniya ne ba sun samu wadatar arziki da fiye da kashi 60 cikin dari. Yayin da ake fuskantar matsalar gibin dake tsakanin hamshakai da matalauta a duniya, kasar Sin ta samar da gudummawarta wajen daidaita matsalar. Confucius ya taba cewa, abin damuwa shi ne yadda kowa ba ya samun daidaito, amma ba zama da talauci ba. Kana kasar Sin ta kawar da talauci ga mutane miliyan 100 a cikin shekaru 8, kuma a halin yanzu ana kokarin sa kaimi ga dukkan jama’ar kasar su samu wadata tare, yayin da ake kokarin zamanintarwa irin ta kasar Sin. Kasar Sin ba ta bi hanyar kasashen yammacin duniya wacce ta haifar da matsalar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba October 23, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka October 23, 2025 Daga Birnin Sin An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15 October 23, 2025
    Wasu daga cikin sojojin sun ji rauni amma suna cikin ƙoshin lafiya. Haka kuma, wasu gine-gine da motocin da ke kusa sansaninin sun lalace yayin artabun. Rundunar sojin ta yaba da jarumtar dakarunta, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare ƙasar daga duk wata barazana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 23, 2025 Manyan Labarai Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025
      Yanzu haka kuwa, hankula na kara karkata ga shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 da Sin za ta aiwatar tsakanin shekarar 2026 dake tafe zuwa shekarar 2030, kuma masharhanta na ganin a karon gaba, Sin za ta fadada manufofinta na samar da ci gaba domin dorar da nasarorin da ta riga ta cimma.   Muhimman fannonin da ake ganin shirin na iya mayar da hankali a kansu, sun hada da tunkarar kalubalen karuwar kason al’ummar kasar masu tsayin shekaru, da kokarin warware tarnakin kasashen yamma dangane da harkokin cudanyar fasaha, yayin da Sin din ke fafada kirkire-kirkire a cikin gida.   Kamar yadda Sin ta riga ta dora dan-ba a fannonin zuba jari don cin gajiyar...
    Fitaccen ɗan wasan tamaula, Lionel Messi, ya tsawaita kwantiraginsa da ƙungiyar Inter Miami har zuwa shekarar 2028, kamar yadda kulob ɗin ya sanar a ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025. Wannan sabon kwantiragin zai bai wa kulob ɗin da ma gasar MLS ta Amurka damar ci gaba da kasancewa tare da ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan da duniya ta taɓa gani har zuwa ƙarshen kakar wasa ta 2028. An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe A ƙarshen wannan kakar ce kwataragin ɗan wasan na ƙasar Argentina zai ƙare, inda ya bayyana farin cikin sabunta shi kamar yadda wani saƙo da kulob ɗin ya...
    Jami’ar mai aikin tsarawa MDD rahoto akan Falasdinu  Farencesca Albanese ta bayyana cewa; tsagaita wutar yaki da aka yi a Gaza, bai wadatar ba, wajibi ne a kawo karshen tsarin mamaya a Falasdinu. Albanese ta kuma ce Amurka ce take bai wa ‘yan mamaya cikakken goyon baya a kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Falasdinu,don haka ya zama wajibi a kawo karshen yadda ‘yan mamayar suke sarrafa albarkatun al’ummar Falasdinu,sannan kuma a tarwatsa tsarin mulkin mallaka na mamaya. A halin da ake ciki a yanzu dai Albanese tana kasar Afirka Ta Kudu, inda take halartar taron shekara-shekara akan “Nelson Mandela” za kuma ta gabatar da jawabai a wurin. Tun a cikin watan Mayu ne dai Amurka ta kakawa ma’aikaciyar...
    Fadar mulkin kasar Rasha Krimlne ta sanar da cewa, shugaban kasar Valdmir Putin ne ya sa ido akan yadda rundunar dake kula da makaman Nukiliya ta gudanar da rawar daji a sansnain “Blisitiks”. Sanarwar ta kara da cewa, rundunar dake kula da muhimman makakan Nukiliyar kasar ta Rasha  ta yi amfani da makamai masu linzami samfurori mabanbanta. Haka nan kuma fadar gwamnatin Rashan ta ce, an gudanar da  dukkanin gwaje-gwajen cikin nasara, an kuma yi ne domin tabbatar da cewa rundunar tana cikin shirin ko-ta-kwana. A wani labari mai alaka da Rasha, ma’aikatar harkokin waje ta gargadi kasashen turai akan kokarin bai wa Ukiraniya kudadenta da suke a cikin bankunansu. MA’aikatar harkokin wajen Rasha ya fadawa kasashen turai din cewa...
    An tsara cewa a cikin wannan makon da aka shiga ne dai za a gana a tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha domin share fagen ganawar shugabannin kasashen biyu. Fadar mulkin Amurka “ White House” ta bayyana cewa an yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin ministocin harkokin wajen Amurka da Marco Rubio da Sergey Lavrov a shekaran jiya inda su ka cimma matsaya akan cewa, ganawar ba ta zama dole ba. A makon da ya shude ne dai shugabannin kasashen Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladmir Putin su ka yi ttataunawa ta wayar tarho, inda su ka cimma matsaya akan ganawa a birnin Budaphast na kasar Bulgaria. A cikin watan Ogusta na wannan shekarar an...
    Shugaba kasar Venezuela Nicolas Maduro ne ya bayyana cewa, kasarta ta mallaki makamai masu linzami samfurin “Igla-S” kirar kasar Rasha har 5000, domin tabbatar da tsaronta. Shugaba Maduro ya ce, tuni an girke wadannan makaman a wurare masu muhimmanci, kuma za a sake girke su a fadin kasar domin bayar da kariya ga sararin samaniyar kasar. Bugu da kari shugaban kasar taVeneuela ya ambaci cewa da akwai dubban kwararru da su ka iya sarrafa wadannan makaman na tsaron sararin samaniyar kasar, da za su iya watsuwa a duk inda aka girke makaman a cikin dukkanin kusurwowi hudu.Nicholas Maduro ya kuma ce, wajibi kasar Venezuela ta zama mai kariya, ta yadda babu wanda zai iya kawo mana hari, domin ba mu...
    Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran wanda ya gana da tawagar masu shirya taron tunawa da Alamah Mirzai Na’ini ( R.A), ya ce; muhimman siffofi biyu da malamin ya kebanta da su, su ne kirkira a fagen ilimi da kuma a cikin ilimin siyasa. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana Allamah Na’ini a matsayin daya daga cikin fitattun malamai, masu tarin sani a cikin jami’ar Najaf mai tsohon tarihi; jagoran juyin na Iran ya yi ishara da yadda marigayin malamin ya samar da ka’idojin da aka gina ilimin usulu akansu, wanda ya kai ga sabunta shi. Daga cikin rukunonin tunanin Allamah Na’ini kamar yadda jagoran juyin ya ambata da akwai batun kafa tsarin musulunci akan ginshikin wilaya domin kalubalantar...
    A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama. An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar...
    Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya ta ƙaddamar da yunƙurin ƙasa baki ɗaya na yin rigakafi kyauta ga karnuka da maguna domin yaƙar cutar haukan kare inda Jihar Gombe ke shirin yin riga-kafi ga karnuka 2,500 a matakin farko. Da take jawabi yayin bikin ƙaddamarwar da aka gudanar a Gombe, Babbar Sakatariya na Ma’aikatar, Dokta Chinyere Akujobi wadda Mataimakiyar Darakta, Dokta Salome Bawa ta wakilta ta bayyana cewa cutar haukan kare na ci gaba da hallaka dubban mutane a duk shekara a faɗin duniya, musamman a nahiyoyin Afirka da Asiya. An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe Ta ce, mafi yawan waɗanda ke mutuwa sakamakon...
    A wurin taron, kwamitin tsakiya na JKS ya kafa wasu tsare-tsare da za su zama jagora kan bunkasa harkokin tattalin arziki da walwalar al’umma a cikin shirin na shekaru biyar-biyar na 15 wadanda suka hada da sake tabbatar da shugabancin jam’iyyar baki daya, da sanya kula da mutane a gaba da komai, da neman samun ingantaccen ci gaba, da cikakkiyar zurfafa gyare-gyare a gida, da karfafa cudanya tsakanin kasuwa mai albarka da gwamnati mai kwazon aiki, da kuma tabbatar da samun ci gaba da inganta tsaro. Har ila yau, kwamitin tsakiya na JKS ya shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka...
    Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa a ranar 16 ga watan Oktoba. Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin? Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja  A yayin taron, Shugaba Tinubu ya buƙaci Farfesa Amupitan da ya tabbatar am gudanar da sahihancin zaɓe a Nijeriya tare da inganta INEC domin tabbatar da gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci. An tabbatar da naɗin Amupitan bayan Majalisar Dattawa ta...
    A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sakamakon matakan takunkumi da kasar Amurka ta dauka kan kamfanonin fasahohin zamani na kasar Sin, kasar Sin ta kara saurin yin kirkire-kirkire a matsayin mai zaman kanta, wanda ya haifar da karuwar sabbin nasarori a fannonin da suka hada da fasahohin kere-kere, da na’urar mutum-mutumi, har ma ta zarce sauran kasashe a wasu muhimman fasahohin zamani. Sa’an nan, dangane da takunkumin da wasu kasashen yammacin duniya suka kakaba mata, kasar Sin ta yi kokarin inganta karfin jure wahalhalu da tabbatar da kiyaye bangaren masana’antu da samar da kayayyaki, tare da rage tasirin matsalolin da kan taso daga waje yadda ya kamata. Wadannan ingantattun hanyoyin mayar da martani ga matsin lamba daga ketare sun nuna...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa  zata kara karfafa dankon zumunta da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin da mahukunta hukumar NAFDAC suka ziyarce shi a ofishin sa dake Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana farin cikinsa da ziyayar, inda ya jaddada bukatar aiki tare domin cimma dukkan nasarar da ake bukata a tsakanin hukumomin biyu. Da yake bayani dangane da shirin da hukumar alhazan take yi, Labbo yace dukkanin shirye-shirye sunyi nisa na rigistar kujerun aikin hajji shekarar 2026. Yana mai cewar, hukumar NAFDAC tana cikin masu ruwa da tsaki na hukumar jin dadin alhazan jihar. Alhaji Ahmed Labbo, yayi nuni...
    Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan manoman da suke aikin girbin amfanin gona a yankin Mbor na masarautar Mushere na Ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Filato, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu biyu a ranar Laraba da yamma. Shugaban Ƙungiyar matasan Mushere, Kopmut Monday ne ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin a ranar Alhamis. Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga A cewar shugaban matasan, ’yan bindigar sun kai farmaki wurin ne inda suka buɗe wuta kan manoman da ke cikin aikin girbin amfanin gona, inda ya ce manoman sun tsere domin tsira da rayukansu. Shugaban ya zargi makiyaya da kai wa...
    An zargi mayaƙan Boko Haram da ISWAP da kai hare-hare wasu yankuna biyar da ke Jihohin Borno da Yobe. Sun kai hare-haren ne garuruwan Mafa, Dikwa, Marte, da Ajiri a Jihar Borno, da kuma Katarko a Jihar Yobe. Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara kai hari wani shingen sojoji  da ke Mafa, sannan suka sace makamai da sabbin babura da sojoji ke amfani da su. Wata majiyar tsaro ta ce: “Sun zo da yawa kuma ɗauke da muggan makamai. Sun sace makamai da baburanmu. Yawansu dana gani abun mamaki ne.” Ba a tabbatar da adadin sojojin...
    Rahotanni sun bayyana cewa Ƴan ci rani 40 daga kudu da saharar Afrika sun mutu, sakamakon  kifewar kwale-kwale a kasar Tunisia, sai dai  an samu nasarar ceto wasu mutum 30. Kakakin ofishin masu gabatar da kara a Tunisia Walid Chtabri ne ya tabbatar da kifewar kwale-kwalen dake dauke da mutane 70 ‘yan kudu da saharar Afrika a Tunisia. Walid ya ce an gano gawarwakin ƴan ciranin 40 ciki har da jarirai, yayin da aka ceto mutane 30 da ransu, kuma dukkaninsu daga kasashen kudu da sahra suka fito. Gabar ruwan Tunisia na da nisan kilomita 145 tsakanin ta da tsibirin Italiya na Lampedusa, inda ya zama hanyar da dubban ƴan cirani ke amfani da ita wajen tsallaka wa zuwa Turai...
    Kungiyar gwagwarmyar ta Hamas ta yi maraba da matakin da kotun kasa da kasa ta ICJ ta dauka na karyata ikirarin da HkI ta yi kan hukumar bada agaji ga falsdinawa yan gudun hijira  ta majalisar dinkin duniya . Gwamnatin Sahyuniya ta yi ikirarin karya kan hukumar ta UNRWA inda kafafen yada labarai na kasashen turai suka yayata ba tare da wani bincike ba kan gaskiyar lamarin, inda kotun ta ICJ ta majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan ikirarin karya da isra’ila ta yi kuma ta kare hukumar UNRWA ta bayyana irin ayyukan jinkai da take yi da gudanarwa ga alummar falasdinu. Babban kotun duniya ta umarci isra’ila da ta bada dama a shiga da kayayyakin agaji zuwa...
    Alkalan kotu a Kamaru sun yi watsi da bukatar da jamiyyun adawa suka ka gabatar masu ta neman ko dai su soke wasu sakamakon zaben shugaban kasar ko kuma su soke zaɓen baki daya, inda suka ce za su sanar da sakamako a ranar Litinin, sai dai ta dage lokacin daga baya. Zanga-zanga ta barke a wasu manyan biranen kasar, inda ƴan adawa suka yi zargin an tafka kura-kurai a zaɓen na ranar 12 ga watan Oktoba. Alkalan kotun tsarin mulki sun yi watsi da korafi har takwas da aka gabatar masu, domin a cewar su babu cikakkiyar shaida mai tabbatar da su. Dan takarar ƴan adawa, Issa Tchiroma Bakary ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben, wani...
    Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf.   Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani ya yabawa hukumar DSS kan nasarar da ta samu, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawar da miyagun laifuka a fadin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki  October 22, 2025...
    Sama da yahudawa 450 daga sassa daban daban na duniya ne suka yi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran shuwagabannin kasashen duniya da su kakabawa gwamnatin Isra’ia takunkumin saboda kisan kare dangi da nuna rashin dan adamtaka da ta yi kan alummar gaza. Acikin wata budaddiyar wasika da suka rubuta sun bayyana cewa ba mu manta da cewa mafi yawancin dokoki da sharudda da kuma yarjeniyoyi da aka kafa an yi su ne don kiyaye da kuma kare rayukan yan adam, kuma don mayar da martani ga kisan yahudawa da aka yi na holocus. Wasikar ta bukaci a girmama hukumcin da kotun kasa da kasa  ta fitar da ta hana aikawa da isra’ila makamai, sanya takunkumi ga duk wanda...
    Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kama ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore, bisa ci gaba da zanga-zangar neman a saki shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Sowore, wanda aka kama a ranar Alhamis a birnin Abuja, wasu jami’ai dauke da bindiga ne suka yi masa dirar mikiya, sannan suka tafi da shi zuwa wani wuri da ba a bayyana ba tukuna. Nnamdi Kanu ya kori lauyoyinsa, ya ce zai kare kansa a kotu Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio Lauya mai kare haƙƙin ɗan adam kuma mai rajin kare ’yancin jama’a, Deji Adeyanju, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu. “Eh, Sowore yanzu haka ’yan sanda sun kama shi,” in ji shi. Har yanzu...
    “Allah ya albarkace mu da shugaba mai tsoron Allah da kishin jama’a – mutum ne mai kaunar al’ummar jihar Kano da Nijeriya, kuma me aiki tukuru domin ganin ci gabansu,” in ji Yusuf.   Ya kuma jaddada kudirin sa na ciyar da jihar gaba bisa tsarin falsafar Kwankwasiyya, wanda ke jaddada hidima, rikon amana, da tallafawa.   A nasa jawabin, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar NNPP da na Kwankwasiyya na kasa baki daya da su ci gaba da hada kai da kuma jajircewa wajen ci gaban jam’iyyar.   Ya kuma mika godiyarsa ga shugaban NNPP na kasa Dr. Ajuji Ahmed, da sauran shugabannin jam’iyyar daga jihohi sama da 30, da masu biyayya da suka halarci bikin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan leken asiri na kasar iran Ismail Khatib a wajen taron da aka yi a lardin chahar mahali bakhtiyar  ya bayyana cewa iran bata da wani  lamuni na kare maslaharta ta hanyar tattaunawa da kasar Amurka, yace Amurka tana ikirarin cewa za ta ci gaba da tattaunawa da iran, tana boye adawar da take yi da kasar iran ne kawai. Yace kasashen Amurka da isra’ila da sauran kasashen dake adawa da Iran, sun yi kokari wajen durkusar da kasar iran a yakin kwanaki 12 wanda washignton da tel aviv suka kakabamata a watan yuni. Minstan ya ci gaba da cewa irin wannan ci gaba da da kuma cin zarafi da HKI ta yi da goyon bayan...
    Shugaban Ƙungiyar ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya sallami dukkanin lauyoyinsa. A zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis, Kanu ya shaida wa kotu cewa a shirye yake ya kare kansa ba tare da taimakon lauya ba. DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum Lauyoyin da ke kare shi ƙarƙashin jagorancin Kanu Agabi (SAN), sun yanke hukuncin cire hannunsu daga kare shi kan shari’ar da yake fuskanta. Daga nan sai Kanu ya fara magana kai-tsaye, inda ya ƙalubalanci ikon kotu na ci gaba da yin shari’arsa.   Cikakken bayani zai biyo baya…
    Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da yin ƙarin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata daga cfa 30,000 zuwa cfa 42,000, wanda ya yi daidai da naira 108,780 a Najeriya. Wannan ƙarin albashi na daga cikin matakan gwamnatin domin inganta rayuwar ma’aikata da ƙarfafa su wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kamar yadda gwamnatin ta sanar. Majalisar Ministocin gwamnatin ce ta ɗauki wannan mataki a taron da ta gudanar jiya Laraba, inda kuma minsitocin suka tattauna hanyoyin da za a tabbatar da cewa ƙarin albashin zai shafi dukkan ma’aikatan gwamnati ba tare da rarrabewa ba. Wannan mataki ya zo ne bayan da gwamnatin ta lura da ƙaruwar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi a ƙasar. Gwamnatin ta bayyana cewa...
    Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama wasu mutum uku da ake zargi da sayar da wa ’yan bindiga makamai da harsasai a Jihar Kaduna. An kama su ne bayan wani samame da jami’an DSS suka kai a ƙananan hukumomin Igabi da Kachia. ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio An kama ɗaya daga cikinsu mai shekaru 30, a kan titin Nnamdi Azikiwe Bypass da ke Igabi. An gano bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, bindigar PKT guda ɗaya, harsasai sama da 200. Sauran mutum biyu kuma an kama su ne a ƙauyen Doka da ke Ƙaramar Hukumar Kachia, a kan hanyar...
    Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kwara, Barista Senior Ibrahim Sulyman, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da inganta adalci, kyakkyawan shugabanci, da samar da damar samun shari’a ga kowane ɗan ƙasa.   Sulyman ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai na watanni uku (quarterly ministerial briefing) da aka gudanar a birnin Ilorin.   A cewarsa, Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kwara tana daga cikin ma’aikatun da ke ba da muhimmanci ga hidima ga jama’a, wadda ke da alhakin gurfanar da masu laifi a kotu, kare gwamnati, tsara da tantance takardun doka, da kuma ba da shawarar doka ga sauran ma’aikatun gwamnati.   Ya bayyana cewa ma’aikatar na aiki ta hannun sassa guda shida (directorates)...
    Fiye da gidaje dari biyu da tamanin (280) a Karamar Hukumar Lafia sun samu kwandunan ajiyar shara (trash bins) domin inganta kula da tsaftar muhalli da rage datti a babban birnin jihar.   An gudanar da rabon ne a birnin Lafia, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Nasarawa, Dr. Margaret Elayo.   Shirin wayar da kai da rabon kwandunan ya shafi wasu kananan hukumomi da suka haɗa da Karu, Keffi, Akwanga, Wamba, Obi, da Keana, inda Lafia ta fi kowa samun masu cin gajiyar wannan shiri.   A yayin taron, Dr. Margaret Elayo ta bayyana damuwarta kan yadda datti ke ƙaruwa a tituna da magudanan ruwa, lamarin da ke haifar da barazana ga lafiya da muhalli.  ...
    Ƙungiyar Centre for Communication and Social Impact (CCSI) tare da haɗin gwiwar abokan aikin ta na EngenderHealth Consortium sun shirya taron horo na yini ɗaya a Kano domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta (social media influencers) wajen yada sahihan bayanai da tallafawa manufofin kiwon lafiya da daidaito tsakanin jinsi.   Taron, mai taken “Daga Masu Bi zuwa Masu Faɗa Aji: Amfani da Kafafen Sada Zumunta wajen Yaɗa Sawun Lafiya da Daidaito”, ya mayar da hankali ne kan batutuwan Reproductive, Maternal, Newborn, Child, and Adolescent Health plus Nutrition (RMNCAH+N), Family Planning (FP), da Gender, Youth, and Social Inclusion (GYSI).   Manufar wannan horo ita ce canza masu tasiri a kafafen sada zumunta zuwa ƙwararrun masu...
    Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan mummunar haɗarin fashewar motar mai da ta faru a ƙauyen Essa, cikin Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa.   A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya sanya wa hannu, Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Neja da al’ummar jihar bisa wannan babban rashi, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin tunawa da illar da ke tattare da haɗarin motocin mai a ƙasar.   Sanarwar ta nuna damuwa kan yadda, duk da wayar da kai da gargadin da ake yi a kai a kai, wasu ’yan ƙasa har yanzu ke shiga...
    Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar.   Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu.   Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen taron horaswa na kwanaki biyu mai taken “Leading Learning for Gender Equality in Education” wanda British Council ta shirya domin wakilai daga jihohin Kano, Kaduna, Plateau da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).   Dr. Makoda ya ce, jagoranci mai ƙarfi da tsari a cikin makarantu shi ne ginshiƙin cimma ingantaccen ilimi. Ya kara da cewa, shugabannin makarantu...
    Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bai wa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars Football Club sabbin motoci uku domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri a yayin gasar Premier ta shekarar 2025/2026 da ke gudana.   Motocin sun haɗa da babbar motar Marcopolo mai kujeru 29 don ɗaukar ’yan wasa, motar samfurin Hummer, da kuma Sharon da za a yi amfani da ita wajen harkokin gudanarwa da sufuri.   A lokacin da yake mika makullai da takardun motocin a madadin Gwamnan, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Malam Ibrahim Umar Farouk, ya roƙi matasan jihar masu son wasanni da su ci gaba da zama masu bin doka da oda tare da guje wa duk wani abu da zai...
    Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja. Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da tankar ta kife kuma ta kama da wuta yayin da jama’a ke ƙoƙarin ɗibar mai. Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi Wasu da dama sun ji rauni kuma an garzaya da su Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Bida. Shehu, ya ce mata ne suka fi...
    Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi.   Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin wadannan bala’o’in da za a iya rigakafin su, na nuna bukatar kara wayar da kan jama’a game da haɗurran da ke tattare da hakan cikin gaggawa.   Ya ce, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), an umurce ta da ta hada karfi ga kokarin Gwamnatin Jihar ta hanyar samar da kayan agaji da taimakon magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. ShareTweetSendShare...
    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya. Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin karatu na biyu a kan dokar gyaran tsarin zabe a zaman majalisa da aka yi a ranar Laraba. Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 “Ina da tabbacin cewa ni da Sanata Abaribe, wanda muka shafe kusan shekaru 25 muna cikin...
    Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki.   A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne na manufofin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na binciko albarkatun ma’adanai na jihar don haɓaka tattalin arzikin cikin gida mai ɗorewa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki  October 22, 2025 Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta...
    Kotun kasa da kasa ta ICJ ta bayyana cewa Isra’ila ta karya dokokin kasashen duniya lokacin da ta hana shigar da kayan agaji ga Falasdinawa a Zirin Gaza. Kotun na mai bayyana cewa akwai wajabci kan Isra’ila na bayar da damar shigar da taimako cikin sauki zuwa yankin, sannan ya zama wajibi ta guji yin amfani da yunwa a matsayin makamin yaki. Kotun ta kuma bayyana cewa Isra’ila na da wajabcin hada hannu da kungiyoyin agaji na MDD, musamman Unrwa. Babban zauren MDD ne ya bukaci kotun ta bayyana ra’ayinta kan lamarin bayan da Isra’ila ta haramta ayyukan hukumar bayar da agajin jin kai ta falasdinawa cewa da Unrwa, tana mai zargin hukumar da hada kai da kungiyar Hamas. Share...
    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi gargadin cewa amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi na samar da kudirorin doka da nufin tsawaita ikon Isra’ila a gabar yammacin kogin Jordan “barazana ne ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya shaidawa manema labarai a lokacin da yake shirin tafiya Isra’ila cewa, ” wannan ba wani abu ne da za mu iya ba da goyon baya gare shi ba a wannan lokaci.” Furin nasa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin Isra’ila ta kada kuri’a kan samar da wani kudirin mallake Gabar Yamma da Kogin Jordan a matsayin yankin Isra’ila. Kudirin wanda wani dan majalisar Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi ya gabatar na zuwa ne...
    Tehran ta yi maraba da hukuncin da wata kotun Faransa ta yanke na yi wa ‘yar kasar Mahdieh Esfandiari saki bisa sharadi. ‘yan sandan Faransa sun dai kama ‘yar Iran din ce bisa zarginta da goyan bayan ta’addanci mai nasaba da nuna goyan bayan al’ummar Gaza . Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran,Esmail Baghaei ya ce Tehran za ta ci gaba da bin diddigin shari’ar Esfandiari, ‘yar kasar wacce malamar jami’a ce mai shekaru 39 da ke zaune a Lyon, har sai ta samu cikakken ‘yanci tare da komawa gida,” in ji Baghaei. Esfandiari, wacce ta zauna a Faransa kusan shekaru takwas, an cafke ta ne a asirce a ranar 1 ga Maris, 2025, wanda ya sa danginta sanar da hukumomin...
    Majalisar tsarin mulki a Jamhuriyar Kamaru, ta ce sai zuwa ranar Litini 27 ga watan Oktoban nan ne za ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar. Majalisar ta sanar da ranar ne bayan ta duba tare da yin watsi da duk wasu kararrakin da suka shafi zaben na ranar 12 ga watan Oktoba. Kafin nan gwamnatin Kamaru ta haramta taron jama’a a birane da dama daga jiya Laraba, gabanin sanar da sakamakon zaben, biyo bayan da madugun ‘yan adawa na kasar Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar. Tun a makon da ya gabata ne magoya bayan Issa Tchiroma, wanda bisa ga kidayar tasa, ya ce ya samu kashi 54.8%...
    Ƙungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa naɗin da aka yi masa na mataimaki na musanman a ɓangaren yaɗa labarai ga shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON),  Abdullahi Usman Saleh. A matsayinsa na ɗan asalin jihar Kano, ɗaukaka darajar Malam Ahmad Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari ne ga masu aikin jarida a jihar. ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe Naɗin nasa ya nuna irin ƙwarewarsa da sadaukarwarsa a ɓangaren yaɗa labarai da yake da shi. Mu’azu kafin wannan muƙamin ya...
    Gaza : Sabani tsakanin Isra’ila, Amurka da Masar kan mataki na biyu na tsagaita wuta Rahotanni daga Isra’ila ne cewa sabani ya kunno kai tsakanin gwamnatin kasar da Amurka da kuma Masar kan mataki na biyu na aiwtar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka cimma. Kafar yada labaran Isra’ila KAN ta bayar da rahoton cewa, an samu rashin jituwa tsakanin bnagarorin dangane da aiwatar da kashi na biyu na shirin shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen yakin Gaza. Kafar yada labaran ta bayyana cewa, sabanin ya samo asali ne yayin wata tattaunawa tsakanin jami’an Isra’ila da babban jami’in leken asirin Masar Hassan Rashad, wanda ya je Isra’ila. Rahotanni sun ce Rashad ya gana da Firaminista Benjamin Netanyahu,...
    Gwamnatin Jihar Ondo ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan gargaɗin da Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi na cewar wasu mayaƙan ISWAP na shirin kai hari wasu sassan jihar. A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Mista Idowu Ajanaku, ya bayyana cewa irin waɗannan rahotanni abu ne na yau da kullum a harkokin tsaro. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani Ya ce hukumomin tsaro suna yawan musayar bayanai irin waɗannan domin daƙile duk wata barazana. Ajanaku, ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnati tare da hukumomin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026.   Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden shiga da kuma rage dogaro da albarkatun mai. Sai dai, jama’a da dama ba su da cikakken bayani game da irin wadannan sabbin haraji ko menene suke nufi ba. NAJERIYA A YAU: Halin Da Muka Shiga Sakamakon Haihuwar ’Ya Mai Cutar Motsewar Kwakwalwa DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Shin ko ta wadanne hanyoyi ne wannan sabon haraji  zai shafi rayuwar...
    A yau Laraba 22 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, huldar diflomasiyya ta shugabanni na matukar taka rawar gani wajen jagorantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma shugabannin kasashen biyu suna ci gaba da cudanya da kuma sadarwa a tsakaninsu. Shugaban Amurka Trump ya ce, yana sa ran kasashen Sin da Amurka za su cimma matsaya kan batutuwan kasuwanci a taron kolin APEC da za a yi a mako mai zuwa, amma ya ce, watakila shugabannin Sin da Amurka ba za su gana ba a lokacin. Guo Jiakun ya yi wadannan bayanai ne a lokacin da yake amsa tambayoyi game da wannan batu, inda ya yi nuni da...
    Ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin mai tsara dabara kan harkokin yada labarai a hukumar alhazai ta kasa (NAHCON). A matsayinsa na dan asalin jihar Kano, daukaka darajar Malam Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari ne ga masu aikin jarida a jihar. ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe Nadin nasa ya nuna aikin ƙwarewa da sadaukarwa a ɓangaren yaɗa labarai da yake da shi. Mu’azu ya taɓa yin aiki a Sashen Hulda...
    Bisa kididdigar da hukumar kula da kudaden kasashen waje ta kasar Sin ta gabatar a yau ranar 22 ga wannan wata, a watan Satumba, yawan kudin da aka yi hada-hadarsu ta fuskar samun kudin shiga da kuma wadanda aka kashe na kamfanoni da daidaikun mutane da sauran hukumomin da ba na banki ba na kasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 1.37, wanda ya karu da kashi 7 cikin dari bisa na watan Agusta. Yawan kudin shiga da na kashewa da ya shafi kudaden kasashen waje na kasar Sin a farkon rabu’i na uku na bana ya kai dalar Amurka triliyan 11.6, wanda ya kai matsayin koli a tarihi, kana ya karu da kashi 10.5 cikin dari bisa na makamancin...
    Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen. Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da ƙasar ta fara warwarewa daga rikicin siyasa kuma ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke taka rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin yammacin Afirka. Jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani A ƙarƙashin mulkinsa, Ivory Coast — wacce ita ce babbar mai...
    A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya sace mata kayanta.   “Abubuwan da aka sace, sun haɗa da iphone 13 Pro Max, an kimanta kudinta akan ₦800,000, kwamfutar ‘Apple MacBook’ da darajarta ta kai ₦250,000, da agogon ‘Apple’ da darajarsa ta kai ₦35,000, ‘power bank’ na Oraimo wanda darajarsa ta kai ₦30,000, da jakar makaranta akan darajar ₦25,000.”   Abdullahi ya ce, nan take jami’an ‘yansanda na shiyyar suka dauki matakin kama...
    Tun daga lokacin da kasar Sin ta fara kera jiragen kasa masu saurin gudu a shekarar 2007 da samfurin CRH1 mai gudun kilomita 250 cikin sa’a guda, ba ta tsaya ba har zuwa yanzu da ta kera wannan sabon na zamani samfurin CR450 wanda shi ma an yi masa tsarin da za a ci gaba da inganta shi. Wannan fasaha wacce ta kara jaddada matsayin kasar Sin na ci gaba da zama jagora a fagen kere-keren jirgin kasa mafi gudu a duniya, ba kasar Sin kawai za ta amfanar ba har ma da sauran sassan duniya musamman a wannan zamani da kasar ta Sin ke kara bude kofarta ga kasashen waje da kuma neman cimma burin samar da al’umma mai...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars October 22, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025
    Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da alkaluman kasuwar yawon shakatawa ta kasar tsakanin watan Janairu zuwa na Satumban bana. Kuma sakamakon binciken kididdigar da aka yi ya nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Satumban bana, adadin yawon shakatawa da mutanen kasar Sin suka yi a cikin gida, ya zarce biliyan 4.998, adadin da ya karu da miliyan 761 bisa na makamancin lokacin a bara, karuwar ma ta kai kaso 18 bisa dari. Daga ciki, adadin yawon shakatawa da mazauna birane da garuruwa suka yi ya kai biliyan 3.789, adadin da ya karu da kaso 15.9 bisa dari. Sai kuma adadin yawon shakatawa da mazauna yankunan karkara suka yi ya kai biliyan 1.209, adadin...
    Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa a nahiyyar Afirka (CAF) ta fitar da sunayen ‘yan takarar da za su lashe kyautar CAF ta shekarar 2025 – rukunin maza. Cikin wata sanarwa da CAF ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce an yi la’akari da rawar da ’yan wasa da masu horarwa suka taka wajen bunƙasa kwallon ƙafa a nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya. Hukumar ta ce fitattun masu takarar sun ba da muhimmiyar gudunmawa a fagen tamaula wanda za a yi la’akari da rawar da suka taka a tsakanin ranar 6 ga Janairu zuwa 15 ga Oktoba, 2025. Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani Waɗanda ke...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Komawar Iran kan teburin tattaunawa da Amurka ya dogara ne kan cimma wasu batutuwa Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta koma kan teburin tattaunawa ba matukar Amurkawa ba za su yi watsi da kwadayinsu na tsarin fadada ayyukansu ba, suna ci gaba da gabatar da bukatun Iran marasa ma’ana. Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne ga manema labarai a yau Laraba a filin tashi da saukar jiragen sama na Shahid Hashemi Nejad da ke birnin Mashhad (gabashin kasar Iran), inda zai karbi bakwancin wani taron shiyya mai taken “Diflomasiya na yankin”. Araqchi ya kara da cewa: Tattaunawar da...
    Mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Qasim al-Araji, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki ya ci gaba da ziyararsa a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, inda ya gana da tattaunawa da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran. Qassem al-Araji mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki ya gana da Manjo Janar Seyyed Abdolrahim Mousavi, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi moriyar kasashen biyu. A yayin ganawar, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Cikakkiyar aiwatar da yarjejeniyar tsaro tsakanin kasashen biyu na da muhimmanci. Manjo Janar Mousavi ya kara...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari kan wasu muhimman wuraren da hatta kawayen haramtacciyar kasar Isra’ila ba su sani ba Tauraron dan Adam na Noor 3 ana daukarsa a matsayin dabara, soja, tauraron dan adam da Iran ta kera wanda ya samu gagarumin ci gaba na bayanai da leken asiri ga sojojin Iran. Masanin tsaro da dabarun yaki Laftanar Janar Abdul Karim Khalaf ya tabbatar da cewa: Tauraron dan adam Noor 3 na Iran yana wakiltar ingantaccen na’ura akan tauraron dan adam na Noor 2, wanda aka kara masa kilo 7 na karin kayan aiki. Tauraron dan Adam na Noor 2 yana da nauyin kilogiram 25, yayin da tauraron Noor 3 ke daukar nauyin kilogiram 32. Abin lura shi...
    Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba.   Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda ke bai wa ’yan kasuwa rancen har zuwa Naira miliyan 5 da kaso tara cikin ɗari (9%) a matsayin kudin ruwa, da kuma Naira biliyan 50 a ƙarƙashin shirin Shugaba kasa Bola Tinubu da ke bai wa ƙanana ’yan kasuwa tallafin kuɗi kyauta bisa wasu sharuɗɗa domin bunƙasa kasuwanci (Presidential Conditional Grant Scheme) da ke ba da tallafin Naira 50,000 ga ’yan kasuwa miliyan ɗaya...
    Shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila ya jaddada cewa: Dole ne a gudanar da bincike kan sakacin Isra’ila har Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 Tzachi Hanegbi, shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila, ya yi kira da a gudanar da bincike kan bala’in gazawar da aka yi a ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023 har kungiyar Hamas ta yi nasarar aiwatar da gagarumar nasara kan Isra’ila. Wannan ya zo ne a cikin kalaman farko da Hanegbi ya yi tun bayan da Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kore shi daga kan mukaminsa. Hanegbi ya ce: “Netanyahu ya sanar da shi yau cewa ya kore shi daga kan mukaminsa.” Ya...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi kira ga Maniyyata Aikin Hajjin 2026 da su biya kafin alkalami nan da ranar 14 ga watan Nuwamban 2025. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ibrahim Datti ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2025. Hukumar wacce ta ce kudin kama kujerar kar su gaza Naira Miliyan Biyu, ta ce Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, na kokarin sama wa Maniyyata rangwame bisa kudin kujera da ta sanar a baya. Ta kara da cewa duk wanda bai biya ba kafin karshen wa’adin da ta bayar, ba zai sami kujerar Aikin Hajjin Bana ba. Har ila yau Hukumar ta ce Maniyyata za su...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar October 22, 2025 Daga Birnin Sin Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa October 21, 2025
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da aniyarsa ta inganta daidaito tsakanin maza da mata da kuma karfafa jagorancin mata a fannin ilimi a Jihar Jigawa. Shugabar Ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Mohammed, ya bayyana hakan a wani taron da HiLWA ta shirya tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai (EU) a Dakin Taro na Manpower Development Institute. Ya ce bincike ya nuna cewa ko da yake mata su ne mafi rinjaye a aikin koyarwa a Jigawa, suna da kaso 14 bisa 100 ne kacal a mukaman shugabanci, kamar shugabar makaranta ko mataimakiya. Wannan, a cewarsa, yana takaita gudunmawar mata wajen tsara manufofi da ci gaban ilimi. Rahama Ya bayyana cewa matsalolin al’adu, tsarin...
    Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta bayyana hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a ƙauyen Essa a Ƙaramar Hukumar Katcha a Jihar Neja, a matsayin abin baƙin ciki da tausayi. Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne, ya yi alhinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II Majalisar Yobe ta nemi a dauki mataki kan yawaitar hadura a hanyar Damaturu–Potiskum Ya miƙa saƙon ta’aziyyae ga gwamnatin Jihar Neja da al’ummarta da kuma iyalan da abin ya shafa. “Wannan lamari abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske. Addu’o’inmu suna tare da iyalan mamatan da kuma jama’ar Jihar Neja a wannan lokaci na...
      A cewar ministan, shirin sake gina bangaren samar da kayayyaki da samar da ci gaba wanda na wucin gadi ne tsakanin manufar bunkasa ayyukan masana’antu ta kasar da wa’adinta ya kare da kuma sabuwar manufa ta shimfida tubali mai kwari ga ajandar bunkasa masana’antu ta kasar.   Ya kara da cewa, bangaren samar da kayayyaki wanda ya mamaye kaso 15.3 na alkaluman GDP na Zimbabwe a 2024, shi ne kan gaba wajen ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar. (Mai fassara: Fa’iza) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da...
    Ahmed maiyaki, ya dade yana bayar da gudummawa a harkar yada labarai a a fadin kasar nan bayan kasancewarsa tsohon ma’aikaci a sashin hausa na rediyon Faransa ( FRI).   Jihar Kaduna ta kwashe shekaru takwas babu ma’aikatar yada labarai wacce tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya rufeta , sai bayan lashe zaben gwamna Uba Sani ya dawo da ma’aikatar wacce aka dorawa alhakin kula da yada manufofin gwamnatin jihar . ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince...
    Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara ta  gargaɗi direbobi da sauran jama’a game da rufe lambobin motoci, musamman a cikin garin Gusau, babban birnin jihar. Gargaɗin ya biyo bayan ƙaruwa da ake samu na rahotanni da kuma lura da direbobi da ke tafiya da lambobin motoci a rufe, wanda rundunar ta bayyana a matsayin karya dokokin hanya da ke kawo barazana ga tsaro da zaman lafiya. A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, rundunar ta bayyana cewa wannan dabi’a tana nuna ƙoƙarin kaucewa binciken jami’an tsaro tare da yiwuwar taimaka wa aikata laifuka. Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya jaddada cewa rundunar...
    Majalisar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 2.55 domin gudanar da binciken na musamman, wanda zai mayar da hankali kan albarkatun mai, gas, da sinadarin uranium, tare da cikakken binciken kimiyyar kasa kan ma’adinai a fadin jihar. A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar, ya bayyana cewa wannan muhimmin shiri na gwamnatin yanzu babban mataki ne na gaba wajen cika alkawarin gwamnati na ganowa da kuma amfani da albarkatun kasa masu tarin yawa da ke cikin jihar Jigawa. A cewarsa, wannan bincike zai samar da bayanai masu muhimmanci game da ma’adinai, da mmn fetur da iskar gas da ke karkashin kasa, wanda zai taimaka wajen yanke shawara mai...
    Majalisar dokokin jihar Yobe, ta yi kira ga bangaren zartarwa na gwamnatin jihar da ta dauki matakan gaggawa domin magance yawaitar haduran ababen hawa a garuruwan Ngelzarma, Damagum da Dogon Kuka da ke kan hanyar Damaturu zuwa Potiskum. Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan gabatar da kudiri da dan majalisa mai wakiltar mazabar Damagum, Maina Digma Gana, ya yi kan yawaitar hadura a wadannan garuruwa. Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II MTN zai rufe ofisoshi 101 a Kano, Borno da Adamawa saboda gyare-gyare Gana, ya bayyana cewa yawaitar haduran ababen hawa a yankin abun damuwa ne, don haka ya zama wajibi gwamnati ta dauki mataki don kare rayukan jama’a. Ya kara...
    “Da ba sojoji, da ba za mu iya gudanar da wannan taro cikin kwanciyar hankali ba. Don haka dole mu ci gaba da ƙarfafa musu gwiwa,” in ji shi. Sarkin Musulmi ya kuma nuna damuwa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo ba tare da tunani ba, inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace don tsara amfani da su, inda ya bayyana cewa shi kansa ya taɓa fuskantar matsala bayan yaɗa labaran ƙarya a kansa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce babu wanda zai yi nasara wajen rusa tarihin Kano da aka kafa tsawon shekaru. Ya bayyana hakan ne a Abuja, a ranar Talata, yayin gabatar da littattafai biyu da Dokta Munzali Dantata, ya rubuta; Behind the City Wall da Aminu Dantata: Life and Times of a Nigerian Entrepreneur. An gano sauro a karon farko na tarihin ƙasar Iceland Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio A cewar Sarkin, tarihin Kano ya samo asali ne daga tsohuwar al’ada ta jajircewa, ilimi, kasuwanci, da ƙwarewa. “Mun zo nan ne don murna, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne muna taya Kano murna, birni wanda ya samar da iyalan Dantata...
    Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma, gwamnan ya gyara Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zamfara (ZACAS). A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama a faɗin jihar. Don rage mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa, ya ɗauki ƙarin ma’aikatan lafiya, tare da samar da magunguna da kayan aiki, tare d harkar kyautata kiwon...