Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Za Ta Karfafa Dangantaka Da NAFDAC
Published: 23rd, October 2025 GMT
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa zata kara karfafa dankon zumunta da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin da mahukunta hukumar NAFDAC suka ziyarce shi a ofishin sa dake Dutse babban birnin jihar.
Ya bayyana farin cikinsa da ziyayar, inda ya jaddada bukatar aiki tare domin cimma dukkan nasarar da ake bukata a tsakanin hukumomin biyu.
Da yake bayani dangane da shirin da hukumar alhazan take yi, Labbo yace dukkanin shirye-shirye sunyi nisa na rigistar kujerun aikin hajji shekarar 2026.
Yana mai cewar, hukumar NAFDAC tana cikin masu ruwa da tsaki na hukumar jin dadin alhazan jihar.
Alhaji Ahmed Labbo, yayi nuni da cewar akowane lokaci za’a iya bukatar tattauna muhimman bayanai na shirye-shiryen aikin hajji domin bada ta su gudunmuwar.
Tun farko a jawabin sa, sabon Shugaban hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC a jihar jigawa, Alhaji Mansur Muhammad yace makasudin ziyarar shi ne domin gabatarwa gami da neman goyan bayan hukumar jin dadin alhazan ta jihar.
Ya kara da cewar, hukumar tana daga cikin hukumomi dake aiki tare da hukumar NAFDAC musamman a lokacin fara jigilar maniyyata.
Mansur Muhammad yace za su ci gaba da bai wa hukumar cikakken hadin kai da goyan baya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Hukumar Alhazai Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Shettima Ya Taya Sarkin Gumel Murna Tare da Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Bunkasa Bangaren Noma
Daga Usman Muhammad Zaria
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yaba da gagarumin cigaba a harkar noma da Gwamna Umar Namadi ya samar cikin shekaru biyu kacal na mulkinsa.
Ya bayyana haka ne a masarautar Gumel cikin Jihar Jigawa, yayin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da Gidauniyar Kashim Shettima ta gina a matsayin wani ɓangare na bikin zagayowar cikar Sarkin Gumel shekaru 45 a kan karaga.
A cewarsa, abin sha’awa ne yadda Gwamna Umar Namadi ya mayar da harkar noma a jihar Jigawa zuwa ta zamani cikin shekaru biyu kacal.
Ya jinjina wa Gwamnan da al’ummar Jihar Jigawa bisa wannan ci gaba mai armashi.
Kashim Shettima ya kara taya Sarkin Gumel, Alhaji Muhammadu Sani, murnar cika shekaru 45 a matsayin Sarkin Gumel, tare da yi masa fatan alkhairi.
Ya tabbatar da ci gaba da jajircewar Gidauniyar Kashim Shettima wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
A jawabinsa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yaba wa Mataimakin Shugaban Kasa bisa kaddamar dadMasallacin.
Ya kuma taya Sarkin Gumel murnar cika shekaru 45 a kan karaga, tare da yi masa fatan alheri.
Shi ma a nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya jinjina wa Mataimakin Shugaban Kasa bisa gina Masallacin Juma’ar.
Namadi ya kuma yaba da jinjinar da VP ya yi kan sauyin da aka samu a harkar noma ta Jigawa, yana mai alkawarin cewa za a cigaba da kara himma a bangaren noma da ma dukkan ababen da za su ciyar da jihar gaba.
Gwamnan ya kara jinjina wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi da sauran manyan baki bisa halartar taro.