Dan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Ce: Dole Ne A Hakunta Isra’ila Kan Laifukan Da Ta Aikata
Published: 26th, October 2025 GMT
Memba a Majalisar Tarayyar Turai ya bayyana cewa: Zaman lafiya na gaske yana buƙatar ɗaukar matakin hukunta Isra’ila
Dan Majalisar Dokokin Turai ta Ireland (MEP) Barry Andrews ya jaddada cewa: Daukan matakin hukunta haramtacciyar kasar Isra’ila kan munanan laifukan da ta aikata a Zirin Gaza ita ce hanya daya tilo da za a cimma zaman lafiya na gaskiya da dorewa, yana mai kira ga Tarayyar Turai da ta ci gaba da zabar sanya takunkumi kan Isra’ila.
Jawabin Andrews ya zo ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu na kasar Turkiyya, wanda ya yi daidai da taron Tarayyar Turai da aka gudanar a Brussels ranar Alhamis da ta gabata, wanda ya tattauna makomar dangantakar Tarayyar Turai da Isra’ila bayan tsagaita wuta na baya-bayan nan a Gaza.
Andrews ya ce, “Kwarewar ƙasarsa a cikin tsarin zaman lafiya na Ireland ya nuna cewa; Ba za a iya cimma zaman lafiya ba tare da adalci da rikon amana ba. Sulhu tsakanin Isra’ila da Falasdinawa yana buƙatar goyon bayan ƙasashen duniya mai ɗorewa, amma ba zai yi nasara ba idan duniya ta yi watsi da laifukan da aka aikata.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Ce: Dole Ne A Hakunta Isra’ila Kan Laifukan Da Ta Aikata October 26, 2025 Mayakan Kungiyar Kurdawa Ta PKK Sun Fice Daga Turkiyya Zuwa Iraki October 26, 2025 Iran Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kungiyar Tattalin Arziki TA “Eco” A Gobe Litinin October 26, 2025 Bahrain: Fursunoni 90 Suna Yajin Cin Abinci Saboda Neman ‘Yanci October 26, 2025 Shugaban Kasar Nigeria Ya Yi Sauye-sauye A Rundunonin Sojan Kasar October 26, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Taron Sherme-Sheikh Ne Saboda Kar Ta Zama Mai Shaidar Zur Akan Kisan Kiyashin Gaza October 26, 2025 Jami’ar ABU Ta Karyata Zargin Da Ake yi Na Kera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 M D D Ta ce Akalla Mutane miliyan 1.5 Ne Ke Bukatar Taimakon Gaggawa A Gaza October 25, 2025 Tony Balai Na Fuskantar Turjiyar Kasashen Larabawa Game Da Rawar Da Zai Taka A Gaza. October 25, 2025 Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Ivory Coast October 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Tarayyar Turai
এছাড়াও পড়ুন:
Antonio Gutrress: MDD Tana Bukatuwa Da A Yi Ma Ta Kwaskwarima
Babban magatakardar MDD Antonio Gutrress ya bayyana cewa majalisar tana da bukatuwa da a yi kwaskwarima da gyare-gyare.
Gutrress dai ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin cika shekaru 80 da kafuwar MDD.
Gutrress ya kuma ce, tare da cewa ayyukan da Majalisar take aiwatarsa suna da matukar muhimmanci,amma kuma halarcinta yana tangal-tangal, sannan kuma ya kara da cewa an dade ana sauraron a yi ma ta kwaskwarima.
A wani sashe na jawabin nashi, ya zargi wasu daga cikin mambobin MDD da cewa a lokuta da dama suna yin abubuwan da suke cin karo da dokokin majalisar, da hakan yake sa ake yin shakku akan ita kanta majalisar ta dinkin duniya.
Har ila yau, Guterres ya ce; Majalisar Dinkin Duniya ba aikinta mamaya ba, kuma ba mallakin wata daula ba ce, tare da yin kira da gyara gibin da ake samu na kasafin kudi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Lebanon: An Sami Shahidai 3 Sanadiyyar Hare-haren HKI A Kudancin Lebanon October 25, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Isra’ila Kan Kasar Lebanon October 24, 2025 Rasha Ta Jaddada Cewa: Kasashen Turai Sun Taka Doka Kan Batun Makamashin Nukiliyar Iran October 24, 2025 Ayatullahi Khatami Ya Ce: Shugaban Kasar Amurka Trump Dan Ta’adda Ne October 24, 2025 Shugaban Amurka Ya Ce: Za Su Dauki Matakin Soji Kan Kasar Venezuela Nan Gaba Kadan October 24, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Yi Allah Wadai Da Mamaye Yankin Yammacin Kogin Jordan Na Falasdinu October 24, 2025 ‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu October 24, 2025 Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada October 24, 2025 Gaza: Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci