2025-11-06@05:48:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11194

«sabon Sarkin»:

    Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci dukkanin kwamandojin rundunar da su ƙara ƙaimi wajen yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta ta sama  A yayin wani taron da suka gudanar da Abuja a ranar Laraba, Aneke, ya umarci kwamandojin da su kai hare-hare masu yawa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa. Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai Ya ce, “Dole ne yayin kowane aiki a nuna ƙwarewa da ƙaunar ƙasa.” Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce taron ya mayar da hankali kan duba dabarun aiki da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin kwamandoji....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta.   A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta. NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Shirin Najeriya  A...
    A yau Laraba 5 ga watan Nuwamba, an bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa (CIIE) karo na 8 a birnin Shanghai. A yayin wani taron manema labarai na yau da kullum da ya gudana a wannan rana, mai magana yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta nuna cewa, nasarar karbar bakuncin bikin baje kolin CIIE tsawon shekaru takwas a jere ta nuna kudurin kasar Sin da ayyukanta na cika alkawarinta na bude kofa, da kuma cimma burin samun moriyar juna da kuma nasara ga kowane bangare. Mao Ning ta bayyana cewa bikin baje kolin na CIIE shi ne babban baje kolin kayayyaki a matakin na kasa na farko...
      “Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.   Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane.   A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani.   An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan...
    Li Chenggang, wakilin cinikayyar kasa da kasa na ma’aikatar kasuwanci kuma mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, ya gana da tawagar cinikayyar kayan noma ta Amurka a birnin Beijing a jiya Talata 4 ga watan Nuwamb, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da cinikayyar kayayyakin noma, da sauran batutuwa masu alaka. Li Chenggang ya bayyana cewa kyakkyawar alaka ta tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka tana da alfanu ga kasashen biyu da kuma duniya baki daya. Tun daga watan Mayu na wannan shekarar, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na bangarorin biyu sun tattauna har sau biyar bisa jagorancin muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda...
    Hukumar shirya gasar ƙwallon yashi ta ƙasa ta tabbatar da cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na bana a filin wasa na Jabi Lake Park, da ke babban birnin tarayya Abuja. Kodinetan hukumar a Najeriya, kuma shugaban hukumar a nahiyar Afirka, Mahmud Hadejia, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da Trust Radio a cikin shirin “Bakin Raga” da safiyar yau Laraba. An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano Shugaban ya bayyana cewa wannan ce gasa ta biyar da za a buga, kuma ta farko da za a fafata a Abuja. A cewarsa, za a fara buga wasannin ƙarshe daga...
    Majalisar Dattawa a ranar Laraba ta amince da kudirin da ke kayyade hukuncin daurin shekaru 14 ga malamai da aka samu da laifin cin zarafin dalibai mata a manyan makarantu. Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke ci gaba da cewa, malamai suna amfani da damar dalibai masu neman maki ko wata alfarma sai su yi lalata da su – wannan matsalar ta tabbata a wani bincike da aka yi a jami’o’in Nijeriya tsawon shekaru, ciki har da binciken sirri na 2019 mai taken “Lalata don samun maki”, wanda ya fallasa cin zarafin da ake yi a wasu jami’o’i. Dokar mai taken ‘Dokar Cin Zarafin Dalibai ta 2025’ (HB.1597), Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta tsakiya)...
    Majalisar Tarayya ta amince da hukuncin cin sarƙa ga duk wani malami da aka samu da laifin cin zarafi ko lalata da ɗalibai a makarantu a faɗin ƙasar nan. Hakan ya biyo bayan amincewar majalisar da Dokar Hana Lalata da Dalibai ta 2025 (HB.1597), bayan tsallake karatu na uku a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilai a ranar Laraba. Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos A ƙunshin bayanan da dokar, za a iya yanke wa duk wanda ya saɓa mata hukuncin ɗaurin shekara 14 ko shekara biyar mafi ƙaranci ba tare da zaɓin biyan tara ba. Laifukan da dokar ta bayyana a matsayin cin zarafi sun haɗa da...
      A gaskiya wannan yanayi ya yi matukar burge ni, kuma sai na zaci ko don saboda ina bako ne, amma yayin da na ga wasu Sinawa suna daukar hotunan bishiyoyin, sai na ce to, babu makawa wannan yanayi ne mai burge kowa da kowa, bako da dan gari kuma ciki har da dattawa. Nan take ni ma na zaro wayata, muka ci gaba da kashe hotuna ni da abokin aikina. Na yi kokarin nuna kawaici a kan yadda yanayin ya shaukantar da ni, amma sai na ga abokin nawa ya fi ni “jazabancewa”, domin shi ya fi ni yawan yin “style” na daukar hoton da kuma yawan hotunan da muka dauka.   Wani abu da na lura da shi...
    Ana fargabar cewa wasu yara biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan faɗawa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu A cewarsa, tsautsayin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 8:53 na safiyar ranar Talata a ƙauyen Kashirmo da ke yankin Sarkakiya na Dawakin Tofa, inda wata yarinya mai shekara takwas mai suna Zara’u Muhammad ta faɗa wata rijiya da ke kusa da gidansu. Duk da ƙoƙarin jama’a na...
    Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta ƙuduri aniyar aiwatarwa.   Shugaban na PMAWCA ya kuma yaba wa gwamnati da mutanen Jamhuriyar Congo saboda ɗaukar nauyin taron kuma ya yaba wa sakatariyar ƙungiyar bisa jajircewa wurin tabbatar da dandamalin tattaunawar tsakanin yankunan da kuma yadda ake samar da sabbin tsare-tsare a shugabancin kungiyar mai kula da teku. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A...
      Haka kuma, kaso 73.2 sun yi imanin cewa manyan kasashe ba sa sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu game da harkokin kasa da kasa, sannan kaso 81.9 sun yi kira ga MDD da ta kara mayar da hankali kan muradu da bukatun kasashe masu tasowa. (FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou November 5, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE  November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025
    Wani jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a shataletalen Abbatuwar Phototake da ke birnin Jos a Jihar Filato. Aminiya ta ruwaito cewa an tabbatar da mutuwar direban da wani fasinja guda ɗaya, tare da jikkatar wasu mata biyu. Shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Laraba, bayan tasowar jirgin daga Bukuru zuwa Jos. Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu Likitoci sun wayar da kan mata kan cutar Sankara a Gombe Wasu mazaunan yankin sun ɗora alhakin faruwar hatsarin kan rashin mutumin da ke kula da shingen tsallaka titin jirgin, wanda ya ratsa titin motoci a daidai shataletalen Abbatuwar Phototake. Sai dai mai magana da yawun...
    Majalisar Dattawa ta dakatar da aikin tantance Dokta Kingsley Tochukwu Udeh, SAN, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa domin zama minista, sakamakon rashin gabatar mata da rahoton jami’an tsaro a kansa. Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce ba za su ci gaba da tantancewar ba sai an samu cikakken rahoto daga hukumomin tsaro. Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano A ranar Talata ce Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar sunan Mista Udeh, ɗan asalin Jihar Enugu cikin wata wasiƙar neman sahalewarta. “Ina farin cikin miƙa sunan Dokta Kingsley Tochukwu...
    Kungiyoyin da suka yi hadin gwiwar shigar da karar sun hada da Interfaith Partners for Peace and Development, Fityanul Islam of Nigeria, Sairul Qalbi Foundation, Tijjaniyya Youth Enlightenment Initiative, Hablullahi Mateen Foundation, Dariqa Qadiriyya of Nigeria, Kadiriyya Youth Awareness, Kadiriyya Riyadul Janna Kofar Na’isa, Ashabul Kahfi Foundation, da Majmau Ashabul Yameen.   LEADERSHIP ta ruwaito cewa, takaddamar da ta shafi Malam Lawan Triumph ta fara ne a watan Satumba bayan da wasu ƙungiyoyin addini suka ɗauki wasu wa’azozinsa a matsayin ɓatanci ga Annabi SAW, wanda ya haifar da cece-kuce da muhawara a faɗin jihar. Wannan lamari ya sa gwamnatin jihar ta shiga tsakani ta hannun Majalisar Shura ta Jiha, wadda aka ba da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen.  ...
      Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Labarai Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista November 5, 2025 Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio November 5, 2025
    Kamfanin dillanacin labarun Faransa ya ambato wata majiyar shari’a tana cewa; ‘yan jaridar da aka kama su ne; Ibro Shu’aibu na gidan talbijin din Sarauniya, sai Yusuf Sariba na wani Shafin watsa labaru na  Niger Ecoh da kuma Umaru Kano na jaridar “Errison.” Dukkanin ‘yan jaridar uku an kai su kurkukun Kolo wanda yake da nisan kilo mita 50 daga babban birnin kasar Yamai. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka kama wadannan ‘yan jaridar da kuma wasu abokan aikinsu. Ana tuhumar ‘yan jaridar da fallasa bayanan gwamnati da shi ne bukatar samarwa da gwamnatin taimakon kudi daga ‘yan kasa. Bayan watsa labarin da aka zargi tashar talabijin din Sarauniya da yi, labarin ya watsu a cikin...
    Jakadan Saudan a MDD Hassan Hamid ya bayyana cewa; KAsarta tana yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kara matsin lamba akan HDL wacce take bai wa rundunar RSF makamai da sauran kayan soja. Hamid wanda ya gabatar da taron manema labaru ya ce: ” Afili yake cewa daga ina ne rundunar RSF take samun makamai,abin takaici kuwa ba daga ko’ina ba ne sai HDL. Jakadan na kasar Sudan  a MDD ya yi kira da dakatar da bai wa wannan kungiyar ta ‘yan ta’adda makamai, ba tare da bata lokaci ba. A can kasar Sudan ana ci gaba da fadace-fadace musamman a yankin Darfur. Kungiyar kare hakkin bil’adama ta MDD ta fitar da bayanin dake cewa; ta sami...
    Kungiyar ‘yan tawayen M23 tare da hadin gwiwar kungiyar AFC sun kafa kotunan shari’a a cikin yankunan da suke iko da su a gundumar Kivu ta Arewa. A garin Goma kungiyar ta sanar da kafa kotuna 378 a fadin yankunan da suke karkashin ikonta, lamarin da gwamnatin Kinshasha ta bayyana a matsyin haramtacce. Wani makusancin kungiyoyin tawayen dake rike da yankunan gabashin DRF, Elie Mutela ya sanar da cewa; Tsarin mulkin kasar ya tabbatar da cewa bai kamata a bar mutane ba tare da tsarin shari’a ba, wannan ne dalilin da ya sa kungiyoyin M23/AFC su ka kafa kotuna domin yi wa mutane shari’a akan matsalolin yau da kullum. Tun a ranar 14 ga watan Satumba ne dai aka fara...
    Shugaban kasar Mali Assimi Goita ya yi wa al’ummar kasar jawabi akan karancin man fetur da ake fama da shi a kasar da kuma yadda masu ikirarin Jihari suke killace motocin dakon makamashi. An fara samun kamfar man fetur ne a kasar Mali wacce ba ta da iyaka ruwa, da masu ikirarin jihadi su ka tare kan iyaka da hana tankokin man fetur shiga cikin kasar. Goita ta bayyana cewa: “ A duk lokacin da za a dauko motocin dakon mai, mutane suna mutuwa, ana yin kwanton bauna akan hanya,ana kona motocin da mutane a cikinsu har su kone kurmus.” Goita ya bayyana haka ne a lokacin dake halartar bikin bude wurin hako ma’adanin “Lithium” a yankin Bougouni a kudancin...
      Firaministan kasar Georgia Irakli Kobakhidze da firaministan kasar Serbia Duro Macu da shugaban majalisar wakilan kasar Najeriya Tajudeen Abbas, sun halarci taron bude bikin tare da ba da jawabai. Haka kuma wakilai kimanin 1500 daga sassan siyasa, kasuwanci da ilmi na kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 155 su ma sun halarci taron.(Tasallah Yuan)   ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025 Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika November 4, 2025
    Ya lura cewa kasashe kamar China, Japan, da Indiya sun cimma gagarumin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da harsunan asali don koyarwa a matakin ilimi na farko.   A cewarsa, koyarwa a cikin harshen Hausa zai inganta fahimta tsakanin dalibai, rage yawan faduwa, da kuma rage yawan wadanda ake kora daga makaranta sakamakon faduwa a jarrabawa.   Bayan tattaunawa, shugaban majalisar Jibrin Ismail Falgore, ya mika kudirin dokar ga kwamitin majalisar mai kula da harkokin ilimi domin ci gaba da bincike da neman shawarwari. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana...
    Ƙungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) tare da Hukumar Ci Gaban Arewa Maso Gabas (NEDC), sun ƙaddamar da yaƙin wayar da kan mata game da cutar sankara a Jihar Gombe, domin kare mata daga kamuwa da cutar. Dokta Halima Usman Faruk, ɗaya daga cikin likitoci mata da suka halarci wajen taron ta ce, cututtukan sankarar nono da bakin mahaifa na kashe mata da dama a duniya, musamman a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya. Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri “A Gombe kawai, ana samun aƙalla sabbin mata bakwai masu fama da sankara a duk mako. “Don haka yana da muhimmanci mata su rika zuwa...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce zai ci gaba da yin siyasa matuƙar yana numfashi a doron duniya. Shekarau ya bayyana cewar siyasa wata babbar hanya ce ta hidima wa jama’a. Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano Yayin da yake hira da ’yan jarida a Kano a yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekaru 70, Shekarau, inda ya ce gina siyasarsa ne bisa tafarkin addini da ɗabi’a. “Siyasata addinina ce, addinina kuma siyasata ce. Shiga cikin tsarin samar da shugabanni na gari masu gaskiya hidima ce ga jama’a kuma wannan ibada ce a Musulunci,” in ji shi. Tsohon...
    Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum,  ya mika motocin sintiri 63 ga hukumomin tsaro da kuma Rundunar Hadin Gwiwa ta Farar Hula (CJTF) da ke aiki a Maiduguri da kewaye. Daga cikin motocin 63, an ba da motocin 30 ga sassa daban-daban na Sibiliyan JTF, 16 ga Jami’an tsaron kai daukin gaggawa don dakile masu aikata laifukan cin Zarafi, 10 ga kungiyoyin tsaro, 6 ga mafarauta da kuma daya ga jami’an Hukumar Kula da Fataucin Mutane (NAPTIP). Rarraba motocin yana da nufin inganta karfin yin sintiri da mayar da martanin gaggawa musamman ga ‘yan sanda, sauran jami’an tsaro, da rundunar hadin gwiwa ta farar hula wajen magance barazanar...
      Haka kuma, daga ranar 10 ga watan Nuwamba, kasar Sin za ta soke matakin da ta dauka a kan wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin kamfanoni marasa aminci da ta sanar a ranar 4 ga Maris na wannan shekara, kamar yadda wani mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana a cikin wata sanarwa.   Mai magana da yawun ma’aikatar ya kara da cewa kamfanonin cikin gida za su iya gabatar da bukata da neman yin ciniki da kamfanonin Amurka da aka ambata a sama da zarar an amince da bukatunsu. (Amina/Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kaddamar...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba wa hukumomin tsaro da rundunar haɗin gwiwa ta CJTF kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Maiduguri. Daga cikin motocin, an bai wa rundunar CJTF guda 30, jami’an tsaro 16, ƙungiyoyin tsaro 10, mafarauta shida, sannan aka bai wa hukumar NAPTIP guda ɗaya. Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka An raba motocin ne domin inganta sintiri da kai ɗaukin gaggawa, domin yaƙi da laifuka da barazanar tsaro irin su ’yan daba da sauran masu aikata laifi a Maiduguri da kewaye. Wannan na cikin irin tallafin da Gwamna Zulum ke bayarwa don inganta tsaro da kare...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa daƙile hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka Mamdani ya zama Musulmi na farko da ya zama magajin garin New York na Amurka Abba ya yi wannan yabo ne, yayin da yake karɓar babban kwamandan rundunar soji ta 1, a Hedikwatar Kaduna, Manjo Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, a fadar gwamnati da ke Kano. Manjo Janar Wase, ya ziyarci Kano domin duba halin tsaro a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa. Ya bayyana yadda mahaifinsa,...
    Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta Super Eagles, Eric Chelle, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Nigeria za ta lashe kofin nahiyar Afrika na 2026. Gasar da za a buga a kasar Maroko, Challe ya jadda kwarin gwiwarsa, bisa kafa hujja da zaratan yan wasan da Nigeria ta ke da su. Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, karo na 35 daga ranar 21 ga watan Disamba da tawagogi 24 za su fafata, domin lashe babban kofin tamaulan na Afirka. Wannan shi ne karon farko tun 1988 da Maroko ta karɓi baƙuncin wasannin babbar gasar tamaula ta Afirka da take fatan gudanar da bikin da zai ƙayatar da duniya.
    Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo sun kama wata mata mai suna Chioma Success mai shekaru 27, bisa zargin kitsa garkuwa da kanta don karɓar kuɗin fansa daga mijinta. An kuma kama wasu mutum biyu da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata laifin, wato Martins Chidozie mai shekaru 23 da Osita Godfrey mai shekaru 33. Mamdani ya zama Musulmi na farko da ya zama magajin garin New York na Amurka Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150 Mataimakiyar Kakakin rundunar a jihar, ASP Eno Ikoedem, ta ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan bincike kan wani rahoton garkuwa da aka kai wa ’yan sanda. Ta ce a ranar 27 ga Oktoba, 2025,...
    Iran ta sanar da yi wa ‘yan faransa nan guda biyu da take tsare saki bisa sharadi a zarginsu da akeyia da yi wa tsaron kasar Iran zagon kasa. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya fitar da bayanin sakin yana mai cewa na yi shi ne  “bisa umarnin alkali.” Ya kara da cewa za su ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar shari’a har sai an ci gaba da shari’a. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da labarin, inda ya bayyana mutanen biyu a matsayin Cécile Kohler da Jacques Paris, wadanda aka tsare a Iran bisa zargin leken asiri. A halin yanzu suna Ofishin Jakadancin Faransa da ke Tehran. A ranar 21 ga Oktoba, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “matukar damuwarsa” kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ke yi akai-akai a zirin Gaza.   Da yake bayyana ga manema labarai a gefen taron koli na biyu na duniya kan ci gaban zamantakewa a Doha jiya Talata, Guterres ya ce: “Dole ne su dakatar da wadannan ayyuka, kuma dukkan bangarorin dole ne su mutunta sharuddan dake kunshe a matakin farko na yarjejeniyar zaman lafiya.” “Muna aiki tukuru don kara taimakawa mutanen yankin Gaza; muna goyon bayan mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dawo da alaka tsakanin Gaza da Yammacin Kogin Jordan,” in ji Mista Guterres. Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani, hare-haren Isra’ila a Gaza...
    A Amurka karon farko an zabi Musulmi Zohran Mamdani a matsayin magajin New York, birni mafi girma a Amurka. Dan takarar magajin gari kuma dan majalisa mai shekaru 34 ya yi nasara a zaben mai zafi wanda ya jawo hankalin duniya. Mamdani ya yi nasara a kan babban abokin hamayyarsa – tsohon gwamna Andrew Cuomo – da akalla kashi 50 cikin 100. Dan majalisar na Democrat ya yi alkawarin duba matsalolin haya da tafiye-tafiye kyauta na bas. A cewar bayanai, matsayin Mamdani kan Isra’ila da Falasdinu ya taimaka masa wajen tabbatar da nasarar farko, duk da ra’ayoyinsa game da yakin, wanda yanzu ake yi wa kallon kisan kare dangi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new...
    Kungiyoyin agaji da dama na kasashen duniya sun yi gargadin cewa tallafin da ake bai wa yankin Gaza bai isa ba kusan wata guda bayan da aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da yankin ke ci gaba da fuskantar matsalar abinci da matsugunai yayin da hunturu ke gabatowa. A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta nuna cewa rabin kayan abinci da ake bukata ne kawai ke isa yankin da aka killace. Abeer Etefa, babban mai magana da yawun WFP, ya bayyana cewa hukumar ta isar da tan 20,000 na abinci, kusan rabin adadin da ake bukata, kuma ta bude wuraren rarraba abinci 44 daga cikin 145 da aka tsara. Ofishin...
    China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar da Amurka ta yi na janye tallafi da kuma daukar matakin soja kan kasar da ke Yammacin Afirka saboda zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci. A kwanan nan ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar “barazana” a Najeriya, yana mai gargadin cewa Amurka za ta iya tura sojoji idan gwamnatin Najeriya ta gaza dakatar da abin da ya bayyana a matsayin ta’addacin masu kaifin kishin islama. Ya kuma sanar da cewa za a saka Najeriya cikin jerin “kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.” ke sa wa ido. Hukumomin Najeriya dai sun yi watsi da wadannan zarge-zargen, suna bayyana su a matsayin marasa tushe a...
    Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025 Manyan Labarai Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
    Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar, duk da suka daga Shugaba Donald Trump da ‘yan Republican, da wasu ‘yan Democrat masu matsakaicin ra’ayi. Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150 An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump A jawabin nasararsa bayan doke tsohon Gwamna Andrew Cuomo, Mamdani ya ce yana da cikakken goyon baya daga jama’a, kuma ya bayyana...
    Daga Khadijah Aliyu  An fara shirye-shirye  gudanar da taron shekara-shekara karo na 2 da bikin shigar da sabbin mambobi na Ƙungiyar Masana Harkokin Yada Labarai ta Najeriya (SNB), bayan an kaddamar da Kwamitin Shirya Taron (LOC) a Kano. An tsara gudanar da taron ne daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamban 2025. Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Umaru A. Pate, ya umarci kwamitin da ya gudanar da aikinsa da himma da jajircewa domin tabbatar da nasarar taron, wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Kano. Ya bayyana cewa ana sa ran masana sama da 400 da sabbin mambobi daga ciki da wajen jihar za su halarta. Farfesa Pate ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano kan jajircewarta wurin...
    Zohran Mamdani ɗan jam’iyyar Democrat ya lashe zaɓen magajin garin birnin New York. Mista Mamdani shi ne musulmi na farko da ya lashe zaɓen maganin garin a tarihin birnin. Ɗan asalin Asiyan shi ne mafi ƙanƙantar shekaru da ya zama magajin garin birnin mai muhimmanci a Amurka. Hakan na zuwa ne a ranar da ake ganin jam’iyyarsu ta yi rawar gani a sauran zaɓukan da aka yi a wasu wurare a Amurka. Mista Mamdani ya yi nasara a kan Andrew Cuomo na jam’iyyar Indifenda da kuma Curtis Sliwa na jam’iyyar Republican wanda ake gani shi ne zai zo na uku a zaɓen. Waɗannan zaɓuka su ne na farko da ake gani kamar wani ƙalubale ne ga gwamnatin Trump. Tuni dai...
    Kungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) reshen Jihar Gombe, tare da hadin gwiwar Hukumar Ci gaba ta Arewa maso Gabas (NEDC), za su gudanar da gwaji kyauta na gano cutar sankarar nono da ta mahaifa ga mata fiye da 500 cikin tsawon kwanaki uku. Wakiliyar kungiyar MWAN, Dr. Hauwa Saurayi, ce ta bayyana haka a hira da manema labarai a Gombe, a cikin shirin bikin Watan Wayar da Kan Jama’a game da Cutar Sankara. Ta ce an shirya gwajin ne domin inganta gano cutar tun da wuri da kuma bada magani cikin lokaci, kasancewar cancer na nono da na mahaifa su ne manyan cututtukan sankara da suka fi addabar mata. Dr. Hauwa Saurayi ta jaddada cewa gano cuta tun da...
    Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla. A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin wani gida, suna harbi a sama, sannan suka tafi da wasu daga cikin mazauna gidan. Daga nan ne rundunar ’yan sanda tare da ’yan banga da masu farauta suka isa yankin cikin gaggawa, lamarin da ya kai ga ceto sun hada da Fatima Wasiu da Kudus Wasiu da jaririya mai watanni shida, ba tare da jin rauni ba. Sai dai har yanzu ana ci gaba...
    Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin dan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu a Jihar Neja, Honarabul Jafaru Mohammed Ali. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a jiya, a kauyen Kubul, kan hanyar Agwara zuwa Babana, a cikin Karamar Hukumar Borgu, yayin da dan majalisar ke hanyarsa ta zuwa ganawa da jama’arsa kan muhimmin shirin ci gaba. Bayan harin, Honarabul Jafaru da tawagarsa sun samu rauni, inda aka garzaya da su asibiti, kuma suna karbar kulawar likitoci a halin yanzu. A halin da ake ciki, jami’an tsaro sun isa yankin domin fatattakar ‘yan bindigar da kuma kare rayukan jama’a. Duk da haka, babu wata sanarwa ta hukuma a hukumance a yanzu game da...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce ta samu amincewar gwamnatin tarayya domin gina sabbin gada biyu na sama da kuma ta karkashin kasa (under-pass) a yankin Mararaba da ke Karamar Hukumar Karu. Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Abdullahi Sule kan Harkokin Jama’a, Mr. Peter Ahemba, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar. A cewar Ahemba, gwamnati za ta fara aikin kafin gwamnatin yanzu ta kai ga karewar wa’adinta a shekara ta 2027. Ya ce tun da dadewa Gwamna Abdullahi Sule ya ware kudaden aikin, kafin ma a kammala tsarinsa. Ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2019, gwamnatin jihar ta kan ** tabbatar da ajiyar kuɗi kafin fara kowanne babban aiki**,...
    Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa gaggawar daukar mataki kan hare-haren ‘yan bindiga da suka faru a wasu sassan jihar. Gwamnan ya yi wannan yabo ne a lokacin da Babban Hafsan Runduna ta 1, wato GOC 1 Division da ke Kaduna, Major Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, ya kai masa ziyara a Gidan Gwamnati Kano. Gwamna Yusuf ya bayyana jin dadinsa da yadda sojoji ke gudanar da aikinsu cikin kwarewau, jajircewa da kishin kasa, tare da bayar da tabbacin ci gaba da hadin kai tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro. Ya kuma gode wa Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu, bisa nada manyan hafsoshi masu kwarewa da suka himmatu wajen yaki...
    Kwamishinan Habbaka kiyon Dabbobi na Jihar Kano, Dr. Aliyu Isa Aliyu, ya fara ziyarar wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a kananan hukumomin Ajingi da Dawakin Tofa. Ziyarar ta yi daidai da shirin gwamnati na kaucewa rikici, musamman sakamakon yuwuwar shigowar makiyaya daga Jamhuriyar Nijar cikin jihar. A Ajingi, Dr. Aliyu ya jagoranci tawaga ta jami’an tsaro, ma’aikatan ma’aikatar da shugabannin kungiyoyin manoma da makiyaya, inda ya bukaci tattaunawa, fahimtar juna da zaman lafiya, domin kauce wa sabani. Wakilin Hakimin yankin, Alhaji Abdulkadir Abdullahi, da shugaban karamar hukumar Dr. Abdulhadi Chula, sun yaba da wannan yunkuri tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kafa ma’aikatar da naɗa kwamishina mai nagarta. A Dawakin...
    Pars Today – Wakilin Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kalaman shugaban Amurka game da gwajin makaman nukiliya a matsayin abin tsoro. A cewar Pars Today, Amir Saeed Iravani, jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, ya rubuta a ranar Talata ga Shugaban Majalisar Tsaro da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a matsayin martani ga kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da barazanar nukiliya, yana mai kiran su “abin damuwa ne kwarai da gaske.” Iravani ya yi gargadin cewa irin wadannan kalamai suna wakiltar babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya kuma suna nuna keta hakkokin Amurka a karkashin dokokin kasa da kasa. Shugaban Amurka ya sanar a ranar 29 ga Oktoba cewa...
    An zabi Zohran Mamdani na jam’iyyar Democrat a matsayin Magajin Garin New York, inda ya kayar da Curtis Sliwa na Republican da Andrew Cuomo dan Takara mai zaman kansa, sannan ya kafa tarihi a matsayin Musulmi na farko kuma magajin gari mafi karancin shekaru a birnin cikin sama da shekaru 100. Mamdani, mai shekaru 34, ya samu kashi 50.4% na dukkanin kuri’un da aka kada, yayin da Sliwa ya samu kashi 41.3%, a cewar sakamakon Hukumar Zabe, Ana sa ran zai fara aiki a ranar 1 ga Janairu 2026. A halin yanzu yana aiki a Majalisar Dokokin Jihar New York, Mamdani yana da alaƙa da Jam’iyyar Democrat Socialist kuma ya kasance mai sukar  manufofin Shugaba Donald Trump. Nasarar da ya...
    Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas Musa abu marzuk ya shaidawa gidan talabijin din Aljazeera cewa  sun yi watsi da batun tura dakarun tabbatar da zaman lafiya zuwa yankin Gaza wadanda zasu yi aiki a madadin sojojin mamayar Isra’ila Yace ba zamu taba amincewa da aikewa da sojojin da za su zama madadin sojojin Isra’ila a gaza ba, Wannan bayanin ya zo ne bayan da kasar Amurka ta fitar da wani daftarin kuduri a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya dake bukatar kafa dakarun tababtar da zaman lafiya na wucin gadi a yankin Gaza, akalla na shekaru 2 adaidai lokacin da falasdinawa ke fargabar tsoma bakin kasashen waje a yankin, Rahotanni da aka fitar ya nuna cewa...
    Gidan talabijin da radiyo na kasar iran ya rattaba hannu kan yarjeniyoyi guda biyar da kafar sadarwa ta kasar Pakistan kan harkokin sadarwa da aladu a wata ziyara da babbar tawagar kasar Iran ta kai birnin Islam abad na kasar Pakistan ,inda ya samu halartar ministan sadarwa da yada shirye shirye na kasar Attaullah Tarar. Wadannan yarjiniyoyin ya nuna irin babban matakin da aka taka a bangaren diblomasiya na sadarwa tsakanin Tehran da kuma Islam Abad, wanda zai kara bunkasa alakar alaadu da sadarwa yadda zaa yi aiki tare a fadin kudancin Asiya. Tawagar kasar iran da Ahmad Norouzi ya jagoranta shugaban bangaren gidajen radiyoyin  kasashen waje na gidan talabijin da redio na kasar iran su ne suka jagorancin sanya...
    Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar Ansarullah Abdul-malik al-houthi yayi gargadin cewa yankin yana gab da fuskantar gagarumin rikici da isra’ila da kasashen yamma a yanki, don haka yasha alwashin cewa  tsayin dakar dakarun kasar yafi karfi fiye da  baya kuma a shirye take ta kalubalanci duk wanda yayi mata shisshigi a nan gaba. Wadannan kalaman suna nuna irin yadda ake samun karuwar fadace-fadace a yammacin asiya yayinda kungiyoyin dake goyon bayan yan gwagwarmayar daga yaman da labanon  ke ciin shirin ko ta kwana na yaki da isra’ila da kawayenta na kasashen turai, haka kuma jawabin ya jaddda irin dabarun yaki da kungiyoyin yan gwagwarmaya da isra’ila suka bi  bayan yakin gaza da kuma sabunta kokarin sojojin Amurka a yankin...
    Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da cewa, daliban jami’a suna ci gaba da karatunsu ba tare da wani cikas ba, yana mai cewa, Gwamnatin Tarayya tana yin duk abin da ya dace don hana Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) tsunduma wani yajin aiki a nan gaba.  Da yake magana da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Talata, Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya umarce shi da ya nemo mafita mai ɗorewa ga duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga ayyukan ilimi a manyan makarantun kasar nan. Kamar yadda na gaya muku, Shugaban Ƙasa ya umarce mu da cewa, ba ya son ASUU ta sake...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon shirinsa na ciyo sabon bashin Naira tiriliyan 1.150, don cike gibin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2025. Buƙatar na kunshe ne cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata. An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump HOTUNA: Mun kori jami’ai fiye da 100 cikin shekara guda — DSS A cikin wasiƙar, Shugaba Tinubu ya ce za a samo bashin ne daga kasuwar bayar da lamuni ta cikin gida. Ya ce buƙatar karbo bashin ta zama dole ne sakamakon ƙarin girman kasafin kuɗin shekarar 2025. Shugaban ya kuma ce an gabatar da...
    Sai dai Sanata Barau Jibrin ya ce, “Ni ɗan Nujeriya ne, kuma zan faɗi ra’ayina. Ba na jin tsoron Trump. Mu ƙasa ce mai cikakken ’yanci.” Maganarsa ta sa wasu Sanatoci dariya kafin Akpabio ya rufe tattaunawar, inda ya roƙi ’yan jarida su tabbatar da sahihancin labarai kafin su wallafa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno November 4, 2025 Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025
    An yi musayar yawu a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kan zargin Shugaban Amurka, Donald Trump, na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Zaman majalisar ya biyo bayan sanarwar Trump da ke bayyana Najeriya a matsayin “Ƙasa Mai Ƙalubale Na Musamman,” yana zargin Gwamnatin Tarayya da bari a ci gaba da kashe Kiristoci a ƙasar. DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Ba addini ne kaɗai ke haifar da rikici a Nijeriya ba — EU Batun ya taso ne a ƙarshen zaman majalisar na ranar Talata, lokacin da Akpabio ya shaida wa ’yan majalisar cewa ’yan Najeriya na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro. ‘Yan bindigar sun yi ikirarin suna samun kimanin naira miliyan 300 duk mako daga haramtattun wuraren hakar ma’adinai. NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Shirin Daga Laraba na...
    Dakta Bukar ya bayyana wannan hadin gwiwar a matsayin abu mai muhimmanci wanda yazo a kan gaba wajen karfafa wayar da kan jama’a game da rawar da sahihan bayanai suke takawa wajen tsara ci gaba da samar da manufofi masu tushe , da dorewar cigaban kasa.   Dakta Bukar, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da kafafen yada labarai wajen isar da bayanan Hukumar ga al’umma.   A cikin jawabinsa, Kwamishinan yada labarai Malam Ahmed Maiyaki, ya yaba da wannan shiri tare da tabbatar da cikakken goyon bayan Ma’aikatarsa ga manufofin Hukumar.   Yace samar da sahihan da kafa gwamnati mai wacce da dogara da adalci yana daga cikin manifofi da kudirorin gwamnatin jihar Kaduna wanda hakan zai taiama wajen kawo...
    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ta fahimci cewa ba addini ne kaɗai ke haifar da rikice-rikice a Najeriya ba. Jaridar Vanguwar ta ruwaito wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar kan harkokin ƙasashen ƙetare, Anouar El Anouni ya fitar, yana cewa ƙungiyar EU na jajanta wa mutanen da rikicin ya rutsa da su a Kudanci da Arewa maso Gabashin ƙasar. HOTUNA: Mun kori jami’ai fiye da 100 cikin shekara guda — DSS Barazanar Trump: Ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Nijeriya — Tuggar Jaridar Vanguard ta bayyana cewa matakin na ƙungiyar EU na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, kan abin da ya kira...
    Cibiyar kandagarki da dakile cututtuka masu yaduwa ta Sin (CDC) ta fara kwas din horon fasahar gwaje-gwaje a kasashen waje a ranar 3 ga wata a hedkwatar CDC ta Afirka. Masana daga gwamnatocin Sin da Afirka da fannin kiwon lafiya, da kuma dalibai 30 daga kasashen Afirka 16, sun halarci bikin bude horon.   An bayyana cewa, wannan horon zai dauki tsawon makonni 3, inda cibiyar Africa CDC za ta taimaka wajen gudanar da shi. Fannonin horon sun hada da binciken kwayoyin cuta, da parasite, da gwajin cutar sida, nazarin kwayoyin halitta wato DNA, da ilimin halittu, da sa ido kan juriyar magunguna, da sauran fannoni masu muhimmanci. Manufar ita ce, horar da daliban da ma’aikatan gwaje-gwaje na Afrika CDC...
      A halin yanzu, sashen saukar kumbuna da dukkan na’urori da tsare-tsaren da ke aikin tallafa wa saukar kumbo suna ci gaba da shirye-shiryen tarbar ‘yan sama jannatin, kamar yadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Kumbuna ta kasar Sin ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar November 4, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya November 4, 2025 Daga Birnin Sin Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa November 4, 2025
    Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota. Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.
    Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa ta sallami jami’anta fiye da 100 a tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025, a wani yunƙuri na aiwatar da gyare-gyare a cikin hukumar. Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, DSS ta ce jimillar jami’ai 115 ta sallama daga aiki saboda dalilai daban-daban da suka shafi aiwatar da tsare-tsaren sabunta tsarin aiki. Fitaccen ɗan wasan tseren motoci Jenson Button zai yi ritaya Barazanar Trump: Ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Nijeriya — Tuggar Sanarwar wadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce an fitar da sunaye da hotunan jami’an da abin ya shafa domin ankarar da jama’a. “A wani ɓangare na ci gaba da aiwatar...
    Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota. Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.
      Ya ƙara da cewa: “Mun cika dukkan buƙatunsu. Yanzu mun koma teburin tattaunawa, yanzu haka na zo wurin shugaba Tinubu ne don zayyana masa inda muka tsaya da ASUU.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai 2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC November 4, 2025 Labarai Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume November 4, 2025 Manyan Labarai Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno November 4, 2025
    Daga Shamsuddeen Mannir Atiku  Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokar kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani ta Jihar Kaduna, wacce za ta taimaka wajen ƙarfafa tsarin fasaha na jihar da inganta gasa a fannin tattalin arziki. Dokar mai taken “Kaduna State Information Technology and Digital Economy Agency and for Related Matters, 2025” ta samu amincewa bayan karatu na uku a zaman majalisar na ranar Talata. Shugaban majalisar, Hon. Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana muhimmancin dokar, yana mai cewa kafa hukumar zai faɗaɗa damar tattalin arziki tare da bai wa jihar Kaduna damar cin moriyar cigaban fasahar zamani a duniya. Ya ce hukumar za ta ƙarfafa kirkire-kirkire, bunƙasa ƙwarewar dijital, da daidaita...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana...
    Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya gargaɗi Shugaban Amurka Donald Trump, kan kada ya ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Najeriya bayan zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar. Mista Tuggar, wanda ya yi jawabi a taron manema labarai a birnin Berlin tare da takwaransa na ƙasar Jamus, Johann wadephul, yana mai cewa Najeriya ƙasa ce mai bin doka da tsarin mulki, wadda ke tabbatar da cikakken ’yancin addini ga dukkan ’yan ƙasa. Dalilin da Trump ya yi iƙirarin ana kisan Kiristoci a Nijeriya — Ndume Ousmane Dembele zai buga wasan PSG da Bayern Munich “Kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin ƙasa sun haramta cin zarafin addini, kuma suna tabbatar da damar...
    Sanata Ali Ndume ya ce jahiltar halin da Najeriya ke ciki ne ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa ana kisan Kiristoci a ƙasar. Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise ranar Talata. Ousmane Dembele zai buga wasan PSG da Bayern Munich ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu Sanatan ya ce maganganun Trump sun nuna rashin cikakken fahimtar yadda matsalar tsaro take da sarƙaƙiya a Najeriya. Ya ce matsalar rashin tsaro a ƙasar ta shafi al’umma baki ɗaya ba tare da la’akari bambancin addini ba, yana mai cewa “mutane daban-daban ne ke...
    A yau Talata ne firaministan Sin Li Qiang, ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya isa birnin Shanghai don halartar baje kolin CIIE karo na takwas. Yayin zantawarsu, Li Qiang ya bayyana aniyar kasar Sin ta karfafa salon wanzar da ci gaba bisa manyan tsare-tsare tare da Najeriya, da zage damtse wajen aiwatar da wasu muhimman matakai goma na bunkasa kawance tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, da hada hannu wajen gina shawarar “Zira Daya Da Hanya Daya” mai inganci, da bunkasa matakin hadin gwiwa a sassan gargajiya, da fadada hadin gwiwa a sabbin masana’antu, da kara kyautata gina tattalin arziki da zamantakewar al’ummun sassan biyu. Li Qiang ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen...
    Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su. China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya tilasta shugaban majalisar da sauran...
    Ya ce, “Wannan ba yana nufin ba a kashe Kiristoci ba ne.” Abin da muke faɗa shi ne, ba Kiristoci kaɗai ake kashewa ba – ana kashe Musulmai ma,”   “Addinan biyu sun tabbatar da hakan, akwai kashe-kashen rayuka da yawa da ke faruwa a Nijeriya tsawon shekaru 16 da suka gabata da kuma fiye da haka daga rikicin Boko Haram a 2009. Babu wanda zai iya musanta hakan.   “Amma a ce kawai ana kai wa Kiristoci hari ya dogara ne da inda abin ya faru. Idan ya faru a yankin da Kiristoci suka mamaye, a zahiri Kiristoci ne za su kasance waɗanda abin ya shafa kamar yadda yake a yanzu a Benuwe da Filato.   “Idan ya faru...
    Kakakin Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususluni na bayyana yaƙin kwanaki 12 kan Iran ya tabbatar da cewa ba za a taɓa amincewa da Amurka ba Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya tabbatar da cewa: Yakin kwanaki 12 da aka yi da Iran ya nuna rashin amana ga masu yanke shawara na Amurka, kuma al’ummar Iran sun san halin da ake ciki kuma sun haɗu wuri ɗaya, inda suka samar da garkuwar da ba za a iya ratsawa ba. Birgediya Janar Ali Mohammad Na’ini, kakakin Dakarun kare juyin juya halin Musulunci {IRGC}, ya yi jawabi ga mahalarta taron gangamin Ranar Yaƙi da Girman Kai na Duniya a Karaj, yana mai nuna godiyarsa ga kasancewar mutane masu aminci...
    Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon ya bayyana cewa; Gwagwarmaya ta tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila rashin girke sojojinta a kan iyakar da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Nabih Berri ya tabbatar da cewa: “Gwagwarmaya ta yi cikakken biyayya ga sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma sojojin Lebanon sun tura sojoji da jami’ai sama da 9,000 a yankin da ke kudancin Kogin Litani.” Ya ƙara da cewa “sojojin suna da ikon tura sojoji a kan iyakokin da ƙasashen duniya suka amince da su tsakanin Labanon da Isra’ila, amma abin da ke kawo cikas ga wannan shi ne ci gaba da mamaye yanki mai girma na kudancin Lebanon da sojojin mamayar Isra’ila suka yi, kamar yadda Rundunar UNIFIL da rahotanninta na...
    Tsohon mataimakin shugaban Amurka da ya kasance wanda ya tsara mamayar Iraki, ya mutu a yau Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney, wanda ya yi aiki a karkashin Shugaba George W. Bush, ya rasu a yau Talata yana da shekaru 84 a duniya, a cewar rahotannin kafafen yada labarai na Amurka. Cheney ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Bush daga 2001 zuwa 2009. Kafafen yada labaran Amurka sun bayyana shi a matsayin babban mai tsara “Yakin Ta’addanci,” wanda ya jagoranci Amurka ta mamaye Iraki a shekara ta 2003 bayan hare-haren 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 da suka kashe dubban ‘yan Iraki. Cheney, wanda kuma ya yi aiki a matsayin Sakataren Tsaro kuma Babban Jami’in...
    Ana ci gaba da tattara gawarwakin mutane da mayakan kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai DaukinGaggawa suka kashe a jihar Arewacin Kordofan na kasar Sudan. Kungiyar Likitoci na Kasar Sudan ya ruwaito cewa: Ana ci gaba da tattara gawawwakin mutane a Arewacin Kordofan, bayan da mayakan Rappid Support Forces suka farma yankunan a kokarin da suke yi na kwace iko da jihar baki daya. Kungiyar Likitoci ta Sudan ta bayyana cewa, tana bin diddigin manyan laifukan da Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces suke aikatawa kan fararen hula marasa makamai a birnin Bara da ke jihar Arewacin Kordofan. Kungiyar ta tabbatar da cewa: Gawawwaki da dama sun taru a cikin gidaje a cikin birnin, kuma mayakan Rapid...
    Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ta sahale wa jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da aka tsara gudanarwa a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025, a filin wasa na Lekan Salami, Adamasingba. A hukuncin da kotun ta yanke, ta umarci jami’an jam’iyyar da wakilanta da su guji duk wani yunƙuri na daƙile ko rusa jadawalin da aka tsara tun farko dangane da taron. Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A. L. Akintola, ta kuma bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) umarnin tura jami’anta domin sa ido da lura da duk abin...
      Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.   Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a Borno. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi  November...
    Ƙasar China ta soki abin da ta kira yunƙurin Shugaban Amurka Donald Trump na yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na Najeriya, inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Mao Ning, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata, a matsayin martani kan barazanar Shugaba Trump ta tura sojojin Amurka zuwa Najeriya domin yaƙi da abin da ya kira kisan kiyashi ga Kiristoci. Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa Trump, wanda ya yi ikirarin cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya, ya zargi gwamnatin Shugaba Tinubu da yin biris da zarge-zargen, yana...
    KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICE Daga Abdullahi Shettima. Hukumar Asusun kula da yara kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince kuma fara aiwatar da shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ga yara kanana (RUTF) wanda hakan ya zama wani muhimmin mataki wajen yakar karancin abinci mai gina jiki tsakanin yara. Da take jawabi yayin wani taron hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kaduna, wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ta bayyana yadda jihar Kaduna ta nuna gagarumar jajircewa a bangaren kiwon lafiya tare da samar da...
    Matsayar da China ta ɗauka na nuna cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Tinubu a lokacin da ƙasashen Yammacin duniya, musamman Amurka, ke matsa lamba kan batutuwan haƙƙin ɗan adam da tsaron cikin gida a Nijeriya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi  November 4, 2025 Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja  November 4, 2025
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington ya samo asali ne daga muradun jama’a, yana mai gargadin cewa duk wani hadin gwiwa da Amurka za a iya cimma shi ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa Isra’ila, ta kuma janye dukkan sansanonin sojinta daga yankin, sannan ta daina tsoma baki a harkokin Iran. Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya bayyana hakan yayin ganawa da wani rukunin dalibai na kasar a jajibirin Ranar Dalibai ta Kasa wacce kuma ta yi daidai da ranar kasa ta yaki da girman kai na duniya. Jagoran ya bayyana ranar a matsayin “ta tarihi” kuma wani muhimmin bangare...
    Kasashen Musulmi bakwai, da suka yi taro a Istanbul a ranar Litinin don tattauna makomar Gaza, sun dage kan cewa Falasdinawa ne kawai ke da hakkin mulkin kansu, inda sukayi fatali da sabon tsarin kafa wata wani kwamitin gudanarwa na kasa da kasa a yankin bayan makonni biyu na tsagaita wutar da akayi wacce ke tangal-tangal. “Dole ne Falasdinawa su mallaki Falasdinawa, kuma Falasdinawa dole ne su tabbatar da tsaron kansu,” in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, ga manema labarai bayan ganawa da takwarorinsa daga Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan, Pakistan, da Indonesia. “Akwai bukatar sake gina Gaza, kuma mutanenta suna bukatar komawa gida inji shi. Ya bayyana fatansa na “sulhu tsakanin Falasdinawa” cikin sauri tsakanin Hamas...
    Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice  daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi  November 4, 2025 Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja  November 4, 2025 Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025
    A Tanzaniyaan rantsar da Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan a wa’adinta na biyu bayan ta lashe zaben da ya haifar da mummunar zanga-zanga a fadin kasar. An ayyana Samia, wacce ta hau mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar magabacinta, a matsayin wacce ta lashe zaben da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi kusan 98.% na kuri’un da aka kada. Tayi rantsuwar kama aikin ne a sansanin sojoji da ke Dodoma, babban birnin kasar. Samia Hassan mai shekaru 65 ta fafata da ‘yan takara daga kananan jam’iyyu, yayin da manyan abokan hamayyarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu aka haramta musu tsayawa takara. Babbar jam’iyyar adawa a kasar ta ce an kashe daruruwan mutane a zanga-zangar. Gwamnati ta yi...
    A Iran dubban ‘yan kasar ne suka taru a Tehran da kuma birane sama da 900 a fadin kasar don tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a 1979, bikin da ake wa lakabi da ‘’Ranar Yaki da Girman Kai ta Duniya’’ A kasar. Dalibai, matasa, malamai, da iyalai ne suka halarci tarurrukan na yau Talata suna masu Allah wadai da ayyukan Amurka da Isra’ila, gami da harin da suka kai wa Iran a watan Yuni. Mahalarta tarukan dauke da tutocin Iran da hotunan wadanda suka yi shahada a hare-haren Isra’ila da Amurka yayin da suke rera taken “Mutuwa ga Amurka” da “Mutuwa ga Isra’ila.” Jami’ai daga cibiyoyin gwamnati da na soji, iyalan shahidai, da tsoffin sojoji yakin da Irak na...
    Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta nuna damuwa kan rahotannin baya-bayan nan na “kasha kashe, fyade, da sauran laifuka” da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta aikata a yankin El-Fasher, na Sudan, tana gargadin cewa wadannan ayyukan na iya zama “laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.” “Irin wadannan ayyuka, idan aka tabbatar da su, na iya zama laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a karkashin yarjejeniyar Roma,” in ji sanarwar da Ofishin Mai Gabatar da Kara na ICC, ya fitar. A cewar sanarwar, wadannan ayyukan sun lalata dukkan yankin Darfur tun daga watan Afrilun 2023,” ranar da aka fara yaki tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Taimakon Gaggawa. A cikin sanarwar, Ofishin Mai Gabatar da Kara ya tuna cewa, a...
    Natasha ta bayyana dakatar da ita a matsayin mataki wanda ba na doka ba, tana mai cewa hakan ya nuna yadda tsoro da barazanar siyasa ke rinjayar halayen jami’an gwamnati. An dakatar da Sanata Natasha a watan Maris saboda zargin da ya shafi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, amma ta koma kujerarta a watan Satumba bayan kammala wa’adin dakatarwar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump November 3, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna November 1, 2025 Siyasa Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar October 31, 2025
    Jami’an tsaro sun kama wani mutum da wayoyin sata guda 17 da kuma kudi a wurin taron sauyin shkear Gwamna Douye Diri daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. A ranar taron, Gwamna Diri tare da yawancin ’yan majalisar dokokin jihar Bayelsa sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC, a gaban Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni da manyan jami’an siyasa na ƙasa. Shugaban sa-kai na jihar, Doubiye Alagba, wanda ya jagoranci kama wanda ake zargin, ya bayyana cewa an mika mutumin ga jami’an Operation Puff Adder na rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. A cewar Alagba, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya...
    Ya kuma tunatar da cewa Nijeriya da Amurka na da kyakkyawar alaƙa tun da daɗewa, don haka bai kamata wannan sabuwar dambarwa ta lalata dangantakar ƙasashen biyu ba. Obi ya ce dole ne a yi amfani da diflomasiyya da tattaunawa wajen shawo kan matsalar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja  November 4, 2025 Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025 Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump  November 4, 2025
    Sarakunan gargajiya, lauyoyi da jami’an gwamnati sun koka bisa yawaitar kananan ’yan mata da ke daukar ciki da kuma zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba, a sansanonin ’yan gudun hijira da ke Maiduguri, Jihar Borno. Lamarin ya fito fili ne a wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da ƙungiyar Grassroots Researchers Association (GRA) ta shirya tare da tallafin We Are Not Weapons of War (WWoW) a karshen makon da ya gabata a Maiduguri. Taron ya haɗa mutane fiye da 500, ciki har da waɗanda suka tsira daga fyade da cin zarafi a lokacin rikici, sarakunan gargajiya, lauyoyi, jami’an gwamnati da abokan ci gaban ƙasa, domin tattauna hanyoyin magance wannan matsala. “’Yan mata kanana na sayar da jikinsu, suna kuma zubar...
    Bayan shafe lokaci, wani jami’in hukumar shige da fice ya dawo mata da fasfo ɗinta. Duk da haka, Natasha ta ci gaba da nuna ɓacin ranta. “Da ban yi bidiyon kai-tsaye ba, da ba za su dawo da min fasfo ba.” A halin da ake ciki, ofishin Akpabio da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025 Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump  November 4, 2025 Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025
    Gwamnatin Chadi ta sanar da rufe iyakarta da Nijeriya nan take, tana mai cewa an dauki wannan mataki ne saboda dalilan tsaro, bayan rahotannin da ke cewa Amurka na shirin kai harin Soji a yankin Yammacin Afrika. Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar damuwa a yankin Sahel. Majiyoyin Soji a N’Djamena sun tabbatar a ranar Litinin cewa Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ya bayar da umarnin kulle iyakar kasar da Nijeriya, bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda daga arewacin Nijeriya na shirin tserewa zuwa cikin Chadi. An ce umarnin ya shafi manyan hanyoyin shiga da fita, musamman ta yankin tafkin Chadi. Rahotanni sun ce an sanya rundunar Sojin...
    Ya ce matsalolin Nijeriya suna buƙatar yin nazari, ba kalaman da za su ɓata lamarin ba. Gwamnan ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da al’umma a Kudu maso Gabas da su haɗa kai domin samun zaman lafiya da sulhu. A cewarsa, tattaunawa, adalci da kyakkyawan shugabanci su ne hanyoyin da za su kawo ƙarshen tashin hankali da dawo da amincewa tsakanin jama’a. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump  November 4, 2025 Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025
    Wata majiya ta hizbbulla  ta fadawa gidan talabijin din al-hadatha cewa kungiyar tana nan kan bakanta na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka sanyawa hannu tsakaninta da isra’ila musamman a yankunan kudancin kasar da kuma tekun litani Duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan decembar shekara ta 2024 amma akwai fargaba sosai  a iyakokin labanon da Isra’ila , sai dai hizbullah ta fitar da sanarwa a baya bayan nan wanda ke nuna shirinta na mayar da martani mai tsanani idan israila ta tsokaneta, duk da kasashen yamma na kokarin ganin an kawar da makamai da kuma rage tasirinsu,  adaidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yiyuwar sake barkewar wani rikici Ministan...
    Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa bayanan baya bayan nan da hukumar kula d makamashin nukiliya ta duniya  da ministan harkokin wajen Oman suka fitar na cewa iran bata kokarin kera makamin nukiliya ya karyata ikirarin da Amurka da HKI ke yi kan shirin nata. Babban darakata janar na hukumar IAEA a baya bayan nan ya fayyace cewa iran bata kokarin kera makamin nukiliya da kuma kasar Oman babbar mai shiga tsakanin da aka amincewa tsakanin iran da Amurka, yace wadannan kalamai zasu iya bude kofar sake koma teburin tattaunawa tsakanin Iran da kuma kasashen duniya. Rafeal Grossi ya fitar da sanarwar cewa iran bata neman kera makamin nukiliya shi ma ministan harkokin wajen oman Al-busaidi...
    Prime ministan kasar sudan Kamil idris yayi gargadin cewa aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasashen waje a kasar Sudan  zai kara ruruta wutar rikicin ne da kuma keta yancin kasar, kuma kalaman nasa suna cewa ne bayan rahoton da aka fitar game da cin zarafin dan Adam da aka yi a El-fasher dake arewacin Darfur. Sudan ta dade tana cikin rikci wanda ya haddasa yunkurin juyin mulki sau 20 a kasar da kuma yakin basasa guda biyu, lamarin ya kara taazzara ne bayan rikicin da ya barke a baya bayan nan, wanda ke barazanar ga zaman lafiya yankin , sai dai har yanzu kasashen duniya basu cimma matsaya ba kan yadda zaa samar da zaman lafiya mai...
    rahotanni suna nuna cewa mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin  tsaro Malam Nuhu Ribadu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da jagororin sassan tattara bayanan sirri kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump. Trump ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ya ce yana so gwamnati ta dauki matakin gaggawa ko kuma ya turo sojoji domin su yaki maharan da ya bayyana da ƴanbindiga masu ikirarin jihadi. A sanarwar, ya ce, “na ba sashen yaki umarni su fara shirin daukar mataki. Idan har za mu kai hari, to za mu kai harin ne cikin sauri ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda ƴan ta’addan nan suke kai hari kan kiristoci,” in ji...
    Ya jaddada cewa gwamnati tana tabbatar da tsaron kowa ba tare da bambanci ba. Kalaman Trump sun haifar da ruɗani da cece-ku-ce a tsakanin ‘yan Nijeriya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025 Manyan Labarai Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi November 3, 2025
    Gwamnatin Kaduna Da Hadin Gwiwar UINL Da FHFL Sun Gina Gidaje 100 Ga Mutanen Da Rikici Ya Raba Da Muhallans Daga Abdullahi Shettima Gwamnatin Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar kamfanin Ummi International Nigeria Ltd (UINL) da Family Homes Funds Ltd (FHFL), bisa tallafin Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi ta Tarayyar Najeriya, sun kammala ginin gidaje 100 domin mutanen da rikici ya raba da muhallansu da kuma marasa galihu a cikin jihar. Wannan aiki ya gudana ne a yankin Rigachikun, inda kamfanin Ummi International Nigeria Ltd ya bayar da fili, yayin da Gwamnatin Kaduna, Family Homes Funds, da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare suka ɗauki nauyin ginin gidajen gaba ɗaya. A yayin ƙaddamar da ginin da kuma miƙa ma waɗanda...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta sanar a yau Litinin cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, sarkin Spaniya Felipe VI, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, daga ranar 10 zuwa 13 ga watan nan na Nuwamba. (Mai fassara Bilkisu Xin) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce November 3, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau November 3, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai November 3, 2025
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na fadada ayyukan ci gaban karkara, tare da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma. Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin jami’in kula da shirin rage radadin illar da annobar cutar Korona ta haifar, wato (NG-CARES), Dakta Abdulkareem Obaje, wanda ya kai masa ziyara ta ban girma a Dutse. Dakta Obaje ya yaba wa gwamnan da gwamnatin jihar Jigawa bisa goyon bayan da suke bai wa shirin NG-CARES tun daga lokacin da aka ƙaddamar da shi a shekarar 2021. Ya bayyana cewa an kirkiro shirin ne a shekarar 2020 sakamakon tasirin annobar COVID-19, domin taimaka wa jihohi su...