Aminiya:
2025-12-10@23:25:57 GMT

NSCDC ta yi alhinin mutuwar Kwamishinan Tsaron Gombe

Published: 26th, October 2025 GMT

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Gombe, ta bayyana alhini bisa rasuwar Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (mai ritaya).

Haka kuma hukumar ta bayyana jimami kan da ɗan sandan da ke tsaron kwamishinan, Sajan Adamu Husaini, da direbansu, wadanda suka rasu a wani mummunan hadarin mota da ya afku ranar Juma’a.

Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa 

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar, Kwamandan hukumar, Jibrin Idris, ya ce rasuwar babban rashi ce ba ga iyalan mamatan kawai ba, har ma ga Gwamnatin Jihar Gombe da al’ummar jihar baki ɗaya.

Kwamandan ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, da iyalan mamatan da abokan aikinsu, yana mai jaddada irin jajircewar da suka nuna wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

“Kwamishina Abdullahi Bello da Sajan Adamu Husaini da direbansu sun bayar da gudunmawa mai muhimmanci ga sha’anin tsaro a Gombe. Rasuwarsu babban rashi ne ga kowa da kowa,” in ji Kwamandan Idris.

Ya yi addu’ar Allah Ya jikansu, Ya ba su Aljannatul Firdausi, tare da ba iyalan da suka bari hakurin jure wannan babban rashi.

Laftanar Kanar Abdullahi Bello kafin rasuwarsa, shi ne Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Gombe, wanda aka san shi da jajircewa da kishin kasa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: jihar Gombe Kwamishina Jihar Gombe

এছাড়াও পড়ুন:

Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Jamhuriyar Benin – Soyinka

Marubuci kuma mai lambar yabo ta Nobel, Wole Soyinka, ya ce kamata ya yi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tura ɗansa, Seyi Tinubu, zuwa Jamhuriyar Benin domin “kwantar da” yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

Soyinka ya soki matakin Tinubu na tura dakarun rundunar Sojojin Sama ta Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi domin kifar da Shugaba Patrice Talon daga mulki.

Ya yi wannan jawabi ne a bikin bayar da kyaututtuka na shekara karo na 20 da Cibiyar Binciken Kwakwaf ta Wole Soyinka (WSCIJ) ta shirya a Legas ranar Litinin.

Fitaccen marubucin ya tuna yadda ya ga jami’an tsaro masu makamai sosai suna gadin Seyi Tinubu a Legas.

Ya ce: “Shugaba Tinubu bai kamata ya tura Sojojin Sama da na ƙasa ba domin shawo kan wannan tayar da hankali da ke barazana ga tsaronmu da daidaituwarmu; a’a akwai hanyoyi mafi sauƙi na yin hakan.

“Bari in gaya muku inda Tinubu ya kamata ya nemi rundunar da za ta shawo kan wannan tayar da hankali, na nan a Legas ko ma a Abuja, amma babu buƙatar kiran sojojin ƙasa ko na sama.

“Zan gaya muku abin da ya faru a ɗaya daga cikin ziyarata zuwa gida watanni biyu da suka gabata, ina fita daga wani otel sai na ga abin da ya yi kama da wurin yin fim, wani matashi ya rabu da ’yan wasan ya zo ya gaishe ni cikin ladabi.

“Na kalli wurin sai na ga kusan rundunar sojoji ce gaba ɗaya sun mamaye filin otel ɗin a Ikoyi. Na koma cikin motata na tambaya wanene wannan matashin, sai aka gaya min.

“Na ga sojoji, haɗin jami’an tsaro masu makamai sosai, akalla 15 suna ɗauke da manyan makamai, abin da ya isa ya tsare karamar makwabciya kamar Benin.

“Na yi tunanin cewa a gaba mai girma shugaban ƙasa ya kamata kawai ya kira ya ce ‘Seyi je ka kwantar da fitina a can’. Na yi matuƙar mamaki har na fara neman Mashawaracin Shugaban Kasa a fannin tsaro,” in ji Soyinka.

Soyinka ya kuma ce ba Tinubu ne shugaban da ya fara mulkar Najeriya yana da ’ya’ya ba, don haka bai ga dalilin da zai sa a girke tarin jami’an tsaro kawai don su rika gadin dansa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji
  • Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Ta Taya Oluremi Tinubu Murnar Nadin Sarauta a Ile-Ife
  • Kasar China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Babban Jami’in Banki
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Jamhuriyar Benin – Soyinka
  • Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC
  • Gwamnonin Arewa Za Su Zuba Biliyoyin Naira Don Yaki da Matsalar Tsaro
  • Zaben 2027: NNPP Ta Sha Alwashin Maye Gurbin Tinubu da Radda
  • ASUU-SSU Ta Zargi VC Da KaryDokokin Jami’ar Jihar Sakkwato
  • An kama tsohon fursuna ya je fashi da bindiga AK-47