‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu
Published: 24th, October 2025 GMT
‘Yan sandan kasar Ghana sun sanar da cewa tserato da wasu ‘yan Najeriya 57 da aka yi faskwaurinsu, haka nan kuma wasu mutane 5 da suke aikata laifuka ta hanyar sadarwar na “Internet”
Jami’an ‘yan sandan sun kwace nau’ra mai kwakwalwa 77 da wayoyin hannu 38, sai kuma wasu motoci 2, akwatin talbijin 3, da kuma wasu na’urori da suke amfani da su a yaudarar mutane.
A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an ‘yan sandan kasar ta Ghana su ka sanar da kai farmakin a birnin Accra a ranar Laraba 22 ga watan nan na Oktoba.
Shekarun mutanen da ake amfani da su wajen yaudarar mutane ta hanyar internet suna a tsakanin 18 zuwa 26,tuni kuma an kai su asibiti domin kula da su.
Ana amfani da mutanen da aka kama ne dai ta hanyar karuwanci domin yaudarar mutane.
A watan da ya shude ma dai, ‘yan sandan kasa da kasa -Interpol- sun sanar da kama 260 a cikin kasashen Afirka 14 da suke aikata laifuka irin ta hanyar internet. Mutanen kan dauki hotunan tsiraici na mutanen da suke son cutarwa, domin daga baya su rika karbi kudi a wurinsu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada October 24, 2025 Gaza Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Akan Yara Da Matan Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaron kasashen pakistan da Afghanistan sun yi musayar wuta mai tsananin a iyakokin kasashensu, kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 5, hakan na nuna irin rikicin dake tsakanin kasashen masu makwabtataka da juna, bayan sun cimma yarjejeniyar sulhu a kasar saudiya amma da alama babu ci gaban da aka samu.
A wani sakon da kakakin gwamnatin Taliban ya wallaka a shafinsa na x zabihullah majahid yace sojojin kasar Pakistan sun kaddamar da hari a wani yanki dake lardin kandahar na kasar Afghanistan da hakan yasa sojojin su mayar da martani.
Sai dai ana sa bangaren firaministan kasar Pakistan Shebaz sharif ya ce sojojin kasar afgahnistan ne suka fara harbe harbe a iyakar chaman,
Dangantaka tsakanin Afghanistan da Pakistan ta kara tabarbarewa ne a yan watannin baya bayan nan, inda rikici ya kara Kamari tsakaninsu a iyakokin kasar duk da tattaunawar sulhu da ka yi a a Qatar da kuma na bayan bayanna a kasar saudiya amma har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Masar Sun yi Kira Da Kawo Karshen Keta Hurumin Gaza da Labanon da Isra’ila ke yi December 6, 2025 Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba December 6, 2025 Gwamnatin Najeriya Za ta Karbi Sabon Bashin Dala Miliyan 500 A Bankin Raya Kasashen Afrika December 6, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Sun Yi Gargadi Game Da Yunkurin Isra’ila Na Kashe Barghusi December 6, 2025 Gasar FIFA: Iran Ta Fada Cikin Group Mai Sauki A Gasar Kwallon Kafa Ta FIFA 2026 December 6, 2025 Kasashen Musulmi 8 Sun Ki Amincewa Da Korar Falasdinawa Daga Gaza December 6, 2025 Sojojin Afganistan Da Pakistan Sun Yi Musayar Wuta A Tsakaninsu Duk Tare Da Tsagait Wuta December 6, 2025 Rasha Tace Ta Kakkabo Jiragen Drones Na Ukrai 116 A Daren Jiya December 6, 2025 ‘Yar Iran ta isa wasan karshe na gasar cin kofin duniya na wasan harbi a karo na 4 December 6, 2025 Iran da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi 20 da kwangiloli 5 a fannin fasaha December 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci