Aminiya:
2025-12-10@05:34:31 GMT

ABU ta musanta zargin ƙera makamin nukiliya a ɓoye

Published: 25th, October 2025 GMT

Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU,  ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta, cewa tana aikin ƙera makamin nukiliya a ɓoye a cikin jami’ar.

A wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jami’ar, ƙarƙashin Malam Auwalu Umar, ya fitar, jami’ar ta bayyana cewa labaran da ake yaɗawa ba su da tushe balle makama.

Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum ’Yan sanda sun taimaka wa ’yan daba rusa gidaje — Al’ummar Shendam

“Mun lura da wani faifan bidiyo da na’urar AI ta ƙirƙira, wanda wasu ke yaɗawa suna iƙirarin cewa ABU na ƙera makamin nukiliya a ɓoye. Wannan ƙarya ce babu gaskiya a cikinta,” in ji sanarwar.

An zargi jami’ar da “ɓoye aikin uranium” tun a shekarun 1980, tare da iƙirarin cewa “masu bincike a ABU sun gina injin centrifuge daga Pakistan kuma suna dab da kammala makamin nukiliya a 1987.”

Jami’ar ta bayyana cewa waɗannan zarge-zargen ƙarya ne, domin a wancan lokacin, yawancin masana kimiyyar da ke Cibiyar Binciken Makamashin Nukiliya a Jami’ar (CERT) suna karatu a waje, kuma ba su dawo gida ba sai farkon shekarun 1990.

“Ba mu da wata alaƙa da Pakistan ko AQ Khan Network. CERT ma ba ta da cibiyar nukiliya mai aiki a 1987, sai injin ‘14 MeV Neutron Generator’ wanda aka fara amfani da shi a 1988,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa shirin farko na binciken nukiliya a Najeriya ya fara ne a 1996, karkashin haɗin gwiwa da hukumar IAEA, wanda ya kai ga ƙaddamar da injin bincike na farko a Najeriya (Nigeria Research Reactor-1) a 2004.

Tun a 1968, Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya (NPT), kuma tana amfani da fasahar nukiliya ne don zaman lafiya kawai.

A tarihin ABU, tun daga kafa ta, ta kasance cikin sahun gaba wajen bincike a ilimin kimiyya domin ci gaban al’umma, ba wai samar da makami ba.

“CERT ta ABU tana aiki ne tare da IAEA da ƙasashen Amurka, Rasha, da China don bunƙasa amfani da makamashin nukiliya cikin lumana.

“Ba mu da masana’antar sarrafa uranium, kuma duk abin da ake amfani da shi ana sarrafa shi a ƙasashen waje,” in ji jami’ar.

Jami’ar ta nanata cewa duk wani aiki da take yi na nukiliya ana gudanar da shi ne cikin gaskiya da amincewar hukumomin duniya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Makamin nukiliya zargi makamin nukiliya a

এছাড়াও পড়ুন:

Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin

Aƙalla sojoji 13 aka cafke a ƙasar Benin bayan yunƙurin da juyin mulki da suka yi bai yi nasara ba.

Majiyoyin tsaro da na soja sun bayyana cewa dukkan waɗanda aka kama sojoji ne masu aiki a halin yanzu, sai mutum ɗaya da ya taɓa yin aiki a rundunar amma ya yi ritaya.

Kama su ta biyo bayan sanarwar da aka yi a talabijin na ƙasar da safiyar Lahadi, inda sojojin suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da rushe dukkan cibiyoyin gwamnati.

Jami’an da suka kira kansu Kwamitin Soja na Sake Tsarawa, sun ce sun karɓe mulki, sun rufe iyakokin ƙasar tare da dakatar da jam’iyyun siyasa.

Sai dai fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Shugaba Talon yana cikin ƙoshin lafiya, kuma dakarun da suka tsaya kan gaskiya na dawo da doka da oda.

Gwamnati ta bayyana lamarin a matsayin aikin “tsiraru  mutane” da ba su da tasiri.

“Wasu ’yan tsiraru ne kawai da ya mamaye talabijin. Rundunar sojan ƙasa na sake karɓar iko. Birnin da ƙasar gaba ɗaya suna cikin tsaro,” in ji sanarwar fadar shugaban ƙasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa”
  • ASUU-SSU Ta Zargi VC Da KaryDokokin Jami’ar Jihar Sakkwato
  • Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah
  • Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin
  • An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja
  • Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi)
  • Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166