An saki Ɗan Uwa Rano bayan tsare shi kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano
Published: 19th, October 2025 GMT
’Yan Sanda sun saki ɗan jaridar Kano, Ibrahim Ɗan Uwa Rano, bayan tsare shi da suka yi kan zargin ɓata sunan hadimin Gwamnan Jihar, Abdullahi Ibrahim Rogo.
An tsare Rano a Shiyyar ’Yan Sanda ta Ɗaya da ke Kano, bisa zargin ɓatanci.
Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku ’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan KanoƘungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana tsare shi a matsayin saɓa doka da kuma ƙoƙarin danne ’yancin ’yan jarida.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda cin zarafi Ɗan Uwa Rano Hadimin Gwamna
এছাড়াও পড়ুন:
Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na shirin sayen jirage marasa matuƙa da wasu kayan aiki domin kare yankunan da ke iyakar Kano da Katsina.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000Gwamna Abba, ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci sansanin rundunar haɗin gwiwa ta JTF, domin ganin yadda suke shirin kare al’umma daga hare-haren ’yan bindiga a yankunan Tsanyawa da Shanono.
Ya roƙi al’ummar yankunan da abin ya shafa da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani game da duk wani motsi na ’yan bindiga.
Gwamnan ya ce ya kai wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ziyara, domin neman taimako kan lamarin, inda shugaban ya amince da buƙatar da aka gabatar masa cikin gaggawa.
Ya umarci dakarun JTF da su yi duk mai yiwuwa wajen ceto mutanen da aka sace a Tsanyawa da Shanono.
“Mun san cewa waɗannan hare-hare sun jawo asarar rayuka, wasu kuma an yi garkuwa da su. Insha Allah za a ceto su,” in ji shi.
Gwamna Abba ya ce sun kai wannan ziyara ne domin fahimtar halin tsaron yankin da kuma ƙarfafa guiwar jami’an tsaro.
Ya ƙara da cewa irin wannan matsalar tsaro sabon abu ne a Kano, amma gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro domin magance ta.
A yayin ziyarar, ya jajanta wa iyalan mutanen da aka sace tare da tabbatar musu cewa gwamnati na ƙoƙarin ganin an dawo da su cikin gaggawa.
Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutum 10 aka sace a Tsanyawa da Shanono, ciki har da wata tsohuwa da ’yan bindiga suka hallaka.