Aminiya:
2025-10-27@14:07:14 GMT

Paul Biya mai shekara 92 ya lashe zaɓen Kamaru

Published: 27th, October 2025 GMT

Shugaba Paul Biya na Jamhuriyar Kamaru ya sake lashe zaɓen Shugaban Ƙasar domin fara wa’adi na takwas na shekara bakwai.

Kotun Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ta sanar cewa Mista Paul Biya mai shekaru 92 ya samu nasara ne bayan ya samu 53.66 na kuri’un da aka jefa a yayin da babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35.

19.

Da haka biya zai ci gaba da mulki inda zai kammala sabon wa’adin yana dan shekara 99.

Zuwa ƙarshen wa’adin, Biya wanda ya shekara 43 a gadon mulki tun 1982 zai cika shekara 50 a kan mulki.

A halin yanzu shi ne shugaban kasa mai ci mafi tsufa a duniya.

Shi ne kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na biyu a tarihin Kamaru tun bayan samun ’yanci daga Turawan mulkin mallaka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Biya Issa Tchiroma Bakary Kamaru Paul Biya Zaɓe

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙaddamar da Kyautar Jaruman Indomie Karo Na 17 Yayin Da Zakarun Matasa Suka fafata daga karshe an samu zakaru

An Kammala bikini bada Kyautar Jaruman Indomie Karo Na 17, An Girmama Matasan da suka nuna hazaka Kuma wadanda suka kasance jakadun Najeriya.

Wannan gagarumin biki ɗaya gudana a Lagos, Najeriya, a ranar 16 ga watan Oktoba, 2025: kamfanin Dufil Prima Foods, masu yin Indomie Instant Noodle suka shirya karkashin shirinsu na kyautata alaka da Al’umma na Kamfanin Indomie, sun tabbatar da bada Kyautuka ga Jaruman Indomie, wani mataki na daraja, wadanda suka nuna jarunta bisa ayyukan jarumtaka da sukayi, ta hanyoyi daban daban da suka kunshi kirkire-kirkire na yaran Najeriya.

An gudanar da wannan taro a Legas, inda gasar karshe ta wannan shekarar, mai taken “Jaruman da ba a San Su ba” inda fitattun matasa uku ‘yan Najeriya wadanda labaransu na jarumtaka suka shahara bisa baiwarsu da girman na jarumtaka da halayya na gari da suka nuna.

Daga 11 zuwa 13 ga Oktoba, 2025, miliyoyin ‘yan Najeriya sun saurari shirye-shiryen talabijin na kasa don shaida labaran da ke motsa rai da kuma karfafa gwiwa na wadannan yara masu ban mamaki.

L-R: Tomike Adeoye, Host and Media Personality; Mr. Temitope Ashiwaju, Group Corporate Communications and Events Manager, Dufil Prima Foods; Sola Salako Ajulo, Member, Competition and Consumer Protection Tribunal and Founder, Consumer Advocacy Foundation of Nigeria (CAFON); Nyma Akashat Zibiri, Nigerian Lawyer and co-host on TVC’s Your View; Karishma Rustagi, National Coordinator, Indomie Fan Club; Ayisat Agbaje-Okunade, Executive Secretary
Lateef Jakande Leadership Academy and Mr Kehinde Adegboyega, Executive Director, Human Rights Journalists Network Nigeria, at the just concluded 17th edition of the Indomie Heroes Awards, held recently in Lagos.

Bayan wani tsari mai kyau na zaɓe a duk faɗin ƙasar Nan da ya haɗa da hirarraki da al’umma da tantance makarantu, da kuma bincike na waɗanda suka yi nasara a rukuni uku sun fito kuma an karrama su da suka hada Abraham Umoren, mai shekaru 9, daga Jihar Akwa Ibom, wanda ya lashe gasar nuna jaruntaka wato Physical Bravery, da Ismail Muhammad, mai shekaru 13, daga Jihar Kwara wanda ya lashe gasar nuna jaruntaka da muamala wato Social Bravery, da Hassan Adamu, mai shekaru 15, daga Jihar Yobe, wanda ya lashe gasar ganinta a bangaren Basira wato Intellectual Bravery.

An zaɓi waɗannan jaruman matasa daga dubban matasa da aka gabatar daga ko’ina cikin Najeriya, bayan watanni na tantancewa da tabbatarwa daga hukumomin bincike masu zaman kansu waɗanda kamfanin Dufil Prima Foods ya samar.

Da yake magana a ƙarshen bikin Karo na 17, Temitope Ashiwaju, Manajan Sadarwa na Rukunin Kamfanoni, Dufil Prima Foods, ya ce, “Kowace shekara, muna Masu lura da zurfin jarumtaka da, fasaha, da yaran Najeriya suke nuna da Kuma tallafa Masu amatsayin gudunmawa da zamu bada ga bunkasa cigaban matasan.

Wannan Kyautar Jaruman ta Indomie ta fi karfin bikin baje koli kawai domin madubi ce da ke nuna makomar Najeriya.

Waɗannan labaran suna tunatar da mu cewa ba a bayyana jarumtaka ta hanyar shekaru ko matsayi ba, amma ta hanyar ayyukan waɗanda ke ɗaga matsayin wasu.

Zakarun matasa, sun nuna farin ciki da godiya bisa wannan dama da kamfanin indomie ya basu suka nuna hazakarsu.

Kowannensu ya gode wa Indomie saboda wannan karramawa kuma ya yi alƙawarin ci gaba da yin abubuwan masu na gari a cikin al’ummominsu don zama abin kiyi ta hanyar amfani da baiwarsu don ƙarfafa takwarorinsu matasan Nigeriya a Nan gaba.

Ba mu taɓa tsammanin za a yi irin wannan bikin ba,” in ji Abraham Umoren. Inda yace “Na gode, Indomie, Kuma zan ci gaba da taimaka wa wasu gwargwadon iyawata.”

Shekarar 2025 an gabatar da wannan bikin na girmamawa na matakin jiha a karon farko, inda aka girmama waɗanda suka zo na hazaka daga kowane rukuni da kuma faɗaɗa damar da aka samu don girmama ƙarin matasa masu kawo sauyi a faɗin Najeriya.

Tun lokacin da aka fara wannan biki a 2008 ta Jaruman Indomie jarumai matasa 59 na Najeriya, suka amfana da miliyoyin naira amatsayin tallafin karatu, ga waɗanda suka nuna jarumtaka, don basu ƙarfin gwiwar don cigaban al’umma baki ɗaya.

An yada wannan bikin bayar da kyaututtukan a duk faɗin ƙasar nan wanda ya bai wa iyalai da malamai, da shugabanni damar shaida labaran da ke ci gaba da ƙarfafa bege da juriya a cikin al’ummomi.

Kyautar Jaruman Indomie bata tsaya a matsayin shaida ga jajircewar Kamfanin Dufil Prima Foods Wanda ya daɗe yana ƙoƙarin haɓaka tsarin shugabanci, da nuna tausayi, da kuma kishin ƙasa a cikin ingantattun tsare tsarensa da ke nufin tabbatar da cigaban Najeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote 
  • Ƙaddamar da Kyautar Jaruman Indomie Karo Na 17 Yayin Da Zakarun Matasa Suka fafata daga karshe an samu zakaru
  • Masu yabon Buhari sun yi masa ba’a bayan ya sauka daga mulki —Gwamna Sule
  • Ana Zaman dar-dar a Kamaru gabanin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa
  • Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu
  • Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya
  • Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu
  • Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025
  • ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa