A Shirye Nake Na Kare Nasarar Da Na Samu A Zabe – Tchiroma Bakary
Published: 24th, October 2025 GMT
Ɗan takarar jam’iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, ya shaida wa BBC cewa a shirye yake ya kare abin da ya bayyana “nasara ƙarara” da ya samu.
Yayin da al’ummar ƙasar ke ci gaba da dakon sakamakon zaɓen da za a bayyana a ranar Litinin mai zuwa, Bakary, wanda shi ma tsohon jami’in gwamnatin Paul Biya ne, ya ce zai amince ne kawai da sakamako na gaskiya.
Wannan kalami nasa dai zai ƙara rura wutar zaman ɗarɗar da ake yi a ƙasar ta yankin tsakiyar Afirka.
Tun daga farkon makon nan ne mutane, musamman magoya bayan Bakary suka riƙa fita kan tituna domin yin gangamin kira ga gwamnati ta tabbatar ta fitar da sakamako daidai da zaɓin al’umma.
A baya an tsara cewa za a bayyana sakamakon zaɓen ne ranar Alhamis, sai dai wata sanarwa daga gwamnati ta ce an ɗage bayyana sakamakon zuwa ranar Litinin ɗin mako mai zuwa.
Wasu alkalumman da kafofin yada labaran kasar suka ruwaito sun nuna cewa akwai yiyuwar shugaba Paul Biya ne zai zarce kan mulkinsa na shekara 43.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kamaru
এছাড়াও পড়ুন:
Wani Masani Dan Iran Ya Samu Lambar Yabo Ta WHO Don Kirkiro Abin Da Zai Kare Cututtuka Da Basa Yaduwa
Dr Majid Ghayour Mubarhan kwararre kuma farfesa a jami’ar kiwon lafiya ta birnin mashahada ya samu kyautar hukumar WHO na gabashin meditareniya saboda namijin kokarin da yayi na kirkiro abin da zai kula da kuma kare kamuwa da cututtuka da basa yaduwa, kamar cutar kansa ciwon zuciya da kuma ciwon Sugar.
Wannan kyautar tana nuna irin ci gaban da Iran ta samu ne a bangaren kimiyyaa yankin duk da takunkumi da kuma takurawar da take fuskanta daga bangaren kasashen turai dake takaita halartar masana kimiyyar kasar hallara a matakin kasa da kasa.
A duk shekata hukumar lafiya ta duniya tana bada kyauta ga duk wani masanin kimiya da yayi kwazo wajen kirkiro wata fasaha a bangaren lafiyar gama gari, da kare kamuwa daga cututtuka, kyautar wannan shekarar wata cibiyar bada kyaututtuka ne dake kasar Kuwaiti ta samar, kuma aka bawa Dr Ghayour mobarhan saboda gudunmawar da ya bayar wajen kare kamuwa da cutar zuciya,
Sai dai saboda rashin samun visa a akan lokaci bai samu halartar wajen taron ba, amma Dr Riza’i mataimakin ministan lafiya na Iran ya karbi kyautar a Madadinsa,
Dr Ghayour shi ne wanda ya kafa cibiyar kula da kiwon lafiya ta duniya ta Unesco a iran babbar cibiyar hadin guiwa ta bincike a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar Najeriya Ta Amince Da Dokar Daurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Kananan Yara Fyade October 22, 2025 Birtaniya Ta Cire Kungiyar Tahrirush -Sham Daga Jerin Yan Ta’adda October 22, 2025 China Ta Kammala Gina Cibiyar Adana Bayanai Masu Amfani Da Karfin Iska October 22, 2025 Iran Ta Godewa Rasha Game Da Goyon Bayan Da Ta Bata A Kwamitin Sulhu Na M D D October 22, 2025 Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta October 22, 2025 Sheikh Qasim: Natanyahu Ya Zubar Da Jini Mai Yawa Amma Babu Lamuni Ga Amincin Isra’ila Nan Gaba October 22, 2025 Aragchi Da Guterres Sun Tattauna Kan Gaza Da Rikicin Yemen Ta Wayar Tarho October 22, 2025 Rasha da Habasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin nukiliya October 22, 2025 Sayyed al-Houthi: Mun shirya dawowa fagen daga idan Isra’ila ta ci gaba da kisan kiyashi a Gaza October 22, 2025 Nigeria: “Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Neman Sakin Jagoran ‘Yan Awaren Biafara October 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci