AGILE Kano Ta Tattauna da Malamai da Limamai Don Ƙarfafa Goyon Bayan Ilimin ’Yan Mata
Published: 24th, October 2025 GMT
Shirin karfafa ilimin ‘ya’ya mata a jihar Kano ya shirya taron tattaunawa da malamai da limaman masallatan Juma’a domin ƙarfafa haɗin gwiwa da shugabannin addini wajen inganta goyon bayan al’umma ga ilimin ’yan mata a fadin jihar.
Taron, wanda yake ɗaya daga cikin dabarun haɗin kai na masu ruwa da tsaki na AGILE, yana da nufin ƙara samun damar karatu, tsayawa da kuma kammala karatun ’yan mata ta hanyar daidaita ayyukan shirin da dabi’u da imanin al’umma.
A jawabinsa, Shugaban Shirin AGILE na Jihar Kano, Malam Mujtapha Aminu, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin fayyace wasu rashin fahimta da ake da su game da shirin, da kuma tabbatar da fahimtar juna tsakanin shugabannin addini.
A cewarsa, “Shigar malamai da limaman masallatan Juma’a cikin wannan shiri yana da matuƙar muhimmanci domin suna da tasiri wajen gina ra’ayin jama’a. Mun gayyace su ne domin mu wayar da kan su game da manufofi, sassa, da matakan aikin shirin AGILE.”
Malam Mujtapha ya ƙara bayyana cewa shirin ya riga ya haɗa kai da shugabannin gargajiya da na addini wajen duba kundin horarwa don tabbatar da cewa yana tafiya da koyarwar addinin Musulunci da kuma dabi’un Hausawa.
Ya roƙi dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da ba da goyon baya ga shirin tare da neman bayani a duk lokacin da wani abu ya taso, domin kauce wa rashin fahimta. Ya jaddada cewa, “Malamai sune manyan masu tasiri wajen bunƙasa ilimin ’yan mata a Kano da Najeriya gaba ɗaya.”
A sakon sa na fatan alheri, Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, wanda Sakatarensa Sheikh Ibrahim Abubakar Tofa ya wakilta, ya shawarci tawagar AGILE da su tabbatar dukkan sassan shirin suna tafiya da ka’idojin Musulunci da al’adun mutanen Kano, domin jihar na da tsarin rayuwa mai zurfi da al’adu masu ƙarfi.
Ya ce, “A matsayarmu na manyan masu ruwa da tsaki, muna da muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ilimin ’yan mata domin Musulunci yana ƙarfafa neman ilimi ga maza da mata duka.”
Haka kuma, ya yi kira ga masu gudanar da shirin da su ci gaba da haɗa kai da dukkan masu ruwa da tsaki don gujewa yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma tabbatar da gaskiya a duk matakan aiwatarwa.
Taron ya ƙunshi gabatar da cikakkun bayanai kan manyan sassan uku na shirin AGILE, tattaunawa tsakanin mahalarta, da zaman tambayoyi da amsoshi inda malamai suka gabatar da tambayoyi kan wasu bangarorin shirin kuma aka basu bayanai dalla-dalla.
Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: masu ruwa da tsaki
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano
Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa.
Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, kuma suka tafi da shi hedikwatarsu da ke Bompai.
Kwamashinan ya siffanta kamen da “abin damuwa sosai” wanda “ya yi kama da yanayin aikin soja”. Ya yi iƙirarin cewa dakaru kusan 40 ne ɗauke da makamai suka je kama Muhuyi.
“Kwamashinan ya nuna cewa akwai yiwuwar lamarin yana da alaƙa da binciken da ake yi wa wasu manyan ‘yansiyasa,” in ji sanarwar.
Abdulkarim Maude ya kuma yi kira ga rundunar ‘yansandan Najeriya ta yi cikakken bayani game da dalilin kama Muhuyi.