Aminiya:
2025-12-09@18:56:20 GMT

‘Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja

Published: 24th, October 2025 GMT

Rundunar ’yan sanda ta kama wani matashi ɗan shekara 29, mai suna Abubakar Isah Mokwa ɗalibi da yake karatun digiri na biyu a tsangayar Tattalin Arziki na Noma a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai, Jihar Neja.

An kama ɗalibin ne bisa zarginsa da sukar Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago.

Rahotanni sun ce an an kama Abubakar Mokwa ne a wajen harabar jami’ar da yake da masauki a Lapai a ranar Alhamis bayan wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya caccaki gwamnan kan rashin aikin yi.

’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar wa Aminiya kamun da aka yi wa ɗalibin.

Ya ce, an kama wanda ake zargin ne biyo bayan ƙorafin da ya yi kan cin zarafi ta intanet, satar bayanai ta intanet da sauran laifukan da suka shafi intanet.

“Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta samu ƙorafin aikata laifukan da suka haɗa da cin zarafi ta intanet, satar bayanai ta intanet da sauran laifukan da suka shafi intanet akan wani Abubakar Isah Mokwa mai shekara 29 a garin Mokwa kuma ɗalibin IBBUL da yake karatun digiri na biyu.

“Saboda haka, hukumar jami’an Lapai ta gayyace shi ta kama shi a ranar 23 ga Oktoba, 2025 da misalin ƙarfe 11 na dare, sannan aka tura shi hedikwatar ‘yan sanda ta jihar a Minna babban birnin jihar, domin ci gaba da bincike kan ƙarar da ake tuhumarsa da aikatawa. Sai dai wanda ake zargin yana tsare kuma za a ci gaba da yi wa jama’a ƙarin bayanui,” in ji Abiodun.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jami ar Ibrahim Badamasi Babangida Jihar Neja

এছাড়াও পড়ুন:

Pakistan ta Bai Wa Taliban Ta Aghanistan  Zabi A Tsakanin Mu’amala Da Ita Ko  Da  ‘Yan Ta’adda

Kwamandan sojan kasar Pakitsan Asim Munir ya ce; Dole ne Taliban ta zabi wanda za ta yi mu’amala da hulda da su, ko dai gwamnatin Pakistan din, ko kuma ‘yan ta’adda.

Asim Munir wanda a makon da ya shude aka sake tabbatar da shi akan mukaminsa na shugaban sojojin kasar, ya kara da cewa sun isar da wannan sakon zuwa ga gwamnatin Taliban ta Afghanistan.

Haka nan kuma ya ce; Pakistan kasa ce mai son zaman lafiya,amma kuma a lokaci daya ba a shirye take ba, ta bari a tsokane ta akan abinda ta shafi zaman lafiya da kare hurumin kasarta.

A gefe daya, Asim Munir ya kuma gargadi makwabtansu na gabas, wato India yana mai cewa s fito daga cikin rudani, domin anan gaba idan wani abu ya faru, to martanin da Pakistan za ta mayar zai zama cikin sauri kuma da tsanani fiye da baya.

Ministan tsaron na Pakistan ya kuma ce, sojojin kasar sun sami gagarumin ci gaba wajen bunkasa ayyukansu, da kara zama cikin shiri, da kuma hanyoyin aiki tare a tsakanin dukkanin bangarorin tsaro.

A cikin watannin bayan nan dai an sami rashin jituwa a tsakanin kasashen Pakitsan da Afghanistan wanda ya kai ga musayar wuta na kwanani masu yawa. Kasashen Turkiya da Katar ne su ka shiga tsakani da ya kai ga tsagaita wutar yaki.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Kasashen Iran Da Turkiya Za Su Bunkasa Alakarsu A Fagen Ilimi Da Musayar Fasaha December 9, 2025 An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa” December 9, 2025  Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba December 9, 2025 AU Ta yi Tir Da Harin RSF  A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80 December 8, 2025 MِِِِDD:  Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne
  • Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC
  • Kamfanin Mangal ya kori direba kan dauko yara 21 da aka kama a Kogi
  • Pakistan ta Bai Wa Taliban Ta Aghanistan  Zabi A Tsakanin Mu’amala Da Ita Ko  Da  ‘Yan Ta’adda
  • ‘Yan Bindiga 18 Sun Muta a Wata Arangama da Rundunar Operation Fansan Yamma
  • An kama tsohon fursuna ya je fashi da bindiga AK-47
  • Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin
  • An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja
  • Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Wani  Hatsari a Neja
  • Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi