Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF
Published: 15th, October 2025 GMT
Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta zuba jari a fannin kayan aikin wanke hannu da kuma ilimin tsafta.
Asusun ya kuma ce kaso 35 cikin 100 na makarantu ne kawai ke da kayan wanke hannu na asali, yayin da kashi 8 cikin 100 na ’yan Najeriya ne kawai ke iya nuna yadda ake wanke hannu daidai.
Yayin wata ziyara da aka kai makarantu a Jihar Borno a ranar Laraba, a wani ɓangare na bikin Ranar Wanke Hannu ta Duniya ta shekarar 2025, Shugabar Ofishin UNICEF a Maiduguri, Dr. Marie Marcos, ta ce zuba jari a kayan wanke hannu zai ƙara adadin masu zuwa makaranta, inganta lafiyar al’umma, da kuma ƙara ƙwarewa a wuraren aiki.
A cewarta, yankin Arewa maso Gabas ne ke matsayi na biyu a Najeriya dangane da gidaje da ke da wuraren wanke hannu da ruwa da sabulu.
Marie ta ce, “Duk da cewa kaso 99 cikin 100 na ’yan Najeriya sun san lokacin da ya dace a wanke hannu, kashi 8 cikin 100 ne kawai ke iya nuna yadda ake wanke hannu daidai.
“Kaso 17 cikin 100 na gidaje ne ke da damar samun tsafta na asali. Kaso 35 cikin 100 na makarantu ne ke da kayan wanke hannu da ruwa da sabulu.”
“Arewa maso Gabas na matsayi na biyu a Najeriya dangane da gidaje da ke da wuraren wanke hannu da ruwa da sabulu, duk da cewa adadin ya yi kadan a matakin ƙasa baki ɗaya, wato kaso 22.1 cikin 100,” in ji ta.
Sai dai ta ce UNICEF, ta hannun Gwamnatin Jihar Borno, ta tallafa wajen kafa tsarin wanke hannu a makarantu 50 a faɗin jihar, wanda ke kare kusan ’yan makaranta 20,000 a halin yanzu.
“A Jihar Borno, kaso 14 cikin 100 na gidaje ne ke da kayan wanke hannu da sabulu da ruwa. Kashi 20 cikin 100 na makarantu ne ke da kayan tsafta na asali,” in ji ta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: wanke hannu a kayan wanke hannu wanke hannu da ke da kayan a makarantu
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya
A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su.
A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar.
Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba, to akwai alamun sake rage yawan kujerun zuwa dubu hamsin.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’ummaKo yaya kara raguwar kujerun maniyyatan Najeriya ke kara tasiri ga Najeriya?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan