An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa
Published: 26th, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayar da tallafin Naira miliyan biyu ga iyalan SC Bashir Adamu Jibrin, jami’in hukumar sibil difens (NSCDC) da ya rasu a bakin aiki a kasuwar Shuwarin da ke ƙaramar hukumar Kiyawa.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ne ya miƙa tallafin ga matar marigayin a ofishinsa, inda ya ce wannan taimako na nufin tallafa wa iyalan marigayin tare da taimaka musu wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu.
Ya shawarci matar marigayin da ta yi amfani da kuɗaɗen wajen kula da ilimi da walwalar ’ya’yanta, tare da jaddada cewa gwamnatin Jigawa za ta ci gaba da girmama sadaukarwar jami’an tsaro da ke bayar da rayukansu don kare al’umma.
Da yake martani, Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, Muhammad Kabir Ingawa, ya gode wa gwamnatin jihar bisa wannan alheri, yana mai roƙon Allah ya jiƙan marigayin.
Ita ma a nata ɓangaren, matar marigayin, Zainab Muhammad Ahmed, ta bayyana godiyarta ga gwamnatin jihar bisa wannan taimako, tare da tabbatar da cewa za ta yi amfani da kuɗaɗen yadda ya dace.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan kare dangi ga Najeriya.
Ko wannan ziyarar da tawagar Amurka ta kawo zai kawo karshen matsalar tsaron da Najeriya ke ciki?
NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan TsaroWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan