Leadership News Hausa:
2025-10-24@10:27:40 GMT

Dauda Lawal: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

Published: 24th, October 2025 GMT

Baya ga haka, sabon ginin ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Zamfara da aka sake ginawa da kuma sabon ginin kwalejin fasaha da kimiyya na Jihar Zamfara (ZACAS) da aka gyara, sun yi matuƙar haskaka Gwamnatin Dauda Lawal.

Har ila yau, jihar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar zuba jari, wajen gyarawa da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin jihar.

 

A ƙoƙarinsa na rage mace-macen mata masu juna biyu da mace-macen jarirai, an ɗauki ma’aikatan kiwon lafiya tare da horar da su da sayen magunguna da kayan aiki da ɓullo da ayyukan kula da lafiyar mata da ƙananan yara kyauta.

Sannan, an gyara asibitin ƙwararru na Yeriman Bakura tare da samar da kayan aiki na zamani. Haka kuma an gyara tare da samar da kayan aiki ga babban asibitin da ke Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda a jihar. Babban asibitin da ke Kauran Namoda da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da shi, an samar da kayan aiki don isar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya yadda ya kamata. Kazalika, an sanya na’urorin bincike, gadaje, injinan ECG, injin centrifuge, injinan gwaje-gwajen jini, na’urar tantance jini ta atomatik da sauran wasu kayan aiki.

Kazalika, an kuma inganta babban asibitin Nasarawar Burkullu da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum. Bayan ayyukan kiwon lafiya da suka haɗa da na gaggawa, aikin tiyata, kula da lafiyar mata da yara, tsarin wurin keɓewa, wurin ajiyar gawa, ɗakunan tiyata na maza da mata, GOPD, ɗakin gwaje-gwaje, shagon magani, kula da mata masu juna biyu da kula da yar, duk an gina su. Sauran gyare-gyaren, sun haɗa da shingen gudanarwa, wuraren ma’aikata, masallatai da rijiyoyin burtsatse.

Haka kuma, a Ƙaramar Hukumar Maru, an gyara babban asibitin tare da samar da kayan aiki na zamani.

Gwamnan ya kuma kaƙƙamar da aikin sabunta birane, wanda ya kai ga gyara manyan tituna a jihar.

Dangane da batun tsaro kuwa, a shekarun baya-bayan nan, Zamfara ta ɗan samu jinkiri. A wannan lokaci na Gwamna Lawal, kashe-kashe da garkuwa da mutane ya ragu matuƙa a jihar. Hakan ya biyo bayan kafa jami’an tsaron da aka kafa a dukkanin kananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.

An horar da mutanen da aka zaɓo a tsanake, bisa cikakkiyar kulawar jami’an tsaron hukumar DSS, sannan suna yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro na yau da kullum, domin yaƙi da ‘yan fashi a jihar. A kwanakin baya ne gwamnan ya raba motocin aiki guda 140 da aka ware wa ƙungiyoyin tsaro daban-daban a faɗin jihar.

An haifi Dauda Lawal Dare, a ranar 2 ga Satumbar 1965, a Jihar Zamfara. Bayan kammala karatunsa na Firamare da Sakandare, ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa. Ya kuma yi digirinsa na biyu (M.Sc) a fannin kimiyyar siyasa/Hukunce-hukuncen ƙasa da ƙasa duk a jami’ar. Ya ƙara da digirin-digirgir (PhD) a fannin harkokin kasuwanci a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.

Bayan kammala karatunsa na digiri na uku, ya yi kwasa-kwasai a Makarantar Kasuwanci ta Harɓard, Makarantar Kasuwanci ta Jami’ar Oɗford, Makarantar Tattalin Arziƙi ta Landan, Makarantar Kasuwancin Legas da sauransu.

Gwamnan ya yi aiki a matsayin jami’in ilimin siyasa tare da MAMSER, hukumar wayar da kan jama’a, don tabbatar da adalci da dogaro da kai a Nijeriya. A 1989, ya shiga Westeɗ Nigeria Limited a matsayin mataimakin babban manaja.

An naɗa shi a matsayin mataimakin ƙaramin jami’in shige da fice (immigration), a shekarar 1994, sannan ya zama babban jami’in hulɗa da jama’a a ofishin Jakadancin Nijeriya, Washington, DC, Amurka.

A shekarar 2003, ya koma bankin First Bank, a matsayin manajan hulɗa da jama’a, kuma a lokuta daban-daban ya kasance babban manaja a ofishin Abuja. A shekarar 2011, ya samu muƙamin mataimakin shugaban zartaswa, sashen gwamnati na Arewa na bankin na First Bank, bayan ya yi ayyuka da dama. A shekarar 2012, Dauda Lawal ya zama babban darakta a sashen gwamnati na Arewa, na First Bank.

Daga baya ya shiga siyasa ya kuma tsaya takarar Gwamnan Jihar Zamfara. A zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a shekarar 2018, ya sha kaye a hannun Idris Shehu Mukhtar. A zaben Gwamnan Jihar Zamfara na 2023, ya tsaya takara; kuma ya yi nasara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya October 24, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno October 23, 2025 Ra'ayi Riga Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata October 23, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: samar da kayan aiki a Jihar Zamfara kiwon lafiya Dauda Lawal

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Biliyan Daya Wajen Gyaran Ajujuwa A Makarantu

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe fiye da Naira miliyan 528 domin gyaran ginin ajujuwa a wasu zababbun makarantu na gwamnati a fadin jihar.

Ya bayyana cewa, manufar aikin ita ce inganta yanayin karatu, tabbatar da tsaro, da kuma samar da iingantaccen ilimi karkashin shirin gwamnatin jihar na farfado da ilimin asali.

Sagir Musa ya kuma ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 512 domin  samar da kujeru da gadajen ɗalibai, domin ƙarfafa tsarin ilimi tare da tabbatar da walwala da inganci a makarantu.

 

Usman Mohammed Zaria

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Ya Jaddada Kudurin Gwamnatinsa Na Ƙara Zuba Jari A Ilimi
  • Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, Ta Kaddamar da Dakin Karatu Na Zamani a Zamfara
  • AGILE Kano Ta Tattauna da Malamai da Limamai Don Ƙarfafa Goyon Bayan Ilimin ’Yan Mata
  • Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba
  • Babban Lauyan Jihar Kwara Ya Tabbatar da Gudanar da Adalci da Kare Hakkokin Mace
  • UNICEF Ya Tabbatar Da Anniyar Na Karfafa Jagorancin Mata A Fannin Ilimi
  • Rundunar ‘Yan Sanda A Jihar Zamfara Ta Gargadi Direbobi Game Da Rufe Lambar Mota
  • Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal
  • Jihar Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Biliyan Daya Wajen Gyaran Ajujuwa A Makarantu