Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, shugaban kasar Xi Jinping zai halarci taron shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin ta kasashen Asia da Pasifik (APEC), karo na 32 a Gyeongju na Korea ta Kudu, bisa gayyatar shugaban kasar Lee Jae-myung. Taron zai gudana ne daga ranar 30 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba, kana shugaba Xi Jinping zai yi ziyarar aiki a kasar.

(Fa’iza Muhammad Mustapha)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta October 23, 2025 Daga Birnin Sin Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa October 23, 2025 Daga Birnin Sin Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba October 23, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.

Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa yana da “damuwa ta musamman” kan yadda gwamnati ta kasa daƙile ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga, rikice-rikicen ƙabilanci da kuma yaɗuwar makamai ba tare da kulawa ba.

Ya ce abin da ya fi nuna gazawar gwamnati shi ne yadda aka bar jihohi su kafa ƙungiyoyin sa-kai ba tare da horo na musamman ba, abin da ya ƙara yaɗuwar kananan makamai a ƙasar.

“Abin takaici, Gwamnatin Tarayya ta gaza. Hakan ya bayyana a yadda ta amince da jihohi su kafa kungiyoyin sa-kai ba tare da horo na kwararru ba,” in ji shi.

An kama tsohon fursuna da bindiga ƙirar AK-47 Dalilin yawaitar juyin mulki a ƙasashen ECOWAS

Kwankwaso ya gargadi cewa wasu ’yan siyasa suna amfani da wannan dama wajen kafa kungiyoyin su na musamman, abin da ya kara jefa kasar cikin hadari.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ƙara samun wariyar ƙabilanci da yankuna, inda ya ce ’yan Najeriya musamman daga wani yanki ke fuskantar tsangwama ba bisa ƙa’ida ba, tare da cin zarafi da azabtarwa a sassa daban-daban na kasar.

“Hakan ya kara muni da yadda ake samun cin zarafi, tsangwama da maganganun ƙiyayya a kafafen sada zumunta, wanda ake cusawa da kabilanci da addini. Wannan na barazana ga hadin kan ƙasa,” in ji shi.

Kwankwaso ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa don dakatar da wannan hatsari kafin ya ƙara tsananta.

Ya ce a matsayinsa na tsohon Ministan Tsaro da kuma Shugaban Kwamitin Kula da Yaɗuwar Ƙananan Makamai, yana matuƙar damuwa da yadda makamai ke yaɗuwa cikin sauki a kasar.

Sai dai ya taya Janar Christopher Gwabin Musa murnar nada shi Ministan Tsaro, yana mai fatan zai yi nasara idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace.

“Ina da yaƙinin cewa idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace, yana da ƙwarewa da gogewa da za su taimaka wajen dawo da tsaro da zaman lafiya a kasar,” in ji Kwankwaso.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia
  • Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki
  •  Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba
  • Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin Jihohi Shidda
  • Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima Ya Isa Abidjan Wajen Rantsar da Shugaba Ouattara
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
  • Majid Majidi Na Iran Ya Sami Kyauyar Girmamawa Daga Cibiyar Fina-finai Na “Eurasia Dake Kasar Rasha
  • Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa
  • Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
  • Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi