Miliyoyin Mutane Sun Yi Juyayin Imam Husain ( a.s) A Karbala
Published: 6th, July 2025 GMT
A kasar Iraki,miliyoyin mutane sun cika birnin Karbala domin yin juyayin shahadar Ahlul Bayti ( a.s) da iyalansa tsarkaka, a tsakanin hubbaren Imam Hussain da dan’uwansa Abul Fadal Abbas ( a.s).
Masoya Ahlul Bayti ( a s.) da su ka fito daga cikin kasar ta Iraki da kuma wasu kasashe, sun yi cincirindo a cikin birnin na Karbala a tsakanin hubbaren Imam Hussain da Abul Fadal Abbas ( a.
Cibiyar da take kula da wuraren masu tsarki a Karbala ta yi tsari na kula a tafiyar da juyayin a cikin tsaro da kuma gabatar da hidima ga masu Ziyara.
An girke jami’an tsaro masu tsaro yawa a cikin birnin na Karbala da zagayen haramin Imam Hussain ( a.s) , haka nan kuma an girke na’urorin gano abubuwa masu fashewa a wurare mabanbanta da su ka hada da mashiga hudu ta garin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.
Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp