‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe
Published: 23rd, October 2025 GMT
A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya sace mata kayanta.
“Abubuwan da aka sace, sun haɗa da iphone 13 Pro Max, an kimanta kudinta akan ₦800,000, kwamfutar ‘Apple MacBook’ da darajarta ta kai ₦250,000, da agogon ‘Apple’ da darajarsa ta kai ₦35,000, ‘power bank’ na Oraimo wanda darajarsa ta kai ₦30,000, da jakar makaranta akan darajar ₦25,000.
Abdullahi ya ce, nan take jami’an ‘yansanda na shiyyar suka dauki matakin kama wanda ake zargin tare da kwato dukkan kayayyakin da aka sace.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Amurka za ta hana ’yan Najeriyar da ake zargi da yi wa Kiristoci kisan kiyashi biza
Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda ya ce Amurka na ɗaukar mataki mai ƙarfi kan munanan ayyuka da tashin hankali da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da sauran sassan duniya.
NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia“Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka (@StateDept) za ta takaita bizar Amurka ga waɗanda suka san da gaske suna jagoranta, ba da izini, ɗaukar nauyi, goyon baya, ko aiwatar da take hakkin ’yancin yin addini. Wadannan manufofin biza sun shafi Najeriya da sauran gwamnatoci ko mutane da ke zaluntar jama’a saboda addininsu,” in ji Rubio.
Maganganun Rubio sun zo ne kwana guda bayan ’yan majalisar Amurka sun gudanar da taron jin ra’ayi a Washington tare da masana kan ’yancin yin addini da dangantakar ƙasashen waje domin tattauna ƙaruwa da tashin hankali a Najeriya da kuma “zaluncin da aka fi karkata ga Kiristoci.”
Taron majalisar ya kasance wani ɓangare na bincike da ake ci gaba da yi kan batun, bisa umarnin Shugaban Ƙasa Donald Trump.