An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC
Published: 25th, October 2025 GMT
Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin halartar taron shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pacific (APEC) karo na 32 a Koriya ta Kudu da kuma ziyarar aiki a kasar Koriya ta Kudu, an kaddamar da nuna muhimman shirye-shiryen talabijin da fina-finai na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a membobin APEC.
Babban darektan CMG Shen Haixiong, ya fada a cikin wani sakon bidiyo cewa, ana fatan wadannan shirye-shiryen talabijin da fina-finai za su iya taimaka wa masu kallo da sauraro a yankin Asiya da tekun Pacific wajen fahimtar hikimar shugaba Xi a fannin shugabanci, da ci gaban kasar Sin a sabon zamani, da al’adun kasar Sin, da kuma bunkasa ci gaban zaman lafiya, da hadin gwiwa mai amfanarwa ga dukkan bangarori, da kuma samun wadata a tsakanin kasashen Asiya da tekun Pacific. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: Asiya da tekun Pacific
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya jagoranci wani taron karawa juna sani a ranar 27 ga watan Augusta, domin jin ra’ayoyin wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba, dangane da shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar game da tsara shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 15, da ke da nufin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. (Fa’iza Muhammad Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA