2025-10-18@14:01:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3868

«firamare da ke»:

    Dan wasan gaba na Barcelona Robert Lewandowski ba zai buga wasan hamayya tsakanin FC Barcelona da Real Madrid wanda ake yi wa take da El Classico ba bayan da zakarun na Sifaniya suka gano cewa yana fama da rauni a kafarsa ta hagu, dan wasan mai shekaru 37 ya samu rauni ne a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Poland ta buga da kasar Lithuania ranar Lahadi. Lewandowski yana da tsagewar tsoka a cikin femoris na cinyarsa ta hagu,” in ji Barcelona a cikin wata sanarwa, yayin da kafofin yana labarai na Sifaniya suka ruwaito cewa zai iya yin jinyar makonni hudu zuwa shida, Barcelona za ta kara da Real Madrid wadda ke jagorantar gasar La Liga...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi iƙirari cewa ministoci da manyan hafsoshin sojin ƙasar sun taya shi murnar bayan bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala. Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa ministoci da manyan jami’an tsaron da ministocin sun kira shi a waya suna jaddada goyon bayansu da niyyar biyayya ga kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma abin da al’umma suka zaɓa. Ya bayyana haka ne wani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, yana mai nuna godiya ga waɗanda suka goyi bayansa, tare da jaddada cewa wannan lokaci yana da muhimmanci matuka ga kasa. Ya ce, “Ina godiya daga zuciyata ga ministoci...
    Hukumomi a Gaza sun zargi sojojin Isra’ila da satar sassan jikin gawarwakin Falasdinawa tare da kira a binciki wannan “mummunan laifi.” Darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza Ismail Thawabta, ya fada a ranar Jumma’a cewa sojojin “mamaya na Isra’ila sun mika musu gawarwaki 120 ta hannun kungiyar agaji ta Red Cross a cikin kwanaki ukun da suka gabata, amma mafi yawan sun zo cikin mummunan yanayi, suna nuna alamun kisa da kuma azabtarwa. Thawabta ya ce akwai alamun shakewa da alamar igiya a wuyansu, lamarin da ke nuni da kisa da gangan.” “Sassan gawarwakin mutane da yawa sun bace, ciki har da idanu, da sauran gabobin,” in ji Thawabta, wanda ya ce ya tabbatar da cewa sojojin Isra’ila “sun...
    A wani bayani da kungiyar Hamas din ta fitar tayi tir da Israila kan yanayin da gawarwarakin da ta bata na palasdinawa dake hannunta, inda aka ga alamomi na Azabtarwar ajikinsu da kuma cire wasu sassan jikinsu don haka ta yi kara da a kafa kwamitin bincike na kasa da kasa kan halin rashin dan adamta da isra’ilan  ta nuna kan gawarwakin. Ta ce yin amfani da hanyoyi daban daban wajen Azabtarwa yana haifar da damuwa sosai kuma ya taka dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Janeva, kuma wadannan ayyukan daidai suke da kisan kiyashi kan alummar falasdinu,  Wasu kungiyoyin sun mika batun ga kwamitin kula da hakokin dan adam na majalisar dinkin duniya domin yin matsin lamba kan...
    A Madagaska jiya Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar ta rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa. Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha. Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar. A ranar Talata da ta gabata ne, Randrianirina ya sanar da juyin mulkin kwace Mulki a kasar yana mai danganta hakan da rashin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, da keta hakkokin bil’adama.  A kuma...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’il baqae yayi tir da harin da HKI ta kai a kudancin labanon kuma ta bayyana hakan a matsayin keta hurumin kasar , yace kasashen Amurka da faransa a matsayinsu na garanto wajen dakatar da bude wuta suke da alhakin taka mata burki kan hare-haren da take kaiwa. Wannan harin da Isra’iala ta kai a kudancin labanon rahotanni sun nuna cewa shi ne kusan karo na 5000 da ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma  tsakaninsu. Kuma wanann ba shi ne karon farko da Isra’ila ke keta yarjejeniyar da aka cimma ba, saboda  akwai dalilai masu yawa da suka tabbatar da haka saboda ta saba yi a yankin gaza da ma labanon din...
    Aƙalla makarantun gwamnati 188 ne aka rufe sakamakon mtsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya. Binciken da wakilanmu suka gudanar ya nuna cewa, an rufe makarantu da dama a yankin saboda hare-haren da ’yan bindiga suke kai wa ƙauyukan da kuma yadda wasu makarantun ke zama a matsugunin mutanen da rashin tsaro ya raba da muhallansu. Wakilanmu sun gano aƙalla an rufe makarantu 55 a Jihar Binuwai, 52 a Jihar Katsina, 39 a Jihar Zamfara, 30 a Jihar Neja, 6 a Jihar Sakkwato da kuma 6 a Kaduna, baya ga makaratu 52 da 55 da aka rufe a jihohin Katsina da Benuwai. Wannan adadi na iya zama sama da haka, saboda ba za a iya isa ga wasu wuraren ba....
    Hukumomi a Gaza sun zargi sojojin Isra’ila da satar sassan jikin gawarwakin Falasdinawa tare da kira a binciki wannan “mummunan laifi.” Darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza Ismail Thawabta, ya fada a ranar Jumma’a cewa sojojin “mamaya na Isra’ila sun mika musu gawarwaki 120 ta hannun kungiyar agaji ta Red Cross a cikin kwanaki ukun da suka gabata, amma mafi yawan sun zo cikin mummunan yanayi, suna nuna alamun kisa da kuma azabtarwa. Thawabta ya ce akwai alamun shakewa da alamar igiya a wuyansu, lamarin da ke nuni da kisa da gangan.” “Sassan gawarwakin mutane da yawa sun bace, ciki har da idanu, da sauran gabobin,” in ji Thawabta, wanda ya ce ya tabbatar da cewa sojojin Isra’ila “sun...
    A Madagaska jiya Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar ta rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa. Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha. Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar. A ranar Talata da ta gabata ne, Randrianirina ya sanar da juyin mulkin kwace Mulki a kasar yana mai danganta hakan da rashin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, da keta hakkokin bil’adama.  A kuma...
    A yayin da Najeriya ke karkata zuwa amfani da kayan tsaro na zamani na cikin gida domin ƙarfafa gwiwar jami’an tsaronta a fagen fama, wani ɗan Jihar Katsina ya fara ƙera motar yaƙi nau’in Track Armored Personnel Carrier (TAPC). Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga, inda suka kashe dubban mutane tare da raba wasu da muhallansu gami da rusa harkokin tattalin arziki da na zamantakewa. Ana cikin haka ne wani ɗan asalin yankin Kaita a jihar mai suna Injiniya Ibrahim Lawal Ɗankaba, ya fara yunƙurin ƙera motar yaƙi, wadda ya sanya wa suna Beguwa, a ƙoƙarinsa na tallafa wa yunƙurin gwamnati na daƙile ayyukan ’yan ta’addanci da suka daɗe suna...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman Sayyid Abdul-Malik Badreddin al-Houthi ya yi jawabi a yammacin yau alhamis kan batutuwa daban-daban da suka shafi duniyar musulmi, musamman abubuwan da suka faru a Gaza da Yemen. Ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ba tare da la’akari da duk wani matsin lamba ba, ta yi sadaukarwa ta karshe a kan turbar goyon bayan Falasdinu, kuma ta bayar da dama ga kwamandojin gwagwarmayar ‘yanci, daga cikinsu akwai babban kwamandan shahidi Qassem Soleimani. Yayin da yake magana kan zagayowar shahadar babban kwamanda Yahya al-Sinwar, Sayyid Abdul-Malik Badreddin ya ce: “Babban darussan da ya bari na tsararraki, da kuma matsayinsa na sadaukar da kai da jihadi, suna wakiltar muhimman dabi’u da kuma babban...
    An gudanar da bikin bayar da lambar yabo ta wasan kwallon kafa na Asiya da Futsal na shekarar 2025 a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. A bangaren mata kuwa, Marzieh Jafari, shugabar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Iran, ita ce babbar mai horar da mata, yayin da Salar Aghapour ta lashe kyautar ‘yar wasa mafi nuna kwazo a wasan Futsal a wannan  shekara. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe. Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta koma karkashen yarjeniyar NPT, kuma za’a yi mu’amala da shirin kamar sauran kasashen karkashin kula na hukumar IAEA. Tsahar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na bada wannan sanarwan a safiyar Asabar ta kara da cewa dama kudurin na tsawon shekaru goma ne daga yau ta gama aiki. Daga yau shirin Nukliyar JMI zai ci gab aba tare da wani karin ka’idojin...
    Kauyukan kasar Iran guda uku,  Soheili a kan tsibirin  Qeshm, da Kandelous a lardin Mazandaran, da kuma  Shafiabad a lardin Kerman na kasar Iran sun shiga cikin zababbun  kauyuka a duniya na yawon shekatawa saboda kyauwunsu da kuma samar da dukkan abin kyautata rayuwa a cikinsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto mataimakin ministan al-adu na kasar Iran yana bada wannan sanarwan a jiya Jumma’a. Anoushirvan Mohseni-Bandpei, ya kara da cewa zabar wadan nan kauyuka na kasar Iran cikin kyauyuka wadanda suka cancanci shiga wuraren yawon shakatawa a duniya wanda hukumar  ‘ The United Nations World Tourism Organization (UNWTO), ta yi zai bunkasa yawon shakatawa a kasar Iran , kuma ma’aikatarsa tana aiki dare da rana don...
    Mataimakin shugaban kasa na farko a nan kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa JMI, kofarta a bude ga tattaunawa da dukkan kasashen duniya in banda HKI. Ya ce mun tattauna hatta da Amurka amma sai suka farmana da yaki a tsakiyar tattaunawar. Don haka Iran tana tattaunawa da dukkan kasashen duniya, sai dai ba zata amince da bukatun da ba zai yu amince da su ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar  Iran ya nakalto mataimakin shugaban kasar yana fadar haka a jiya Jumma’a a lokacinda yake ganawa da masu masana’antu a kasar a nan Tehran, ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta bukaci tattaunawa da Iran amma tare da sharadin ta amince da bukatarta kafin a fara...
    Tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, Janar Alvin Holsey, kwamandan rundunar sojin Amurka ta Kudu, ya yanke shawarar yin murabus nan da watan Disamba, saboda takun-saka tsakaninsa da sakataren tsaron Pete Hegseth, kan rashin jituwar da aka samu game da batun ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean. Rahoton ya bayyana cewa, a makwannin da suka gabata ne Janar Holsey ya bayyana damuwarsa kan sahihancin wadannan ayyuka, yayin da Hegseth ya nuna takaicinsa kan yadda ayyukan ke tafiyar hawainiya, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin bangarorin biyu. A cewar rahoton, manyan jami’an biyu sun tayar da jijiyoyin wuya ne a  yayin wani taro a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon a makon da ya gabata, inda suka yi musayar...
    Tawagar sun gabatar da kansu ga babban sakataren hukumar gudanarwar ci gaban Jihar Katsina, Dakta Mustapha Shehu. Tawagar sun ce ziyarar wani bangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikace-aikace domin inganta zaman lafiya da kuma sanar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira.   Gwamnan Katsina ya yaba wa Bankin Duniya da ya yi hadin gwiwa da Jihar Katsina don fuskantar matsalolin tsaro da kuma tallafa wa ‘yan gudun hijira. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja October 17, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya October 17, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu...
    Shugaban ya kara da cewa, aana sa ran aikin za a fara gudanar da shi ne, a zangon farko na shekarar 2026.   Ya ci gaba da cewa, aikin na yiwa wadannan Tashoshin garanbawul, na daga cikin kudurorin Gwamnatin Tarayya na zamantar da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa, musamman ta hanyar samar da kayan aiki na zamia da kuma ci gaba da janyo hankalin masu son zuba hannun jari zuwa ga fannin, wanda hakan zai kuma kara sanya gasa a cikin wadanda suke a cikin fannin.   Ya bayyana cewa, masu son zuba hannun jari a fannin suna ci gaba da nuna shawarsau, musamman saboda sauye-sauyen da Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinbu ta kirkiro da su, a fannin kara...
    An rantsar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaban gwamnatin sojin Madagascar, bayan ya jagoranci hamɓarar da shugaba Andry Rajoelina. Sabon shugaban Madagascar kuma ya jaddada cewa hawan sa, ba juyin mulki ba ne, domin ya samu goyon bayan kotun tsarin mulkin ƙasar. Gwamnonin APC sun yi taro a Jihar Kebbi ’Yan sanda sun ƙwato miyagun ƙwayoyi a Gombe Bayan ya sha rantsuwar kama aiki Kanal Randrianirina ya ce abubuwan da zai fi bai wa fifiko sun haɗa da ruwan sha da abinci da kuma kafa gwamnati. Tsohon shugaban Ƙasar Rajoelina wanda ’yan majalisar ƙasar suka tsige bayan tserewarsa waje a ƙarshen makon jiya, ya yi Allah wadai da juyin mulki kuma yaƙi amincewa da murabus duk da baya cikin...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tarwatsa wasu muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya a lokacin yakin 12 Kwamandan Dakarun sa-kai na Basij Birgediya Janar Gholamridha Sulaimani ya bayyana cewa: Tunanin kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yakin kwanaki 12 da aka yi, wauta ce ta makiya yahudawan sahayoniyya, wadanda suka gaza a yunkurin da suka yi. Ya jaddada cewa: Iran ta lalata muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya da makamanta masu linzami a yakin karshe. Birgediya Janar Gholamreza Soleimani ya bayyana a wurin taron tunawa da shahidai a Isfahan cewa: Makiya sun yi tunanin cewa za su iya kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran nan da kwanaki 10, kuma sun yi niyyar haifar da hargitsi da...
    Abokan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa: Sake dawo da takunkumi bayan karewarsa baya da wani tushe na doka ko tsari Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa game da cikar kudiri mai lamba 2231 kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran a ranar 18 ga watan Oktoba, inda ta bayyana cewa matakin da Amurka da Turai suka dauka na sake daukar matakin kakaba takunkumin da ya kare kan wata kasa tsari ne da baya ya kan wani tushe na doka ko yarjejeniyar kasa da kasa. Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis da ke nuna cikar kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya...
    Kasar Iran ta yi Allah wadai da harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankin kudancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai a wurare da dama a kudancin kasar Lebanon. Ya jaddada cewa, sun biyo bayan yadda aka ci gaba da yin sassauci da rashin daukar nauyin masu daukar nauyin yarjejeniyar tsagaita bude wuta – Faransa da Amurka – yana mai nuni da alhakin kai tsaye da ke kan kasashen biyu a wannan fanni. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya dauki hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai a jiya da rana da kuma dare kan wasu wurare a kudancin...
    Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su matsa wa haramtacciyar kasar Isra’ila lamba kan aiwatar da sharuddan yarjejeniyar Gaza Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su ci gaba da taka rawa wajen bin diddigin aiwatar da sauran tanade-tanaden yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, musamman ma wadanda suka shafi shigar da adadin taimakon da ake bukata. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta jaddada bukatar gaggauta fara kafa kwamitin tallafawa al’umma domin fara gudanar da ayyukansa na gudanar da harkokin yankin zirin Gaza. Kungiyar Hamas ta bayyana jin dadin ta ga kokarin da masu shiga tsakani a Masar, Qatar, da Turkiyya suka yi na cimma yarjejeniyar dakatar da yakin wuce...
    Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da wasu manyan kwangiloli da kudinsu ya haura Naira Biliyan 6, domin karfafa bangarorin noma, ilimi da ci gaban tattalin arziki a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar da aka gudanar a fadar gwamnatin Dutse, kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna kudirin gwamnatin jihar wajen inganta muhimman bangarori da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma. A cewarsa, majalisar ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2 domin sayen babura nau’in Hunter guda 1,180 ga malaman gona a fadin jihar. Ya ce wannan mataki ya yi daidai da kokarin Gwamna...
    A taron majalsar zartarwar, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa zabinsa na Amupitan ya yi ta’allaka ne a kan rashin nuna son kai na siyasa, gaskiya da kyakkyawan tarihinsa.   Mambobin majalisar, ciki har da shugabanni na yanzu da na baya, sun amince da nadin, suna bayyana Farfesa Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya. Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya ce tarihin Amupitan na ciki da kwazo da adalci da kwarewa da hidimar kasa.   Bayan amincewar majalisar, ana sa ran shugaba zai mika sunan Amupitan zuwa majalisar dattawa don tantancewa da tabbatarwa bisa ga tsarin kundin mulkin Nijeriya.   Farfesa Amupitan, mai shekaru 58, dan asalin kauyen Ayetoro Gbede a cikin karamar hukumar Ijumu ta Jihar Kogi. Ya...
    Dantsoho ya sanar da haka ne, bayan kaddamar dashi a matsayin Mataimakin Shugaban Kungiyar a kwanan baya a wani taro kan harkokin Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya da aka gudanar.   Kazalika, Dantsoho ya ci gaba da cewa, zai mayar da hankali ne, kan wanzar da tsarin da NPA, ta sanya a gaba da kara karfafa hadaka, musaman domin a habaka samar da sauki a fannin gudanar da hada-hadar Tashohin Jiragen Ruwa da ke a Afrika ta Yamma.   Idan za a iya tunawa, harkar gudanar da Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika ta Yamma na fuskantar kalubale da suka hada da, yin aiki da kayan da suka dade da rashin samar da dawamammen tsari da kuma rashin rungumar yin aiki...
    Rahotanni sun bayyana cewa shakih Naim Qassim babban sakatare janar din hizbullah na kasar labanon ya bayyana a jiya Alhamis a gaban mambobin kungiyar Kashafat Al-Mahadi cewa Amerika da Isra’ila ba za su iya yin galaba akan hizbullah ba, Babban hadafin kafa wannan kungiyar shi ne kokarin wayar da kan yara matasa yan shekara 6 zuwa 18 muhimman alamuran addini, adaidai lokacin da gwamntin sahyuniya take ta kokari wajen yada akidar sahyuniyanci tsakanin yara matasa, kungiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen yada akidar gwagwarmaya ga matasa masu tasowa inda yanzu haka tana da mambobin fiye da 100,000. Shaikh Naim Qaseem ya bayyana muhimmancin wannan kungiyar kuma ya bayyana cewa samuwar wadannan matasa zai kara taimakawa wajen tunkarar dukkan kalubalen dake...
      Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin.   Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ta dace, da kuma ƙarfafa hulɗa tsakanin shugabannin addini, gargajiya da na siyasa domin dawo da zaman lafiya da daidaito a al’umma.   Da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, wanda Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya wakilta, ya kira malamai da shugabanni su haɗa kai wajen...
    Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin tarihi, wanda Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka yi wa Sir Herbert Macaulay, daya daga cikin masu kishin kasa a Nijeriya.   A takaice dai, kwamitin bai wa shugaban kasa shawara, kan jinkai, karkashin jagorancin babban mai shari’a; kuma ministan shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, ya bayar da shawarar yin afuwa ga fursunoni biyu da 15 da aka yankewa hukunci, wadanda 11 daga cikinsu sun...
    Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin tarihi, wanda Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka yi wa Sir Herbert Macaulay, daya daga cikin masu kishin kasa a Nijeriya.   A takaice dai, kwamitin bai wa shugaban kasa shawara, kan jinkai, karkashin jagorancin babban mai shari’a; kuma ministan shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, ya bayar da shawarar yin afuwa ga fursunoni biyu da 15 da aka yankewa hukunci, wadanda 11 daga cikinsu sun...
    Kasar Saudiyya ta rage yawan guraben kujerun aikin hajjin da take ware wa Najeriya daga 95,000 zuwa 66,910 daga shekarar 2026. Aminiya ta ruwaito cewa a baya Najeriya ta shafe tsawon shekaru uku tana samun guraben na 95,000 a yayin Aikin Hajjin. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi A cewar Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), wannan sauyi ya biyo bayan gazawar Najeriya wajen cika guraben da aka ware mata a hajjin shekarun 2024 da 2025. Wata sanarwa da, Mataimakiyar Darakta a Sashen Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara, ta sanya wa hannu, ta ce hakan na nufin za...
    A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa. A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran. “Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman...
    A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa. A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran. “Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman...
    Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki.   Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa.   Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar noma, inda ta ce, manoma mata da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da wadanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000.   Shemau ta kuma mika godiyarta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin kokarin da take yi na bunkasa noman mata a Jihar Zamfara.   Sauran hukumomin da kungiyoyin da suke tare da NAWIA...
    Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana. Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata Oktobar kowacce shekara domin bikin wannan rana. Shekaru 170 ke nan da fara amfani da maganin kashe radadi, inda wasu likitoci su ka yi gwajin wannan magani a asibitin birnin Massachusetts na kasar Amurka, abin da ya kawo sauyi wajen yi wa marasa Lafia aikin tiyata daga shekara 1846. Malam Aliyu Umar Yusuf na sashen bada maganin kashe radadi na asibitin gwamnatin tarayya FMC...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta samu nasarar gano wasu motoci da aka sace tare da kama wasu da ake zargin ɓarayi ne masu aikata laifuka ciki har da ƙwace bindiga ƙirar gida. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a madadin Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Bello Yahaya, inda ya ce nasarorin sun biyo bayan sintiri da sahihan bayanan leƙen asiri da haɗin gwiwar al’umma. Miyetti Allah ta dakatar da shugabanninta a jihohi 3 An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi A cewar sanarwar, a ranar 13 ga Oktoba, 2025, jami’an sashin Balanga sun gano wata mota ƙirar Toyota Jeep...
    A Madagaska gobe Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar zata rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa. Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha. Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar. Saidai kotun tsarin mulkin kasar ta sanar da cewa, ya kamata a gudanar da zaben sabon shugaban kasa cikin kwanaki 60. Tuni Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da kasar ta Madagascar daga kungiyar bayan juyin...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasika daga daukacin malamai da daliban jami’ar nazarin aikin gona ta kasar Sin, inda ya taya dukkan malamai da dalibai da ma’aikatan jami’ar, da kuma wadanda suka kammala karatu a jami’ar murnar cika shekaru 120 da kafuwar jami’ar. Xi ya yi fatan jami’ar za ta ci gaba da tafiyar da harkokinta yadda ya kamata, da kudurce aniyar inganta aikin gona don amfanin kasa, da kuma zurfafa yin gyare-gyare kan hanyoyin koyarwa da ilmantarwa, da kara kokarin bincike, da kirkire-kirkire a fannin aikin gona, da kuma amfani da sakamakon binciken yadda ya kamata, ta yadda za a kai ga horar da karin kwararrun masana a fannin aikin gona, don ba da sabuwar gudummawa ga...
    Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa a koda yaushe makiya suna neman haifar da rikici tsakanin kasashen musulmi domin raunana su, yana mai nuni da barkewar tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan. Mr. Pezeshkian ya bayyana haka ne a yayin wani taro inda ya fayyace matsayin kasar Iran dangane da takun saka tsakanin kasashen musulmi a gabashin kasar Iran. Shugaban ya kara da cewa rikicin baya-bayan nan tsakanin Afghanistan da Pakistan ya haifar da damuwa sosai a tsakanin dukkanin kasashen yankin ciki har da Iran da ke da iyaka da kasashen biyu. Ya kara da cewa, Iran za ta yi iyakacin kokarinta na ganin an rage zaman dar-dar, da inganta tattaunawa, da karfafa dankon zumunci a tsakanin...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, Hukumar ta ce, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a Masar ranar Litinin, “Dole ne duniya ta ga abinda ya kasance a Gaza.” Kungiyar ta ce a yanzu dole ne a bar duniya ta ga irin barnar da aka yi, wa matsugunai, da kuma haddassa wahalhalun ga bil adama sanadin yakin da Isra’ila ta yi na...
    Ƙungiyar kare muradun Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta ayyana dakatar da wasu jagororinta daga muƙamin shugabanci a jihohi uku da ke yankin Arewacin ƙasar nan. A wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren hulɗa da jama’a na ƙungiyar na ƙasa ,Ambasada Muhammad Tasiu Sulaiman da aka bayyanawa manema labarai a ranar Alhamis. An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi Majalisar Dattawa ta amince da Amupitan Shugaban INEC Ƙungiyar ta ce dakatarwar ya shafi shuganta a Jihar Adamawa Usman Abubakar Yirlabe da na jihar Taraba, Banmi Bello Jane, sai na Jihar Bauchi Muhammad Hussaini Buzaye. Sanarwar ta ƙara da cewa, matakin dakatar da shugabnnin uku ya biyo bayan wasu ƙorafe-ƙorafe ne daga...
    Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za a fara ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki daga hasken ranar a jihar. Hakan a cewar gwamnatin ya biyo bayan samun masu zuba jari a fannin na makamashi, bayan rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanoni biyu da suka shahara a fannin, wato Tricell Solar Solutions da IRS Green Energy.. ’Yan sanda sun kama gungun masu fashi a kan hanyar Katsina zuwa Kano Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose An kulla yarjejeniyar ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA) domin bayar da shawarwari na fasaha da daidaita ayyuka, a yayin taron Sabunta Makamashi na...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma nuna iko na bangare guda. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Araqchi yana cewa yana daga cikin manufofin kafa kungiyar NAMA tabbatar da yencin ko wace kasa a duniya. Don haka akwai bukatar nuna wannan a aikace. Dangane da yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran a cikin watan yunin da ya gabata, Aragchi...
    Ma’aikatar masana’antu da ma’adinai ta kasar Iran ta bayyana cewa na sami karin ci gaba a yawan karfen da kasar ke sayarwa ga kasashen waje a rabin farko na wannan shekara ta 2025 zuwa dalar Amurka billion $4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasar ta bunkasa amfani da karfe ko a cikin gida sannan da wasu dabarbarun don saida su ga kasashen duniya. Labarin ya kara da cewa yawan karshen da ake samarwa a cikin gida ya karo da kasha 34% a cikin watanni 6 da suka gabata na wannan shekara ta 2025, sannan yawan karfen da iran take satarwa zuwa kasashen wajen ya...
    Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa. Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu sukarsu a wancan lokaci. Ya jaddada cewa El-Rufai da jam’iyyar APC ba za su iya tserewa daga alhakin halin da Nijeriya ke ciki na rashin tsaro ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce bai dace a ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, laifin rikicin da jam’iyyar PDP ke fama da shi ba. Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce shugabannin PDP ne suka haddasa matsalolinsu, ba Tinubu ko jam’iyyar APC ba. Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a A cewarsa, jam’iyyar PDP “ta mutu tun tuni,” kuma ba ya cikin waɗanda za su nemi farfaɗo da ita. Ya ƙara da cewa yawancin gwamnonin da suka rage a PDP na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki. “Ba daidai...
    Shugaban Majalisar Dabarun Kula da harkokin waje kuma mamba a Majalisar fayyace manufofin kasar Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta tattauna amma ta kin juya akalarta Shugaban majalisar dabarun kula da harkokin waje kuma mamba a majalisar fayyace manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kamal Kharrazi, ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta gudanar da zaman shawarwari, amma bazata  amince da dora mata wasu manufofi da suka sabawa muradunta ba. A wata hira da ya yi da shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR, Kharrazi ya ce, “Idan har aka yi shawarwari bisa tushe na hankali, kuma aka mutunta martabar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, to a shirye Iran take ta gudanar da shawarwari, kuma a shirye take ta tattauna,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran da takwaransa na Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falasdinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi Ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falastinu na bukatar kawo karshen mamaya da kuma tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu na cin gashin kansu. Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi da ministan harkokin wajen kasar Tunisiya Mohamed Ali Nafti suka yi a ranar Laraba a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan ba ruwan mu ta NAM karo na 19 a birnin Kampala na kasar Uganda. A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan ci...
    Kasar Afirka ta Kudu tana ci gaba da shari’ar da ta shigar kan gwamnatin mamayar Isra’ila duk da tsagaita bude wuta da aka yi a Gaza Ma’aikatar huldar kasa da kasa da hadin gwiwa ta Afirka ta Kudu ta tabbatar da cewa: Tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba zai kawar da laifukan da aka aikata kan fararen hula ba, tana mai jaddada cewa: Karar da aka shigar kan haramtacciyar kasar Isra’ila a gaban kotun kasa da kasa na da nufin hana sake aukuwar keta haddi, ba wai don dakatar da su na wani dan lokaci ba. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ta ce: “Tsarin shari’ar ya nuna irin sadaukarwar da...
    Hukumomi a Isra’ila sun ce gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar taƙaita shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza, sannan za ta ɗan dakata ta buɗe bakin iyakar zirin daga Rafas. Isra’ila ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ta kira jan ƙafa da a cewarta Hamas ke yi wajen mayar da sauran gawarwaki da ke hannunsu. Zuwa yanzu dai gawarwaki huɗu kawai Hamas ta miƙa, sannan akwai rahotannin da ke cewa ƙungiyar za ta miƙa wasu gawarwakin guda huɗu, amma ta ce nemo gawarwakin na da wahalar gaske. Shi ma Donald Trump ya yi ƙorafi, inda ya buƙaci Hamas ta mayar da gawarwakin “kamar yadda aka yi alƙawari,” in ji shi. Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta...
    Ma’aikatar raya matasa ta jihar Kwara tare da hadin gwiwar Masu Ruwa da Tsaki don horar da matasa kan amfani da fasahar AI don ganin sun kasance masu amfani da dogaro da kai, da kuma samun fasaha.   Da yake jawabi a lokacin da tawagar ta ziyarci ma’aikatar a Ilorin, kwamishinan ci gaban matasa na jihar, Ndanusa Shehu, ya bayyana matakin a matsayin wanda ya dace kuma ya kawo sauyi.   A cewarsa Artificial Intelligence wata hanya ce ta tsara makomar aiki a duniya tare da jaddada mahimmancin ganin matasa sun iya amfani da irin wannan kirkirarriyar fasaha.   Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ci gaba da nuna kyakykyawan manufa na karfafa matasa, tun daga samar da damammaki a...
    Hukumar kula da gidaje ta jihar Kano ta fara wani gagarumin aikin tsaftar muhalli kashi na biyu a birnin Kwankwasiyya, inda ta kara azama wajen gina tsaftataccen muhalli, lafiya da kuma dorewar muhalli a birane.   Da yake jawabi yayin aikin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Engr. Isyaku Umar Kwa, ya bayyana cewa kashi na biyu ya mayar da hankali ne kan inganta harkar sharar gida, da inganta tsarin tattara shara, da kuma kawata wuraren jama’a a fadin birnin na Kwankwasiyya.   A cewarsa, aikin na da nufin tabbatar da tsaftar tituna, wuraren shakatawa, da wuraren jama’a tare da inganta alkinta muhalli.   Engr. Kwa ya bayyana cewa an tsara wannan shiri ne domin karfafawa mazauna garuruwan Kwankwasiyya da Bandirawo da...
    Kakakin Majalisar Nasarawa ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa al’ummar Nindama, in ji Govt. ya dauki matakan da suka dace.   Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya jajantawa al’umma da iyalan harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a kauyen Nindama da ke karamar hukumar Kokona a jihar.   Shugaban majalisar yayin ziyarar jajantawa al’ummar yankin ya yi kira da a kwantar da hankulan mazauna yankin inda ya tabbatar musu da cewa Gwamna Abdullahi Sule ya dauki matakan da suka dace domin hana afkuwar lamarin nan gaba.   “Wannan abin bakin ciki ne, abin takaici ne, dabbanci da zafi, amma a bar wa Allah Madaukakin Sarki...
    Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa hukuncin daurin shekaru takwas ba tare da zaɓin tara ba, kan laifin luwadi da ɗan wasan kulob dinsa mai karancin shekaru. Kotun dai wacce ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahuru Muhammad a ranar Laraba ta sami kocin mai suna Hayatu Muhammad da aikata laifin. Tinubu na ƙoƙarin mayar da Najeriya mai jam’iyya ɗaya — ADC Majalisar Dattawa za ta tantance Amupitan a ranar Alhamis Wanda aka yanke wa hukuncin, mazaunin unguwar Sanka ne a ƙaramar hukumar Dala, kuma kotun ta tabbatar da cewa ya aikata laifin har sau biyu a wurare daban-daban. Da farko dai ya musanta zargin da ake masa. Sai dai, bayan tabbatar da laifin...
      A yayin shari’ar, wanda ake tuhumar ya musanta zargin, sai dai kotun ta ce masu gabatar da kara sun gabatar da shaida wadda ta gamsar da ita ba tare da wata shakka ba. Mai shari’a Dahiru ya ce laifin ya ci karo da sashe na 284 na kundin laifuffuka, wanda ya haramta yin jima’i ba bisa ka’ida ba, don haka ya yanke wa Hayatu Muhammad hukuncin daurin shekaru hudu a kan kowanne daga cikin tuhumomin biyu, wanda zai fara ne tun ranar da aka kama shi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar October 15, 2025 Labarai Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar...
    Majalisar Dattawa za ta tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a ranar Alhamis, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Daraktan Yaɗa Labarai na Majalisar Tarayya, Bullah Audu Bi-Allah ne, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe A makon da ya gabata ne, Shugaba Tinubu, ya aike wa Majalisar Dattawa sunan Amupitam, domin ta tabbatar da naɗinsa. An karanta wasiƙar Tinubu yayin zaman majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio. A cikin wasiƙar da ya aike, Tinubu, ya ce: “Dangane...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abass Araqchi ya bayyana yadda wasu kasashen turai 3 suka yi amfani da yarjejeniyar JCPOA da kuma kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wajen mayar da kudurin kwamitin da aka soke shi a baya kan kasar iran, wanda ya fuskanci adawa daga kasashe da dama ciki har da mambobin biyu na dindindin a kwamitin sulhu a matsayin dokar da ta sabama doka kuma ba za ta yi tasiri a shari’a ba. Kasashen turai saboda matsin lambar Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA don haka wadannan kasashe basu da hurumin da za su ce wani abu kan jarjejeniyar,  tun da saboda su ne da Amurka dukkan yarjejeniyar ta wargaje Minista Araqchi ya bayyana cewa batun yankin...
    Ministan kula da ayyukan soji na HKI Katz ya bayyana cewa dakarun sojin Isra’ila za su koma da kai hare-hare a yankin Gaza, bayan ta kammala karbar dukkan mutanen ta da kungiyar Hamas ta kama, don nuna rashin amincewa da sabuwar yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin Hamas da kuma gwamnatin tel Aviv. Isra’ila tana fuskantar babban kalubale wanda bayan dawo da dukkan mutanen ta da aka kama, shi ne batun lalata dukkan ramukan hamas dake yankin Gaza kai tsaye ta hanyar sojoji kuma ta hanyar tsarin kasa da kasa da za’a kafa karkashin umarnin da kulawar Amurka, Wannan yana zuwa ne kwana daya kafin kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin hamas da Isra’ila, da shiga...
    Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun samar da sabbin hanyoyin fuskantar makiya wadanda ta daukosu daga abinda ya faru a yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka duka dorawa kasar.  Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Khatami yana fadar haka a jiya a ganawarsa da kwamitin al-amuran tsaro da harkokin waje na majalisar dokokin kasar Iran a ranar Litinin. Khatami ya fadawa kwamitin yadda al-amura suke dangane da harkokin tsaron kasar da kuma al-amura da suka shafiu siyasa, tsaro da shirin sojojin kasar Iran dangane da abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya. Khatami ya kara da cewa yakin kwanaki 12 wanda HKI da...
    Kotun Babban Majistare da ke Yaba ta bayar da umarnin a tono gawarwakin mutane 10 da gobara ta kashe a ginin Afriland Towers da ke Legas a ranar 16 ga Satumba, 2025, domin a gudanar da bincike a kansu. Alkalin kotun, Mai shari’a Atinuke Adetunji ce ta bayar da umarnin a ranar Talata bayan ta samu labarin cewa an riga da binne wasu daga cikin waɗanda gobarar ta ritsa da su. “Mai ƙorafi ya rubuta wa Gwamnatin Jihar Legas don neman izinin tono gawarwakin waɗanda suka mutu, sannan a gudanar da bincike a kansu,” in ji Mai Shari’a Adetunji. Wannan umarni ya biyo bayan wata wasiƙa daga ofishin babban lauya Femi Falana da aka aike wa Babban Mai Kula da...
    Kotun Babban Majistare da ke Yaba ta bayar da umarnin a tono gawarwakin mutane 10 da gobara ta kashe a ginin Afriland Towers da ke Legas a ranar 16 ga Satumba, 2025, domin a gudanar da bincike a kansu. Alkalin kotun, Mai shari’a Atinuke Adetunji ce ta bayar da umarnin a ranar Talata bayan ta samu labarin cewa an riga da binne wasu daga cikin waɗanda gobarar ta ritsa da su. “Mai ƙorafi ya rubuta wa Gwamnatin Jihar Legas don neman izinin tono gawarwakin waɗanda suka mutu, sannan a gudanar da bincike a kansu,” in ji Mai Shari’a Adetunji. Wannan umarni ya biyo bayan wata wasiƙa daga ofishin babban lauya Femi Falana da aka aike wa Babban Mai Kula da...
    Kasar Iran ta yi Allah wadai da kalaman kin jinin Iran da Trump ya yi a majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah wadai da zarge-zarge marasa tushe da kuma da’awar rashin gaskiya da rashin kunya da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kan Iran, wanda ya yi a ranar Litinin a zauren majalisar dokokin yahudawan sahayoniya a gaban masu aikata laifukan kisan kare dangi. A cewar wani rahoto da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar a jiya Talata, sanarwar ta ce: Amurka a matsayinta na kasar da ta fi kowacce kasa samar da ayyukan ta’addanci a duniya, kuma mai goyon bayan gwamnatin sahayoniyya ‘yan...
    Iran ta kai hari a wani sansanin sojan Isra’ila na sirri da ke karkashin wata hasumiya a Tel Aviv Yankin Gray, wani dandali ne na bincike, ya bayyana samuwar wani maboyar sirri na sojan Isra’ila da ke karkashin wani hasumiya a Tel Aviv, wanda ake kyautata zaton yana cikin wadanda aka kaiwa hari da makami mai linzami na Iran yayin harin da aka kai ranar 13 ga watan Yuni. Bisa binciken da aka gudanar, dandalin ya gano wurin da wani wurin karkashin kasa da aka fi sani da “Site 81”, wani rukunin jami’an leken asiri na hadin gwiwar sojojin Amurka da Isra’ila da ke karkashin rukunin gidaje na Da Vinci a wata unguwa mai yawan jama’a a tsakiyar birnin Tel...
    Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ‎ ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi masa tafi, sunan shi tarayya a aikata laifi. Shugaba Gustavo Petro yana mayar da martani ne akan zancen da shugaban kasar Amurka ya yi a Majalisar “Knesset’ ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce; Isra’ilan ta yi amfani da makaman da ya ba ta da kyau. Shugaba Gustavo ya kara da cewa; wadannan makaman na Amurka sun kashe mutane 70,000 sannan kuma sun jikkata wasu 200,000....
    Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya. Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki. Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Hukumar Hana Fatucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce dai da gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harkallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, wadanda su ba su...
      Daga nan sai kakakin ya ce, “Ba zai yiwu bangaren Amurka ya nemi tattaunawa a bangare guda, alhali a daya hannun yana barazanar kaddamar da sabbin takunkumai kan kasar Sin ba. Wannan ba ita ce hanya mai dacewa ta gudanar da cudanya da Sin ba.” (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani October 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa  October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025
    Sayyidi Aliyu ya shaida hakan ne yayin jawabin bankwana da wayar da kan ɗaliban da suka samu gurbin karatun zuwa ƙasar Algeria na shekarar 2025, da ya gudana a cibiyar Sheikh Dahiru da ke Bauchi a ranar Litinin 13 ga watan Oktoba.   Ya ce an ɗauki tsawon lokaci ana wayar da kan ɗaliban na tsawon shekara guda kan yadda za su kyautata rayuwarsu a can ƙasar da kuma samun ilimin da ake tsammani a garesu ba tare da matsaloli ba tare da koyar musu harsunan Farsanci da Larabci domin sauƙaƙa musu fara rayuwa a ƙasar Algeria.   Ya yaba wa Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad bisa biyan kuɗin jirgi wa dukkani ɗaliban jihar su 50 daga cikin waɗanda za...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025 Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata October 14, 2025
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya caccaki Donald Trump kan manufofinsa a yammacin Asiya, yana mai cewa shugaban Amurka ba zai iya da’awar samar da zaman lafiya a yankin ba yayin da yake aiwatar da manufofin wuce gona da iri da kuma hada kai da “masu aikata laifukan yaki.” A cikin wani sako a shafinsa na X, Abbas Araghchi ya ce ikirarin da Trump ya yi a baya-bayan nan na cewa “ya rage makwanni” Iran ta kera makamin nukiliya kafin harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyarta ” karya ce.” “Wannan kawai KARYA ce tsungurungum dinta, kuma ya kamata a sanar da shi cewa babu tabbacin hakan, kamar yadda jami’an leken asirinsa suka tabbatar masa.” Jami’in diflomasiyyar...
    Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki. Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin da ma’akatan agajin suka shafe kimanin awa hudu ba su motsa ba saboda luguden bamabaman. Kwamandan hukumar soji da ke yankin ta bayyana cewa an kona motoci hudu tare da lalata wata a cikin tawagar kayan agajin, amma ba a samu asarar rayuka ba a harin da aka kai da jirage marasa matuka da manyan bindigogin atilare a garin Bilozerka. Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa birnin Kampala babban birnin kasar Uganda don halattan taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar yan ba ruwammu karo 19 . Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran za’a gudanar da taron ne tare da neman ‘shi’arin “zurfafa hadin kai da kuma rabon fahintar juna a duniya’. Ana saran Jami’an dublomasiyya da jakadu daga kasashe duniya 120 ne zasu halarci taron karo na 19 a birnin Kampala. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ila Baghaei ya bayyana cewa banda tattaunawar wadan nan kasashe a tsakaninsu kan al-amura da dama, a gefen taron kuma kwamitin Falasdinu na kungiyar zai gudanar da taronsa, wanda gwamnatin JMI take cikinsa. A taron dai ana saran ministan...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Ya kuma kara da cewa JMI zata saurari shawarorin kawayenta amma kuma tana cikin shirin ko ta kwana idan makiya sun yi kuskure sun fadawa kasar da yaki. Baghaei ya na nuni ne da zantawar firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a makon da ya gabata, inda kuma ya bukaci shugaba...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donal Trump a cikin majalisar dokokin HKI a jiya Litinin inda ya bayyana cewa HKI ta sami nasara a yakin da ta kaiwa JMI a cikin watan Yunin da ya gabata, sannan daga karshe ya ce akwai bukatar a cimma yarjeniya da JMI kan shirinta na makamashin Nukliya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na cewa jawabin Trump a majalisar Knesset jawabi ne wanda bai da wani kima. Musamman a lokacinda yake gabatar da ita a gababan yan ta’adda makasa. Ma’aikatar ta tunatarwa Trump har yanzun tana jirin randa za’a gabatar da shi a gaban kuliya kan kissahn Janar shahida Qasim Sulaimani, wanda...
    Duban dubatan mutane sun gudanar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da kuma yin tir da kokarin samar da huldar jakadanci da HKI a maida kome kamar ba abinda ya faru. Sun kuma bayyana tsagaita wutan da aka samar da Hamas tana tangal tangal saboda tun farko ba’a gina shi kan yadda zata dore ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zanga suna cewa, wannan sulhun da kasashen yamma suka kulla da Hamas wani makirci ne na kara samun iko kasashen musulmi da ma wasu kasashen wadanda ban a musulmi ba. Sun kuma bayyana cewa, bayan shekaru biyu da kissan kiyashi sun samar da abinda suka kira sulhu ne na wani lokaci, amma zaman lafiya ba zata taba...
    Allah Ya yi wa Shugaban hukumar Zavbe ta Jihar Yobe (SIEC) Dakta Mamman Mohammed rasuwa sakamakon gajeriyar jinya. Marigayi Dokta Mohammed, likita ne kuma ƙwararren ma’aikacin gwamnati. Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jihar Yobe da ke Damaturu a ranar Litinin. Za a yi Sallar Jana’izarsa a yau talata 14 ga Oktoba, 2025, a Fadar Sarkin Fika da ke garin Potiskum. Dakta Mohammed ya shahara wajen sadaukar da kai da sadaukarwa wajen inganta dimokuradiyya da shugabanci na gari a Jihar Yobe, in ji waɗanda suka san shi. Za a yi Sallar Jana’izarsa a yau talata 14 ga Oktoba, 2025, a fadar mai martaba sarkin Fika da ke garin Potiskum.
    Tsohuwar mai bai wa Basshar Asad na Syria shawara, Busaina Sha’aban ta kore gaskiyar labarin da aka rika watsawa na cewa ta yi wata ganawar sirri da jami’an kasashen Iran, Iraki da Lebanon tare da Basshar Asad. Busaina Sha’aban ta kuma ce ba ta yi managa da tsohon shugaban kasar ta Syria Basshar Asad ba akan labarun karya da aka watsa na cewa ya gana da jami’an dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran, ko kuma batun kafa sansanonin kungiyar al’ka’ida. Ta kuma kara da cewa a tsawon rayuwarta ba ta taba ganawa da Shahid janar Kassim Sulaimani ba,ko shugaban rundunar “Hashdussha’abi” na janar Shahid Abu Mahdi al-muhandis. Tsohuwar mai bai wa shugaban kasar ta Syria ta kuma ce;...
    Mai bai wa shugaban kasar Iran  shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta tausayawa a tsakanin matan duniya domin samar da damar gina rayuwa ta jin kai da ‘yan’adamtaka mai dorewa. Malama Zahra Behruz Azar ta gabatar da wannan shawarar ne dai a yayin taron kasa da kasa na mata da aka bude a kasar China. Haka nan ta kuma bayyana cewa; A wannan lokacin muna rayuwa ne a cikin karnin da ci gaba da fasahar kere-kere su ka sauya salon rayuwa, ta yadda kirkirarriyar fasaha ta zama mai matukar tasiri a cikin matakan da ake dauka, kamar kuma yadda Sakandami ( Robot) ya maye gurbin bil’adama a...
    Rahotanni sun bayyana cewa wani ƙazamin faɗa ya barke tsakanin wata ƙabilar Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da ƙungiyar Hamas a yankin zirin Gaza bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila. A ranar Litinin da aka fara musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ne rahotanni suka ɓulla game da faɗan da ya ɓarke tsakanin mayaƙan Hamas da ƙabilar Doghmush a ranar Lahadi. Wani jami’in Hamas ya bayyana cewa an samu asarar rayuka daga kowane ɓangare a yayin musayar wutan daga misalin ƙarfe 9.30 na dare ranar Lahadi. Wani mazaunin yankin Sebra da ke Birnin Gaza, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa “Mayaƙan Hamas kimanin 200 ne suka zo aka fafata da su, har sai da suka...
    Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a ranar Litinin. Piwuna ya ce ASUU ta tsaya tsayin daka tare da sauran ƙungiyoyin Malamai kamar CONUA, da NAMDA, da SSANU, da NASU, wajen goyon bayan yajin aikin da ke gudana. Ya zargi Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da ƙoƙarin rarraba malamai ta hanyar yin alƙawarin biyan wasu ma’aikata albashi. “Ya na ƙoƙarin rarraba kan mu, amma kan mu a haɗe yake. Babu wanda...
    Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara himma wajen aikin al’umma (CSR), tana taimakawa hukumomi masu ruwa da tsaki da al’ummomi domin karfafa zaman lafiya da tattalin arziki. A cewar Issa-Onilu, wannan nasara da aka samu a watan Satumba na nuna cewa hukumar Customs ba wai kawai tana cigaba da gyara ba ce, har tana kafa sabon ma’auni na kwarewa da ingantaccen aiki a tsarin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa...
    Shugaban kasar iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana a yau a wajen taron da yayi da gwamnoni jihohin kasar baki daya cewa jamhuriyar musulunci ta iran tana da karfin  juriewa duk wata matsin lamba kuma ba zata taba risunawa duk wani nuna karfi ko cin zarafi ba. Yace kasa kamar iran mai makwabta 16 ba abu ne mai sauki a kakaba mata takunkumi ba, idan muka kara gyara dangantakarmu da makwabtanmu cin sauki zamu iya shawo kan matsin lambar da muke fuskanta, Har ila yau ya kara da cewa ba zasu sa ido kan iyakokin ko wacce kasa ba, amma zamu rufe ido kan duk kasar da ta nemi shiga harkokin kasar ba tare da bata lokaci ba, Iran tasha nanata...
    Rahotanni sun bayyana cewa an gano daruruwan gawawwaki a karkashin burabutsai a yankin gaza bayan sanar da dakatar da bude wuta tsakanin isra’ila da kuma kungiyar Hamas, adadai lokacin da tawagar agaji ke ci gaba da gano gawarwaki da suka makale a karkashin duwatsu bayan kwashen shekaru 2 Isra’ila na kisan kare dangi, Majiyar Asibiti a yankin Gaza ta sanar a yau litinin cewa akalla an gano gawarwakin mutane 323 da suke karkashin burabutsai,  kuma har yanzu akwai gawarwarki sama da 10,000 da ke karkashin gine –gine da aka rusa a yankin Gaza. Bisa kidddigar da majalisar dinkin duniya ta gabatar ya nuna cewa an rusa gidaje 430,000 a yankin Gaza sakamakon hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baqahea yayi gargadin game da barazanar da ake fuskanta na bazuwar fadan da ake yi a kan iyaka tsakanin  kasar Afganistan da kuma kasar Pakistan, a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suke musayar wuta a wurare daban daban dake kusa da iyakokin kasashen. Yace babban abin da ke da muhimmanci a wajen mu shi ne batun tsaro da zaman lafiya a kasashen dake makwabtaka da su, kasashen Pakistan da Afghanistan  yan uwan mu ne musulmi dake makwabtaka da mu, kuma ya yi amanna cewa duk wani kace-nace tsakanin kasashen biyu to zai iya fantsama zuwa wasu kasashe, Jamhuriyar musulunci ta Iran  ta yi kira ga kasashen biyu da su koma teburin tattaunawa, kuma...
    Zamu kawo muku cikakken bayani idan sun bayyana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA October 13, 2025 Labarai Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi  October 13, 2025
    Majalisar Shura ta Jihar Kano ta fara zama da Malam Lawan Shu’aibu Abubakar (Triumph) kan zargin da wasu kungiyoyi biyar ke masa zargin batanci ga Manzon Allah SallalLahu alaihi Wasallama. Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar Kano. Mahalarta sun haɗa shugaban majalisar shurar  Malam Abba Koki da Wazirin Kano, Sa’ad Shehu Gidado, da sakatare, Shehu Wada Sagagi, da mambobin kwamitin da Majalisar Shurar ta kadfa domin zargin binciken zargin da ake wa Malam Triumph.
    A safiyar yau litinin ce majiyar gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan ko kuma ministan harkokin wajen kasar ba zasu halarci taron sanyawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin HKI da Falasdinawa a birnin Sharm sheikh na kasar masar ba. Saboda ba sa son haduwa da shuwagabannin kasashen yamma azzalumai wadanda da makaman sune aka kashe falasdinawa kimani 70,000 a gaza a cikin shekaru 2 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar gwamnatin na cewa shuwagabannin kasar Iran ba zasu amince su zauna kusa da wadanda suka kashe iraniyawa a cikin watan yunin da ya gabata, da kuma jinin mutanen da dama a yankin ba, suna mika masu hannu ba. A taron...
    A safiyar Litinin ɗin nan ƙungiyar Hamas ta saki rukunin farko na ’yan ƙasar Isra’ila bakwai da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza. A ɗaya ɓangaren kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako. Tuni jami’an kungiyar agaji ta Red Cross suka shiga gidan yarin Wada a safiyar domin ɗaukar wani fursuna Bafalasdine da za fitar, wanda ke fama da rashin lafiya. Hamas ta mika su ne ga kungiyar Red Cross a Gaza a yayin da ake da ran sako wasu ƙarin mutum 13 na gaba a Litinin ɗin nanm a cewar hukumomin Isra’ila. Wannan na faruwa ne a yayin da Shugaban Amurka, Donald...
    An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya. Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana dalilin da ya sa Iran ba za ta halarci taron na Sharm el-Sheikh ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana dangane da rashin halartar jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa taron na Sharm el-Sheikh cewa, ba za su iya tunkarar wadanda suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Iran da kuma ci gaba da yi musu barazana da kuma sanya musu takunkumi ba. Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a dandalin X da sanyin safiyar yau litinin cewa: “Iran ta nuna matukar jin dadin ta ga gayyatar da shugaba Sisi ya yi wa Iran na halartar taron na Sharm el-Sheikh. Duk da Muradin Iran din na tattaunawa...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta gayyaci muqaddashin jakadan kasar Oman a kasarta Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gayyaci babban jami’in ofishin jakadancin kasar Oman a birnin Tehran a jiya Lahadi, bayan wani rade-radin da ake yadawa cewa; Mutane biyu a kasar Oman sun mutu sakamakon shan ruwan ma’adinai da aka shigo da su daga kasar Iran. Bayan wasu zarge-zarge marasa tushe da wasu kafafen yada labarai na kasar Oman suka wallafa na alakanta mutuwar mutane biyu a masarautar Oman da shan ruwan ma’adinan da aka shigo da su daga kasar Iran, a ranar Lahadin da ta gabata ne Abdul Rasoul Shabibi, shugaban sashen  ma’aikatar kula da tekun Farisa ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ya gayyaci mai kula...
    Kasar Yemen ta gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan fuskantar hare-hare masu zafi idan har ta karya yarjejeniyar Gaza A ranar Lahadin da ta gabata, Hazam al-Assad, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullahi ta Yemen, ya gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan karin fuskantar hare-hare masu zafi idan ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. A wata sanarwa da ya fitar ta hanyar gidan radiyo Sputnik ta kasar Rasha, Hazam al-Assad ya tabbatar da cewa: Yemen za ta dakatar da kai hare-hare kan gwamnatin mamayar Isra’ila, idan har ta yi aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza. Tun da farko dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila da kungiyar Hamas sun rattaba hannu...
    Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba. Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.” Trump ya kara da...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
    Masar za ta shirya wani taron kasa da kasa kan zaman lafiya a birnin Sharm el-Sheikh da ke bakin Tekun Maliya a ranar Litinin, wanda Shugaba Abdel Fattah el-Sisi da takwaransa na Amurka, Donald Trump, za su jagoranta.   Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta bayyana cewa taron zai tattaro shugabanni daga kasashe fiye da 20. Manufar taron ita ce “kawo karshen yakin Gaza, da karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya, da kuma fara wani sabon mataki na tsaro da kwanciyar hankali a yankin,” in ji sanarwar. A ranar Laraba Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da mataki na farko na wani shiri mai matakai 20 da ya gabatar a ranar...
    Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da ta danganta da na karya da Amurka ke yi wa kasar cewa ta na da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, tana mai daukar wadannan zarge-zarge a matsayin wani makirci na siyasa da nuna kiyayya. A cewar ma’aikatar harkokin wajen Cuba, hukumomi “ba su da wani takamaiman bayani kan ‘yan kasar Cuba” da suka shiga ko kuma suke shiga cikin rikicin “da kansu” a cikin “dakarun sojan bangarorin biyu da ke rikici da juna” tsakanin Rasha da Ukraine. Tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, kotunan kasar Cuba sun saurari kararrakin laifuka tara da suka shafi ayyukan sojan haya, inda suka yanke wa wadanda ake tuhuma 26 hukuncin zaman gidan yari tsakanin...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar. Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi. Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata. “Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana. RN    
    Sojojin Nijeriya sun kashe wani kwamandan ƙungiyar ƴan ta’adda IPOB/ESN da ake nema ruwa a jallo, mai suna ‘Alhaji’, tare da wasu mutane 26 a jerin hare-haren da suka kai a sassan ƙasar tsakanin 8 zuwa 11 ga Oktoba, 2025. Rundunar Sojin ta ce an kuma ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace makamai, da harsasai, da kuɗaɗe. A kudu maso gabas, Sojojin Operation UDO KA sun kai farmaki a Izzi, jihar Ebonyi, inda suka kashe ‘Alhaji’ bayan ya yi yunƙurin kwace bindiga daga hannun wani Soja lokacin kama shi. Haka kuma, a jihar Imo, an rusa wata maboyar IPOB/ESN da ake amfani da shi wajen horar da mambobi. Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
    Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa. Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News. Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Ɗaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki. Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Makaie ya tir da HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a kudancin kasar, Lebanon wanda ya sabawa da farko yarkeniyar tsagaita wutan da ta cimma da kungiyar Hizbulla a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 sannan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Baghaei ya bayyana cewa ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon a kai a kai, da kuma shirun da kasashen duniya suka yi duk sun sabawa dokokin kasa da kasa wadanda HKI da wadanda suke riya daukar nauyin kola da cewa an dabbaka yarjeniyar MDD na kuduri mai lamba 1107. Ya zargi kasashen Faransa da kuna Amurka wadanda suka gabatar da kansu a matsayin masu lamuni don aiwatar...