Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya
Published: 24th, October 2025 GMT
Kazalika, har yanzu batun tsohon shugaban Majalisar Wakilai wato Salisu Buhari, na 1999, na yin amfani da Takardun karatu na bogi da ya yi iƙirarin ya samo daga Jama’iar Toronto, baƙalar na ci gaba da kafa babban misali, a ƙasar.
Badaƙalar ta sa, ba ta tsaya nan ba, ya kuma ƙaryar shekarun na haihauwa, domin kawai, ta tsaya takarar siyasa, a wancan lokacin, wanda kuma ya nuna turjiya daga sauka daga muƙamin na nsa duk da ɗimbin hujjojin da suka bayyana a kansa, inda bayan komai ya bayyana ƙarara, ya sauka daga kan muƙamin shugabancin Majlisar a 2000, ya kuma ɓarke da kuka a Majalisar, ya amsa cewar, Takardunsa na bogi ne.
Haka ita ma, tsohuwar ministan kuɗi Kemi Adeosun, aka samu hanunta dumu-dumu a cikin irin wannan ɗabi’ar ta aikta badaƙala, bayan an gao cewa, Takardar ta neman tsame ta daga yi wa ƙasa hidima, ta bugi ce.
Haka zalika, aikata irin wannan badaƙalar ta kwana-kwanan ita ce ta ministan ƙirere, kimiyya da fasaha wato Uche Nnaji, wanda shi ma, ya gabarwa da shugaban ƙasa Takardun karatunsa na bogi, da ya yi iƙirarin ya samo daga jami’ar Nsukka, domin a tantance shi, ya zama ministan wannan ma’aikatar.
Wannan badaƙalar, za iya cewa, kusan ta faro ne, tun a cikin Azuwan makaranta wanda hakan ya nuna cewa, ba daga kan ‘yan siya ta samu asali ba, inda masu sanya ido kan ɗaliban da ke kan zana jarrabawa, inda masu sanya idon, ke yiwa wasu ɗaliaban jigar Takardun satar amsar jarrabawa.
Hakazalika, lamarin ya kuma nuna jadda wasu iyayen ke haƙilon ganin ‘ya’yansu, sun zana jarrabar kammala sakandare a cibiyon zama jarrabawa, na neman na neman sa’a, domin kawai ‘ya’yansu, su lashe jarrabawar.
Akwai kuma batun yadda ake sauya samakaon jarrabawa yayin kwafo sakamakon WAEC ta hanyar haɗa baki, da wau gurɓatattun ma;aikata a ma’aikatun ilimi da kuma bayanan shidar karatun mutum wato CƁ da Takarun bogi na NYSC.
Irin wannan lamarin, ya kuma haifar da samun wasu matasan ƙasar na shiga cikin mummunar ɗabi’ar damfara ta kafar Internet, wato waɗanda ake yiwa laƙabi da, ‘Yan Yahoo-Yahoo”, inda suka damfarar mutane miliyoyin kuɗaɗe, ta nahyar yin kutse a cikin Asusun ajiarsu na Bankuna.
Lamarin na kuma sanya wasu ma’aikatan Gwamnati da wasu sanatoci, yin arigizo a cikin kasafin kuɗi da kuma biyan wasu ‘yan kwangila kuɗaɗen yin kwangila wanda daga baya, su yi watsi, da aikin, bayan sun karbi kuɗin yin kwagilar.
Abin dubi a nan shi ne, idan har masu aikata irin ɗabi’ar za su iya wucewa da tunanin manyan hukumomin ƙasar wajen yin amfani da Takardun karatu na bogi, kamarsu, majalisar dattawa ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya DSS, hakan ya nuna ƙarara, orin gazarwar waɗannan hukumomin, musamman duba da yadda minista sukutum ya miƙa gabatar da Takardun karatu na bogi, domin a tantance shi a muƙamin minista.
A ra’ayin wannan Jaridar, ya zama wajibi, wannan lamarin, ya sama na ƙarshe da wasu ke aikata wa a ƙasar kuma ya zama wajibi, majalsar ƙasar ta tabbatar ana gudanar da cikakken bincike a ɗaukacin mayan makarantun ƙasar da kuma samo sahihan bayanai na ministocin da ke kan muƙamasu da shuwagannin hukumomin Gwamnati da kuma na ‘yan majalisar da suka samu Takardun sheda na NYSC.
Bugu da ƙari, jami’oin ƙasar da kuma mahukaunata a NYSC, su rinƙa yin amfani da sahihiyar kafar intanet da aka aminta da ita, wajen wallafa sunayen wa rijista.
Kazalika, ya zama wajibi, a rinƙa hukunta duk ɗan ƙasar da aka same shi, da aikata wannan mummunar ɗabi;ar domin hakan ya zama izina, ga sauran masu tunanin aikata hakan, a gaba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: da Takardun
এছাড়াও পড়ুন:
Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su.
A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada cewa gudanar da PoS ba tare da rajista ba ya saɓa wa Dokar Kamfanoni ta 2020 da kuma ka’idojin Babban Bankin Najeriya (CBN).
Hukumar ta kuma zargi wasu kamfanonin fasahar kudi (fintech) da daukar wakilai ba tare da rajista ba, tana bayyana wannan dabi’a a matsayin da sakaci kulawa da kuma barazana ga daidaiton tsarin kuɗi na ƙasar.
Ta ce hakan na jefa miliyoyin ’yan Najeriya, ciki har da ’yan kasuwa ƙanana da masu aiki a karkara, cikin haɗarin tattalin arziki da asarar jari.
Ɗa da mahaifi sun mutu a cikin rijiya a Kano Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi“Duk fintech da ke ba da damar ayyukan da ba bisa ƙa’ida ba za a saka su cikin jerin waɗanda ake sa wa ido, sannan za a kai rahotonsu ga CBN. Duk masu PoS an umurce su da su yi rajista nan da nan. Bin doka wajibi ne.
“Daga ranar 1 ga Janairu, 2026, ba wani mai PoS da zai ci gaba da aiki a Najeriya ba tare da cikakken rajista ba,” in ji CAC.
Wannan daiba shi ne karo na farko da aka yi kira kan buƙatar tsaurara dokokin sa ido kan harkar PoS ba.
An sha yin kira ga CBN da ya ɗauki matakan gaggawa wajen daƙile yawaitar damfara da ke addabar harkar PoS a faɗin ƙasar.