2025-10-18@14:01:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14
«Primary da ke»:
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi iƙirari cewa ministoci da manyan hafsoshin sojin ƙasar sun taya shi murnar bayan bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala. Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa ministoci da manyan jami’an tsaron da ministocin sun kira shi a waya suna jaddada goyon bayansu da niyyar biyayya ga kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma abin da al’umma suka zaɓa. Ya bayyana haka ne wani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, yana mai nuna godiya ga waɗanda suka goyi bayansa, tare da jaddada cewa wannan lokaci yana da muhimmanci matuka ga kasa. Ya ce, “Ina godiya daga zuciyata ga ministoci...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima October 17, 2025 Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya wallafa sako a shafinsa yana cewa ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Vladmir Putin yakan yiyuwar za su gana da juna a birnin Bhudapast na kasar Haugary, domin lalubo hanyar kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban kasar na Amurka ya kuma bayyana tattaunawar da su ka yi a jiya Ahamis da Vladmir Putin da cewa ta yi amfani matuka, kuma na sami ci gaba. Har ila yau shugaba Donald Trump ya ce; Su biyun sun amince da cewa a mako mai zuwa manyan jami’an kasarshen biyu za su gana da juna,kuma ministan harkokin wajensa Marco Rubio ne zai jagoranci tawagar Amurkan. A gefe daya a yau Juma’a ne ake sa ran yin ganawa a...
Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye. Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na ƙuri’u a rumfunan zaɓe da dama. Sun buƙaci Shugaba Paul Biya, wanda ke neman wa’adin mulki na takwas a zaɓen da ya gaggauta miƙa saƙon taya murna ga Issa Bakary Tchiroma. “Muna kira ga shugaban ƙasa mai barin gado da ya gaggauta taya sabon shugaban ƙasa murna,” in ji ƙungiyar,” in ji wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Anicet Ekane da Djeukam Tchameni, suka fitar a...
Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Jamhuriyar Kamaru da ake ci gaba da kirgawa ya nuna jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary, ya samu gagarumin rinjaye a yankunan da a bayan Shugaba Paul Biya ya saba rinjaye. Shugaba Paul Biya mai shekaru 92 yana fuskantar abokan hamayya 11 cikin har da tsofaffin mukarrabansa, da ma tsoffin ministocinsa da ke neman kujerarsa da ya shafe shekara 43 a kai kuma yake namen wa’adi na takswas. Cikinsu har da tsohon Ministan Yawon Bude Ido, Bello Bouba Maigari, da tsohon ministan Ayyuka, Bakary, wanda ya yi murabus a watan Yuli domin shiga takara kuma ya sama mafi shahara bayan doka ta haramta wa madugun adawa Maurice Kamto shiga zaben.. Biya ya ki yin tsokaci...
An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya. Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin...
Gwamnatin Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary International sun ƙaddamar da shirin aikin jinya domin rage mace-macen mata da yara a faɗin jihar. Shirin da aka gudanar a Ƙananan hukumomi uku da suka haɗa: Gombe da Kaltungo da Yamaltu-Deba, inda aka yi wa jama’a gwaje-gwaje, jinya da wayar da kai a unguwannin Yelenguruza da Kagarawal. An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000 Shugaban Rotary Reproductive, Maternal and Child Health a Nijeriya, Farfesa Emmanuel Adedolapo Lufadeju, ya bayyana cewa fiye da mutum 120 aka duba a unguwar Kagarawal kaɗai, inda aka samu kashi 70 cikin 100 sun kamu da zazzaɓin cizon sauro. Ya ce, tun daga...
Ƙungiyar Rotary Club ta Kaduna Metropolitan ta raba kayan haihuwa fiye da 70 ga mata masu juna biyu a cibiyar kiwon lafiya ta Mando, Afaka. Da yake jawabi a wajen taron, shugaban Rotary Club na Kaduna Metropolitan kuma shugaban Rotary Action Group for Peace, Rotarian Luqman Babatunde, ya jaddada cewa kayan haihuwar ba na siyarwa ba ne, kyauta ce don tallafa wa mata masu juna biyu musamman marasa ƙarfi. Ya ce wannan tallafin ana gudanar da shi ne a wurare daban-daban a jihar Kaduna, yana mai jaddada cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya yin komai ba, shi ya sa ake buƙatar goyon bayan ƙungiyoyin sa-kai da na taimakon jama’a irin su Rotary. Ya bayyana cewa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, ɗaya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan ƙasar. Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi — shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ke iya haifarwa a rayuwar talaka? NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki” DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa A kan wannan sauyi da dalilansa ne shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari. Domin sauke shirin, latsa nan
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta yi watsi da bukatar Isra’ila na soke ko kuma ta dakatar da sammacin kama firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan harkokin sojin kasar Yoav Gallant. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kotun ta ICC ta ce ta amince da daukaka karar da Isra’ila ta shigar na sake duba hurumin kotun kan laifukan da aka aikata a yankunan Falasdinu. A watan Nuwamba 2024, kotun ICC ta bayar da sammacin kame Netanyahu da tsohon ministansa na harkokin soji, Yoav Gallant, bisa laifukan cin zarafin bil’adama da laifukan yaki da suka shafi kisan kare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a zirin Gaza. Hukuncin ya tilastawa dukkan...
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta hanyar yin watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu. Esmail Baghai ya bayyana haka ne a cikin wani sako a asusunsa na X, bayan ziyarar aiki da Netanyahu ya kai kasar Hungary duk da sammacin kame shi da kotun ICC ta bayar kan laifukan yaki da cin zarafin bil adama da gwamnatinsa ta yi a zirin Gaza. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce : Sammacin kame jami’an gwamnatin Isra’ila da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi na nuni da yadda duniya ke nuna bacin rai kan kisan kiyashi, laifukan yaki, da...
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) mai hedkwata a birnin Hague ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Hungary ta dauka na kin mutunta sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da zai ziyarci kasar da ke tsakiyar Turai a ranar Alhamis. Mai magana da yawun kotun, Fadi El Abdallah, ya fada yayin wani taron manema labarai cewa, bai kamata mambobin kotun ICC su yi watsi da hukuncin kotun ba. Kakakin ya ci gaba da cewa dole ne mambobin kotun su aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke. Ana sa ran Netanyahu zai isa Budapest a yammacin yau Laraba don ziyarar kwanaki hudu, bisa gayyatar Firaministan Hungary Viktor Orbán. Shugaban na Hangari mai tsatsauran ra’ayi ya gayyaci takwaransa...
Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa ba ta shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje ba, duk da cewa farashin kayan abinci ya ragu a kasuwanni. Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Farfesa Abubakar Kyari, ya bayyana cewa, ko da yake gwamnatin ta yi tunanin shigo da abinci a lokacin da farashinsa ya yi tashin gwauron zabo, daga bisani ta janye wannan shawarar. An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu Ministan ya danganta saukar farashin kayan abinci da ƙoƙarin manoma da suka koma gonaki a daminar bara, wanda ya sa amfanin gona ya yi yawa. Ya kuma buƙaci ‘yan kasuwa da su rage farashi domin jama’a...
Rikici ya ɓarke tsakanin Seaman Abbas da matarsa Hussaina, da kuma mai gabatar da shirin nan na Brekete Family, Ahmad Isa da aka fi sani da Ordinary President. Rikicin ya fara ne bayan Hussaina ta fitar da wani bidiyo tana cewa mijinta na yi mata duka, saboda zargin ta da yake da sama da faɗi da wasu kuɗaɗe da mota da aka ba su a matsayin tallafi. A bidiyon ta kuma bayyana cewa tsangwamar ba ga iya shi ta tsaya ba, har na danginsa, abin da ta ce ya yi sanadiyar komawarta gidan iyayenta. To sai dai mijin nata ya fito ya musanta zarge-zargen, inda ya ce suna zaune lafiya, hasali ma ta je ganin gida ne bayan rashin lafiyar...