Majalisar Tattalin Arziki Ta Amince da Shirin Gyara Cibiyoyin Horar da Jami’an Tsaro
Published: 24th, October 2025 GMT
Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) ta amince da shirin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu na sake fasalin da kuma zamanantar da cibiyoyin horar da jami’an tsaro a faɗin ƙasar. Wannan mataki ya biyo bayan taron majalisar na 152 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya gabatar da jawabi kan dabarun cimma burin Shugaban Ƙasa na samar da tattalin arzikin da ya kai darajar dala tiriliyan guda.
An kafa kwamitin da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ke jagoranta don tsara cikakken tsari na gyaran da sabunta cibiyoyin horar da jami’an ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro cikin wata guda. Mambobin kwamitin sun haɗa da gwamnonin jihohin Kaduna, Ogun, Taraba, Akwa Ibom, Zamfara, da Nasarawa, yayin da tsohon Sufeton ƴan sanda na ƙasa, Baba Usman, zai zama sakataren kwamitin.
Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin inganta yanayin cibiyoyin horar da jami’an tsaro domin ƙara ƙarfin horo da ƙwarewa tare da tabbatar da ƙwararru da ƙwarin gwiwar ma’aikatan tsaro.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya jagoranci taron, ya shawarci gwamnatocin jihohi su mai da hankali wajen inganta rayuwar jama’a ta hanyar gwamnati mai ma’ana da shiri na gaba. Haka kuma, majalisar ta duba bayanin da Ofishin Mai Ba da Shawara Kan Tsaron Ƙasa (ONSA) ya gabatar kan tsarin tunkarar matsalar ambaliyar ruwa, wanda ke da nufin ƙarfafa tsarin gargadin gaggawa da shirin kare jama’a daga ambaliyar ruwa a ƙasar baki ɗaya.
Dangane da burin tattalin arzikin gwamnati, Sanata Bagudu ya gabatar da taswirar cimma tattalin arzikin dala tiriliyan guda nan da shekarar 2033, wanda ke ta’allaka da daidaiton tattalin arziki, samar da ayyukan yi, wadatar abinci da inganta gasa tsakanin jihohi.
NEC ta kuma yaba da tsarin cimma Muradin aikin gona na jihar Katsina tare da shawartar sauran jihohi su rungumi irin wannan tsarin na fasaha domin ƙara yawan amfanin gona da haɗa manoma da tsarin gwamnati. Majalisar ta kuma umarci Ma’aikatar Noma da samarda Abinci ta haɗa da kafa cibiyoyin bayanai da lura da harkokin noma a kowace yankin siyasa a kasafin 2026.
Kwamitin NEC na wucin gadi kan satar man fetur, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana cigaba da aka samu wajen haɗa kai da manyan masu ruwa da tsaki a masana’antar mai don dakile satar man. Majalisar ta ƙarfafa kwamitin da ya ƙara zage damtse wajen ƙara yawan fitar da danyen mai sama da ganga miliyan 1.72 a kowace rana tare da faɗaɗa aikin sa zuwa kan satar ma’adinai. Ana sa ran Najeriya za ta kai matakin samar da ganga miliyan 2.5 na danyen mai a kowace rana nan da ƙarshen shekarar 2025.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Shugaban Ƙasa Majalisar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, Ta Kaddamar da Dakin Karatu Na Zamani a Zamfara
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da Dijital E-Learning Library a Gusau, Jihar Zamfara — ɗaya daga cikin jihohi goma da aka zaɓa a faɗin ƙasar domin aiwatar da wannan muhimmin aiki ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da haɗin gwiwar Hukumar bunkasa ayukkan fasaha ta kasa (NITDA).
A yayin bikin kaddamarwar, Sanata Tinubu ta bayyana cewa wannan aiki ba wai game da fasaha da kwamfuta kawai ba ne, amma yana nufin ƙarfafa matasa, rage gibin fasaha (digital divide), da kuma buɗe sabbin ƙofofin ilimi da ƙirƙira ga al’ummar Zamfara da ma Najeriya baki ɗaya.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, wacce Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta wakilta, ta bayyana cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaba a kowace al’umma.
Ta ce, a wannan zamani na dijital, samun kayan koyon zamani ba wata alfarma ba ce, amma wajibi ne domin ci gaban ilimi.
A cewarta, ta hanyar wannan dijital library, dalibai, malamai, masu bincike da ma jama’a gaba ɗaya za su sami damar shiga manyan bayanai, albarkatu da dama na ilmantarwa a sauƙaƙe.
Sanata Tinubu ta bayyana cewa Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) yana da burin tallafa wa ilimi, ƙirƙira da ci gaban zamantakewa, kuma wannan E-Learning Library na ɗaya daga cikin manyan alamu na hangen nesa na shirin.
Ta kuma yaba wa Ma’aikatar Sadarwa, Ƙirƙira da Tattalin Arzikin Dijital da kuma NITDA bisa ƙwarewar su wajen aiwatar da aikin.
A nata jawabin, Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta nuna godiya mai zurfi ga mijinta, Gwamna Dauda Lawal, bisa jajircewarsa wajen inganta harkar ilimi a jihar.
Ta shawarci dalibai, malamai da masu bincike da su amfani da wannan cibiyar ta dijital yadda ya kamata, domin bunƙasa ilimi da gina kyakkyawar makoma ga matasa da ƙarni masu zuwa.
Tun da fari, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Zamfara, Malam Wadatau Madawaki, wanda Maryam Yahaya, Babban Sakataren Ma’aikatar, ta wakilta, ya yaba wa Sanata Oluremi Tinubu bisa ƙoƙarinta wajen bunƙasa ilimin dijital ta hanyar kafa wannan E-Learning Library ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative.
Kwamishinan ya bayyana aikin a matsayin babbar nasara wajen bunƙasa ƙirƙira, haɗa kai ta hanyar fasaha da kuma tabbatar da ingantaccen ilimi ga ’yan Zamfara.
Haka kuma, ya yaba wa Uwargidan Gwamna Hajiya Huriyya Dauda Lawal bisa wakiltar Uwargidan Shugaban Ƙasa da kuma irin goyon bayanta da jajircewa wajen cigaban ilimi a jihar.
Madawaki ya ƙara da cewa wannan E-Learning Library na tafiya da hangen nesa na Gwamna Dauda Lawal, wanda tun bayan hawa mulki ya ayyana dokar ta-baci kan ilimi, matakin da ya haifar da gagarumin ci gaba a fannin ilimi a jihar.
Aminu Dalhatu