Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Published: 26th, October 2025 GMT
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa Singapore a yau Asabar don ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar firaministan Singapore Lawrence Wong.
Li ya bayyana cewa, a cikin shekaru 35 da suka gabata tun bayan kafa huldar diflomasiyya, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da kasancewa mai kyau da samun ci gaba, tare da zurfafa amincewa da juna a siyasance, da hadin gwiwa mai amfani da kuma mu’amala ta kut-da-kut tsakanin mutanensu, wanda ya kafa misali don koyo tare da hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare a tsakanin kasashe.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin aiki tare da Singapore don karfafa daidaita dabarun ci gaba, da fadada hadin gwiwa mai amfani ga dukkan bangarorin biyu, da ci gaba da yin aiki tare a cikin shirin zamanantarwa, da kuma bayar da gudummawa sosai wajen tabbatar da hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban da kuma bunkasa ci gaba na bai-daya a yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa Hamas ta bayyana cewa za ta mika makamanta ne kawai ” idan Isra’ila ta kawo karshen mamaya, tana mai jaddada cewa ba za a iya kwance damarar makamai ba a cikin yanayin da ake ciki na zaluncin soja da siyasa.
Babban jami’i a ofishin siyasa na Hamas kuma babban mai shiga tsakani na kungiyar, Khalil al-Hayya, ne ya bayyana hakan inda yake cewa idan mamayar ta kare, za a sanya wadannan makaman a karkashin ikon gwamnatin kasar Falasdinu.”
Ofishinsa ya fayyace cewa kalmar “ƙasa” tana nufin “ƙasar Falasɗinawa mai zaman kanta” mai cikaken iko.
“Har yanzu ana ci gaba da tattaunawa game da kwance makamai tsakanin kungiyoyi daban-daban da masu shiga tsakani, kuma yarjejeniyar tana cikin farkon matakanta ne kawai,” in ji shi.
“Mun yarda da tura sojojin Majalisar Dinkin Duniya a matsayin dakarun masu sa ido kan iyakokin da kuma tabbatar da kare yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza,” in ji Khalil al-Hayya.
Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinawa a Gaza ta sanar a ranar Lahadi cewa tun lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki, gwamnatin Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 367 tare da raunata wasu 953.
Sojojin Isra’ila sun kuma karya yarjejeniyar tsagaita wuta akalla sau 591 tsakanin 10 ga Oktoba zuwa 2 ga Disamba, ta hanyar hare-haren sama, manyan bindigogi da kuma harbi kai tsaye, a cewar ofishin manema labarai na gwamnati a Gaza.
Tun bayan fara kai hari kan kisan kare dangi da Isra’ila ta yi wa Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, akalla Falasdinawa 70,354 ne aka kashe, yawancinsu mata da yara, yayin da sama da 171,030 suka jikkata.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi) December 7, 2025 Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila December 7, 2025 Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167 December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166 December 7, 2025 Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya December 7, 2025 Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba December 7, 2025 Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa December 7, 2025 Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci