Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru 40, ba kawai magana ce ta fafutuka ba, har ila yau kalubale ne ga shugabanni.

 

Matakin Dasuki ya kasance wani muhimmin lamari a farfajiyar siyasar Najeriya, inda ’yan siyasa kalilan ke ja da baya daga mukaman su. Sanarwar sa an fassara ta sosai a matsayin wakilcin  gwagwarmayar adalci tsakanin tsararraki wanda ya taimaka wajen jagoranta, wanda ke nufin rage gibin da ke tsakanin tsofaffi da matasa a shugabancin kasa.

 

Yayin da yake waiwayen tafiyar siyasarsa a tsawon shekaru 14 wadda ta hada da Majalisar Dokoki ta Jiha, Majalisar Wakilai ta Tarayya da Majalisar Zartarwa ta Jiha, Dasuki ya bayyana godiya ga mazabarsa, abokan aikinsa, da kuma ubangidan siyasarsa, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

 

Ya ce “Duka babu yadda za a yi wadannan nasarorim su samu ba tare da cikakken goyon baya maras iyaka daga ubangidan siyasa ta ba, kuma jagora na Mai Girma Sanata Aminu Waziri Tambuwal (Mutawallen Sakkwato)

 

“Shugaba ne da ya ga baiwa a cikin wani matashi, ya tallafawa burina na siyasa, ya ba ni damar yin hidima a cikin majalisarsa. Har abada zan kasance mai godiya gare shi saboda amincewar da ya nuna a gareni, da kuma damar da ya bani na jagoranci da koyon darussa masu matukar muhimmanci.

 

“Ga mazaba ta, kun ba ni amincewar ku, kuma na dauke ta a matsayin alamar girmamawa. Ina neman goyon bayanku wajen tabbatar da wannan babban sauyi zuwa sabon babi. Tafiyar da ke gaba ba mai sauki ba ce, za mu fuskanci kalubale da jarrabawa, amma za mu iya shawo kan su idan muka hada kai bisa manufa daya, wato gina Nijeriya mafi kyau, karkashin jagorancin matasa masu kuzari, basira, da kwazo.

 

“Ga matasa babu wani sauran jira kuma! Babu wani sauran uzuri! Babu sauran shiru! Ku dauki matsayin ku. Ku tsayu da karfi. Ku karbi jagoranci da jarumta da gaskiya da hangen nesa. Ku gina mafi kyawun kyakkyawar makoma.” Ya fada cike da kwarin guiwa.”

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna October 26, 2025 Labarai ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano October 26, 2025 Labarai Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma October 26, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Ya tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP a Kaduna tana cikin haɗin kai da zaman lafiya, inda ya bayyana batun tsige shugaban a matsayin yunƙurin ƙirƙirar rikici da tashin hankali a cikin jam’iyyar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa October 22, 2025 Siyasa Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya October 21, 2025 Siyasa Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu October 20, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu
  • Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe
  • Kwamishinan Gombe ya rasu a hatsarin mota
  • Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta
  • Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri
  • Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa
  • Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Shi Beli
  • Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa
  • Matasa Dubu Ɗaya Za Su Samu Horon Fasahar Zamani A Nasarawa — Remi Tinubu