2025-10-21@00:19:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2496
«naira biliyan 500»:
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati ta samu nasarar tara dukiyar da ta haura naira biliyan 500 a tsawon shekaru biyu na gwamnatinsu. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana haka ne a yayin wani taron bita da ƙara wa juna sani na alƙalai da Hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar Hukumar Shari’a ta Najeriya (NJC) suka shirya a birnin Abuja. Red Cross ta kafa cibiyoyin rage haɗurran bala’o’i a makarantun Gombe NLC ta sa zare da gwamnati kan yajin aikin ASUU Shettima ya buƙaci alƙalai da sauran ma’aikatan ɓangaren shari’a da su ƙara ƙaimi tare da yin aiki bisa gaskiya da adalci, yana mai...
Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu. Asrani, wanda asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, ya rasu yana mai shekaru 84, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350. Dan wasan finafinan, ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin jarumi wanda ake kira da mai taimaka wa jarumi wato supporting actor. Daga cikin fina-finansa da suka yi fice akwai Sholay, inda ya fito a matsayin ɗansand da Bawarchi da Chupke-Chupke da Hera Pheri da Muqabla da Dhamaal da Yamla Pagla Deewana da Dillagi da Welcome da Bhool Bhulaiya da Garam Masala da Baghban da The Burning Train da Ajnabee da Seeta aur Geeta da...

Wakilin Amurka Na Musamman A Siriya Ya Matsa Don Ganin Kasashen Saudiyya Da Lebanon Da Kuma Siriya Sun Kulla Alaka Da Isra’ila
Wakilin Amurka na Musamman a kasar Siriya ya matsa kaimi domin ganin kasashen Saudiyya da Lebanon da kuma Siriya sun kulla alakar jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack, ya gabatar da manufofinsa na sake fasalin yankin Gabas taTsakiya a siyasance bayan kawo karshen yakin Gaza. A cikin dogon hangen nesa, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Barrack ya yi ikirarin cewa abu mafi muhimmanci shi ne samar da zaman lafiya a yankin, da kwance damarar Hizbullah, da shigar da kasashen Labanon da Siriya cikin yarjejeniyoyin kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa Saudiyya ma tana dab da kyautata alakarta da haramtacciyar kasar Isra’ila. Barrak ya bayyana cewa: Taron Sharm...
Hukumar gudanarwar Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da Babban Kocinta Ahmed Garba Yaro Yaro da bai ba da shawara ga Kocin, Ogenyi Evans, nan take. Ta kuma nada tsohon kyaftin kuma Mataimakin Koci, Gambo Muhammad nan take, ya jagoranci lamuran fasaha na ƙungiyar. Mai horar da masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, zai taimaka masa, yayin da Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai ba da ƙarin goyon baya har sai an fitar da sabbin umarni. Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan abin da ta kira “rashin tagomashinta” a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) ta 2025/2026 da ake ci gaba da yi. Sanarwa da kulob ɗin ta fitar, hukumar gudanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan...
Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”. LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar mai taken ‘Sai Masu Gida’ tana fama a ‘yan makonnin nan. Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta kuma ci tarar kungiyar tarar kudi sama da Naira miliyan 9 biyo bayan rikicin da ya ɓarke a yayin da suke karawa da wata kungiya a filin wasa na Sani Abacha. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A...
Dakarun kare juyin musulunc na kasar iran ta bayyana cewa tana da cikakken shiri na kafa fadada dabarun yin hadin guiwa da dakarun karejuyin musulunci na kasar yamen wajen kalubalnatar kasashe ma’abota girman ai da kuma yan sahyuniya. A cikin sakon da kwamandan dakarun kare juyin musulunci na iran ya fitar a jiya lahadi mojor ganar mohammad pakpur ya aike da sakon ta’aziya ga babban hafsan hafsoshin sojin kasar Yamen brigadier janar Yousef hassan al’madani na shahadar major ganar mohammad abdular karin al’gamari wanda yayi fama da rashin lafiya sakamakon rauni da ya ji a harin da isra’ila ta kai masa a watan Augusta tare da wasu abokan aiki har da dan sa mai shakara 13. Har ila yau ya...
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a iya warware takkadama kan shirin Iran na makamashin nukiliya ne ta hanyar diflomasiyya kadai. Grossi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Neue Zeitung ta kasar Switzerland a jiya Lahadi. Shugaban hukumar ta IAEA ya ce, masu binciken ba su sami wata shaida da ke nuna cewa Iran ta boye wani adadi na sinadarin uranium da aka inganta ba. Ya kara da cewa, “Yawancin abubuwan da aka samu na Iran an adana su ne a wuraren da aka sani a Isfahan da Fordow, da kuma wani lokaci a Natanz.” in ji shi. Grossi ya bayyana kwarin gwiwa cewa “za a...
An saki ɗan jarida, Ibrahim Ɗan’uwa Rano, bayan da ƴansanda suka tsare shi a shalƙwatar Rundunar Ƴansanda ta Zone 1 Kano bisa zargin batanci ga wani mutum. Sakin nasa ya biyo bayan suka da matsin lamba daga ƙungiyoyin fararen hula irinsu Cibiyar Fasahar Bayanai da Ci Gaban Jama’a (CITAD), da Amnesty International, da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, waɗanda suka bayyana tsarewar tasa a matsayin mataki na keta haƙƙin ɗan Adam da kuma yunƙurin danne ƴancin ƴan jaridu. Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya Ƙungiyoyin sun buƙaci a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba, suna mai cewa tsarewar ta saɓawa...
Ƴansandan sun kuma yi kira ga ƴan jarida da su tabbatar da daidaito a rahotanninsu, tare da tuntuɓar sashin hulɗa da jama’a na yankin kafin yaɗa labaran da ke da sarƙakiya. AIG Garba ya gargaɗi ƴan jarida da su guji tsoma baki a cikin binciken da ke gudana, yana mai cewa “a bar doka ta yi aikinta.” Sai dai sanarwar ba ta fayyace halaccin tsarewar farko da aka yi wa ɗan jaridar ba, ko kuma ko an kama shi ne ba tare da takardar izinin kame ba. A halin yanzu, ƙungiyoyin kare ƴancin ƴan jarida da ƙungiyoyin farar hula da dama suna ci gaba da kira ga ƴansanda da su saki Ishaq tare da dakatar da duk wani yunƙuri na...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana talauci a matsayin babban abokin gabar ɗan Adam. Ya ce ƙaruwar talauci a Najeriya na ci gaba da jawo rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro, da rashin fata a tsakanin jama’a. ’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a Kano A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook domin bikin Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya, Atiku, ya ce wannan rana tana tunatar da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki muhimmancin ƙara ƙoƙari wajen yaƙar talauci “Talauci ne babban abokin gabar ɗan Adam. Yana haifar da matsaloli kamar rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro da sauransu,” in...
Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar rage kaso 30 cikin 100 na sinadarin gishiri (sodium) a kowane nau’in abincin ɗan fakiti da ake sayarwa a kantuna da wuraren kasuwanci a kasar. Aminiya ta ruwaito cewa gwamnatin za ta soma aiwatar da wannan shirin ne a bana domin daƙile cutar hawan jini da dangoginta a ƙasar. Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a Kano An kama sojoji 20 kan yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin lafiya kuma jakadiyar manufofin rage gishiri, Dokta Salma Ibrahim Anas, ce ta bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a fadar shugaban kasa yayin bikin Ranar Abinci ta Duniya ta 2025 a Abuja. A cewarta,...
Yanzu kuma za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a aiwatar da sauran sharuddan da ke ke kunshe a yarjejeniyar. Masu sanya ido na ganin cewa aikin sake ginan yankin Gaza wanda aka rushe kusan daukacinsa a yakin da aka yi na shekara biyu, zai zama babban kalubale. Wannan ce ranar da kowa ke jira -Trump A lokacin da Donald Trump ya yi jawabi, ya bayyana yau a matsayin “ranar da kowa ya yi ta hankoro da addu’ar ganin zuwan ta.” Shugaban na Amurka ya ce “Wannan yarjejeniya mai matukar tarihi” wadda gungun shugabannin duniya suka sanya wa hannu, na nuna cewa “addu’ar miliyoyin al’umma ta karbu”. Daga nan sai ya ce shugabannin sun samu nasarar...
Ofishin Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a ranar Asabar cewa “Mashigar Rafah a Gaza za ta kasance a rufe har sai abin da hali ya yi a nan gaba.” Ofishin Netanyahu ya kara da cewa, bude mashigar ya dogara ne bisa ga yadda Hamas ta aiwatar da tsarin yarjjeniyar da aka cimmawa wajen mika gawawwakin Isra’ilawa da ke hannunta. Wannan bayanin ya zo ne jim kadan bayan da ofishin jakadancin Falasdinu a Masar ya sanar da cewa za a sake bude mashigar Rafah da ke kudancin zirin Gaza a ranar Litinin mai zuwa. A nata bangaren, kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, matakin da Netanyahu ya dauka yana a matsayin keta sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude...
A wani jawabin da aka yada ta kafar sadarwar zamani ta shafin Facebook jiya, ma’aikatar ta kara da cewa tun lokacin da shi Gwamnan ya dare kan Kujerar mulkin Jihar, mulkin gwamna Inuwa ya kafa dokar ta baci kan lamarin daya shafi ilimi, inda ya bullo da tsare tsare da zuba jari da zummar bunkasa bangaren ilimiin. Wadanda za su amfana da karin tallafin kudin karatun sun hada dalibai masu karatun da suka hada da PhD, MSc, PGD, BSc, HND, NCE, ND, da kuma Satifiket. Da yake na shi jawabin wajen sa albarkacin baki kan ci gaban da aka samu, Shugaban kungiyar dalibai ‘yan asalin Jihar da suke Jami’ar Jihar Gombe, Abubakar Muhammad Yamanga, ya bayyanawa LEADERSHIP cewa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kuduri mai lamba 2231 ya ƙare aiki a yau A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen kasar Iran ya tabbatar da cewa a karshe kuduri mai lamba 2231 ya kare a yau, kuma duk wani kira na farfado da shi ko dawo da wa’adin kudirorin da ya kare, ba shi da wani tushe na shari’a, kuma ba zai iya haifar da wani tasiri na tilasta aiki da shi ba. Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Abbas Araqchi ya aike da wasika zuwa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban kwamitin sulhu...
Shi ma a nasa jawabin yayin gudanar da taron, shugaban kwamitin Alhaji Abdullahi Abdulmalik Digi, ya ce, a shekaru hudu da ya yi yana jagorancin kwamitin sun yi abin da yakamata su yi, inda ya ce, a Azumin bara an dauki yara marayu 2000 da aka raba musu abinci da suka hada da buhunan shinkafa da kuma kayan Sallah da za su dinka, mata aka raba musu shadda mata kuma atamfofi inda jimillar kudin da aka kashe ya zama Naira miliyan 64.2. Bayan wannan an kashe Naira milin 26 wajen biya wa yara 520 kudin makaranta, inda kowane yaro ake biya masa Naira dubu 50 a kananan hukumomi shida na FCT Abuja. Sannan an kashe Naira miliyan 3...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi iƙirari cewa ministoci da manyan hafsoshin sojin ƙasar sun taya shi murnar bayan bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala. Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa ministoci da manyan jami’an tsaron da ministocin sun kira shi a waya suna jaddada goyon bayansu da niyyar biyayya ga kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma abin da al’umma suka zaɓa. Ya bayyana haka ne wani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, yana mai nuna godiya ga waɗanda suka goyi bayansa, tare da jaddada cewa wannan lokaci yana da muhimmanci matuka ga kasa. Ya ce, “Ina godiya daga zuciyata ga ministoci...
A yayin da Najeriya ke karkata zuwa amfani da kayan tsaro na zamani na cikin gida domin ƙarfafa gwiwar jami’an tsaronta a fagen fama, wani ɗan Jihar Katsina ya fara ƙera motar yaƙi nau’in Track Armored Personnel Carrier (TAPC). Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga, inda suka kashe dubban mutane tare da raba wasu da muhallansu gami da rusa harkokin tattalin arziki da na zamantakewa. Ana cikin haka ne wani ɗan asalin yankin Kaita a jihar mai suna Injiniya Ibrahim Lawal Ɗankaba, ya fara yunƙurin ƙera motar yaƙi, wadda ya sanya wa suna Beguwa, a ƙoƙarinsa na tallafa wa yunƙurin gwamnati na daƙile ayyukan ’yan ta’addanci da suka daɗe suna...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe. Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta koma karkashen yarjeniyar NPT, kuma za’a yi mu’amala da shirin kamar sauran kasashen karkashin kula na hukumar IAEA. Tsahar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na bada wannan sanarwan a safiyar Asabar ta kara da cewa dama kudurin na tsawon shekaru goma ne daga yau ta gama aiki. Daga yau shirin Nukliyar JMI zai ci gab aba tare da wani karin ka’idojin...
Kauyukan kasar Iran guda uku, Soheili a kan tsibirin Qeshm, da Kandelous a lardin Mazandaran, da kuma Shafiabad a lardin Kerman na kasar Iran sun shiga cikin zababbun kauyuka a duniya na yawon shekatawa saboda kyauwunsu da kuma samar da dukkan abin kyautata rayuwa a cikinsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto mataimakin ministan al-adu na kasar Iran yana bada wannan sanarwan a jiya Jumma’a. Anoushirvan Mohseni-Bandpei, ya kara da cewa zabar wadan nan kauyuka na kasar Iran cikin kyauyuka wadanda suka cancanci shiga wuraren yawon shakatawa a duniya wanda hukumar ‘ The United Nations World Tourism Organization (UNWTO), ta yi zai bunkasa yawon shakatawa a kasar Iran , kuma ma’aikatarsa tana aiki dare da rana don...
Tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, Janar Alvin Holsey, kwamandan rundunar sojin Amurka ta Kudu, ya yanke shawarar yin murabus nan da watan Disamba, saboda takun-saka tsakaninsa da sakataren tsaron Pete Hegseth, kan rashin jituwar da aka samu game da batun ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean. Rahoton ya bayyana cewa, a makwannin da suka gabata ne Janar Holsey ya bayyana damuwarsa kan sahihancin wadannan ayyuka, yayin da Hegseth ya nuna takaicinsa kan yadda ayyukan ke tafiyar hawainiya, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin bangarorin biyu. A cewar rahoton, manyan jami’an biyu sun tayar da jijiyoyin wuya ne a yayin wani taro a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon a makon da ya gabata, inda suka yi musayar...
Tawagar sun gabatar da kansu ga babban sakataren hukumar gudanarwar ci gaban Jihar Katsina, Dakta Mustapha Shehu. Tawagar sun ce ziyarar wani bangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikace-aikace domin inganta zaman lafiya da kuma sanar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira. Gwamnan Katsina ya yaba wa Bankin Duniya da ya yi hadin gwiwa da Jihar Katsina don fuskantar matsalolin tsaro da kuma tallafa wa ‘yan gudun hijira. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja October 17, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya October 17, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu...

Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka
Abokan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa: Sake dawo da takunkumi bayan karewarsa baya da wani tushe na doka ko tsari Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa game da cikar kudiri mai lamba 2231 kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran a ranar 18 ga watan Oktoba, inda ta bayyana cewa matakin da Amurka da Turai suka dauka na sake daukar matakin kakaba takunkumin da ya kare kan wata kasa tsari ne da baya ya kan wani tushe na doka ko yarjejeniyar kasa da kasa. Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis da ke nuna cikar kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya...
Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da wasu manyan kwangiloli da kudinsu ya haura Naira Biliyan 6, domin karfafa bangarorin noma, ilimi da ci gaban tattalin arziki a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar da aka gudanar a fadar gwamnatin Dutse, kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna kudirin gwamnatin jihar wajen inganta muhimman bangarori da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma. A cewarsa, majalisar ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2 domin sayen babura nau’in Hunter guda 1,180 ga malaman gona a fadin jihar. Ya ce wannan mataki ya yi daidai da kokarin Gwamna...
A taron majalsar zartarwar, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa zabinsa na Amupitan ya yi ta’allaka ne a kan rashin nuna son kai na siyasa, gaskiya da kyakkyawan tarihinsa. Mambobin majalisar, ciki har da shugabanni na yanzu da na baya, sun amince da nadin, suna bayyana Farfesa Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya. Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya ce tarihin Amupitan na ciki da kwazo da adalci da kwarewa da hidimar kasa. Bayan amincewar majalisar, ana sa ran shugaba zai mika sunan Amupitan zuwa majalisar dattawa don tantancewa da tabbatarwa bisa ga tsarin kundin mulkin Nijeriya. Farfesa Amupitan, mai shekaru 58, dan asalin kauyen Ayetoro Gbede a cikin karamar hukumar Ijumu ta Jihar Kogi. Ya...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Ismail Baqaei yayi maraba da dakatar da bude wuta da aka yi tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, kuma yayi kira ga kasashen biyu da su warware sabanin dake tsakanin ta hanyar tattaunawa da kuma diplomasiya. Iran ta dade tana ba da shawarwarin magance matsalolin tsaro a yammacin Asiya da kuma Kudancin Asiya, da kuma nuna rashin amincewa kan tsoma bakin kasashen waje kan rashin fahimtar dake tsakanin kasashen musulimi, yace rikicin dake tsakanin Kabul da islam abad barazana ce ga zaman lafiya yankin, kuma zai amfanar da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi masu so su yi amfani da tarzoma a iyaka. Rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan yayi Kamari a yan kwanakin nan inda...
Rahotanni sun bayyana cewa shakih Naim Qassim babban sakatare janar din hizbullah na kasar labanon ya bayyana a jiya Alhamis a gaban mambobin kungiyar Kashafat Al-Mahadi cewa Amerika da Isra’ila ba za su iya yin galaba akan hizbullah ba, Babban hadafin kafa wannan kungiyar shi ne kokarin wayar da kan yara matasa yan shekara 6 zuwa 18 muhimman alamuran addini, adaidai lokacin da gwamntin sahyuniya take ta kokari wajen yada akidar sahyuniyanci tsakanin yara matasa, kungiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen yada akidar gwagwarmaya ga matasa masu tasowa inda yanzu haka tana da mambobin fiye da 100,000. Shaikh Naim Qaseem ya bayyana muhimmancin wannan kungiyar kuma ya bayyana cewa samuwar wadannan matasa zai kara taimakawa wajen tunkarar dukkan kalubalen dake...
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin tarihi, wanda Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka yi wa Sir Herbert Macaulay, daya daga cikin masu kishin kasa a Nijeriya. A takaice dai, kwamitin bai wa shugaban kasa shawara, kan jinkai, karkashin jagorancin babban mai shari’a; kuma ministan shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, ya bayar da shawarar yin afuwa ga fursunoni biyu da 15 da aka yankewa hukunci, wadanda 11 daga cikinsu sun...

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da KuraAfuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka Ta Bar Baya Da Kura
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin tarihi, wanda Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka yi wa Sir Herbert Macaulay, daya daga cikin masu kishin kasa a Nijeriya. A takaice dai, kwamitin bai wa shugaban kasa shawara, kan jinkai, karkashin jagorancin babban mai shari’a; kuma ministan shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, ya bayar da shawarar yin afuwa ga fursunoni biyu da 15 da aka yankewa hukunci, wadanda 11 daga cikinsu sun...
Kasar Saudiyya ta rage yawan guraben kujerun aikin hajjin da take ware wa Najeriya daga 95,000 zuwa 66,910 daga shekarar 2026. Aminiya ta ruwaito cewa a baya Najeriya ta shafe tsawon shekaru uku tana samun guraben na 95,000 a yayin Aikin Hajjin. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi A cewar Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), wannan sauyi ya biyo bayan gazawar Najeriya wajen cika guraben da aka ware mata a hajjin shekarun 2024 da 2025. Wata sanarwa da, Mataimakiyar Darakta a Sashen Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara, ta sanya wa hannu, ta ce hakan na nufin za...
A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa. A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran. “Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman...
Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki. Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa. Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar noma, inda ta ce, manoma mata da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da wadanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000. Shemau ta kuma mika godiyarta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin kokarin da take yi na bunkasa noman mata a Jihar Zamfara. Sauran hukumomin da kungiyoyin da suke tare da NAWIA...
Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana. Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata Oktobar kowacce shekara domin bikin wannan rana. Shekaru 170 ke nan da fara amfani da maganin kashe radadi, inda wasu likitoci su ka yi gwajin wannan magani a asibitin birnin Massachusetts na kasar Amurka, abin da ya kawo sauyi wajen yi wa marasa Lafia aikin tiyata daga shekara 1846. Malam Aliyu Umar Yusuf na sashen bada maganin kashe radadi na asibitin gwamnatin tarayya FMC...
Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa a koda yaushe makiya suna neman haifar da rikici tsakanin kasashen musulmi domin raunana su, yana mai nuni da barkewar tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan. Mr. Pezeshkian ya bayyana haka ne a yayin wani taro inda ya fayyace matsayin kasar Iran dangane da takun saka tsakanin kasashen musulmi a gabashin kasar Iran. Shugaban ya kara da cewa rikicin baya-bayan nan tsakanin Afghanistan da Pakistan ya haifar da damuwa sosai a tsakanin dukkanin kasashen yankin ciki har da Iran da ke da iyaka da kasashen biyu. Ya kara da cewa, Iran za ta yi iyakacin kokarinta na ganin an rage zaman dar-dar, da inganta tattaunawa, da karfafa dankon zumunci a tsakanin...

Kungiyar Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, Hukumar ta ce, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a Masar ranar Litinin, “Dole ne duniya ta ga abinda ya kasance a Gaza.” Kungiyar ta ce a yanzu dole ne a bar duniya ta ga irin barnar da aka yi, wa matsugunai, da kuma haddassa wahalhalun ga bil adama sanadin yakin da Isra’ila ta yi na...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma nuna iko na bangare guda. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Araqchi yana cewa yana daga cikin manufofin kafa kungiyar NAMA tabbatar da yencin ko wace kasa a duniya. Don haka akwai bukatar nuna wannan a aikace. Dangane da yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran a cikin watan yunin da ya gabata, Aragchi...
Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa. Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu sukarsu a wancan lokaci. Ya jaddada cewa El-Rufai da jam’iyyar APC ba za su iya tserewa daga alhakin halin da Nijeriya ke ciki na rashin tsaro ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October...
Shugaban Majalisar Dabarun Kula da harkokin waje kuma mamba a Majalisar fayyace manufofin kasar Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta tattauna amma ta kin juya akalarta Shugaban majalisar dabarun kula da harkokin waje kuma mamba a majalisar fayyace manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kamal Kharrazi, ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta gudanar da zaman shawarwari, amma bazata amince da dora mata wasu manufofi da suka sabawa muradunta ba. A wata hira da ya yi da shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR, Kharrazi ya ce, “Idan har aka yi shawarwari bisa tushe na hankali, kuma aka mutunta martabar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, to a shirye Iran take ta gudanar da shawarwari, kuma a shirye take ta tattauna,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran da takwaransa na Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falasdinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi Ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falastinu na bukatar kawo karshen mamaya da kuma tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu na cin gashin kansu. Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi da ministan harkokin wajen kasar Tunisiya Mohamed Ali Nafti suka yi a ranar Laraba a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan ba ruwan mu ta NAM karo na 19 a birnin Kampala na kasar Uganda. A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan ci...
Kakakin Majalisar Nasarawa ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa al’ummar Nindama, in ji Govt. ya dauki matakan da suka dace. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya jajantawa al’umma da iyalan harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a kauyen Nindama da ke karamar hukumar Kokona a jihar. Shugaban majalisar yayin ziyarar jajantawa al’ummar yankin ya yi kira da a kwantar da hankulan mazauna yankin inda ya tabbatar musu da cewa Gwamna Abdullahi Sule ya dauki matakan da suka dace domin hana afkuwar lamarin nan gaba. “Wannan abin bakin ciki ne, abin takaici ne, dabbanci da zafi, amma a bar wa Allah Madaukakin Sarki...
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa hukuncin daurin shekaru takwas ba tare da zaɓin tara ba, kan laifin luwadi da ɗan wasan kulob dinsa mai karancin shekaru. Kotun dai wacce ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahuru Muhammad a ranar Laraba ta sami kocin mai suna Hayatu Muhammad da aikata laifin. Tinubu na ƙoƙarin mayar da Najeriya mai jam’iyya ɗaya — ADC Majalisar Dattawa za ta tantance Amupitan a ranar Alhamis Wanda aka yanke wa hukuncin, mazaunin unguwar Sanka ne a ƙaramar hukumar Dala, kuma kotun ta tabbatar da cewa ya aikata laifin har sau biyu a wurare daban-daban. Da farko dai ya musanta zargin da ake masa. Sai dai, bayan tabbatar da laifin...
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, ta sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba, 2025, idan aka kwatanta da kashi 20.12 da aka samu a watan Agusta. A cewar rahoton hukumar, hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya a watan Satumba ta kasance kashi 0.72, yayin da farashin kayan abinci ya ragu da kashi 1.57, idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF Ragin na zuwa ne sakamakon saukar farashin kayayyakin abinci kamar masara, garri, wake, gero, dankali, albasa, kwai, tumatir, da barkono. Haka kuma, an bayyana cewa matsakaicin karin...
Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun samar da sabbin hanyoyin fuskantar makiya wadanda ta daukosu daga abinda ya faru a yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka duka dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Khatami yana fadar haka a jiya a ganawarsa da kwamitin al-amuran tsaro da harkokin waje na majalisar dokokin kasar Iran a ranar Litinin. Khatami ya fadawa kwamitin yadda al-amura suke dangane da harkokin tsaron kasar da kuma al-amura da suka shafiu siyasa, tsaro da shirin sojojin kasar Iran dangane da abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya. Khatami ya kara da cewa yakin kwanaki 12 wanda HKI da...
Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi masa tafi, sunan shi tarayya a aikata laifi. Shugaba Gustavo Petro yana mayar da martani ne akan zancen da shugaban kasar Amurka ya yi a Majalisar “Knesset’ ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce; Isra’ilan ta yi amfani da makaman da ya ba ta da kyau. Shugaba Gustavo ya kara da cewa; wadannan makaman na Amurka sun kashe mutane 70,000 sannan kuma sun jikkata wasu 200,000....
Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya. Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki. Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Hukumar Hana Fatucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce dai da gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harkallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, wadanda su ba su...

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
Daga nan sai kakakin ya ce, “Ba zai yiwu bangaren Amurka ya nemi tattaunawa a bangare guda, alhali a daya hannun yana barazanar kaddamar da sabbin takunkumai kan kasar Sin ba. Wannan ba ita ce hanya mai dacewa ta gudanar da cudanya da Sin ba.” (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani October 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya caccaki Donald Trump kan manufofinsa a yammacin Asiya, yana mai cewa shugaban Amurka ba zai iya da’awar samar da zaman lafiya a yankin ba yayin da yake aiwatar da manufofin wuce gona da iri da kuma hada kai da “masu aikata laifukan yaki.” A cikin wani sako a shafinsa na X, Abbas Araghchi ya ce ikirarin da Trump ya yi a baya-bayan nan na cewa “ya rage makwanni” Iran ta kera makamin nukiliya kafin harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyarta ” karya ce.” “Wannan kawai KARYA ce tsungurungum dinta, kuma ya kamata a sanar da shi cewa babu tabbacin hakan, kamar yadda jami’an leken asirinsa suka tabbatar masa.” Jami’in diflomasiyyar...
Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki. Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin da ma’akatan agajin suka shafe kimanin awa hudu ba su motsa ba saboda luguden bamabaman. Kwamandan hukumar soji da ke yankin ta bayyana cewa an kona motoci hudu tare da lalata wata a cikin tawagar kayan agajin, amma ba a samu asarar rayuka ba a harin da aka kai da jirage marasa matuka da manyan bindigogin atilare a garin Bilozerka. Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Ya kuma kara da cewa JMI zata saurari shawarorin kawayenta amma kuma tana cikin shirin ko ta kwana idan makiya sun yi kuskure sun fadawa kasar da yaki. Baghaei ya na nuni ne da zantawar firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a makon da ya gabata, inda kuma ya bukaci shugaba...
Allah Ya yi wa Shugaban hukumar Zavbe ta Jihar Yobe (SIEC) Dakta Mamman Mohammed rasuwa sakamakon gajeriyar jinya. Marigayi Dokta Mohammed, likita ne kuma ƙwararren ma’aikacin gwamnati. Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jihar Yobe da ke Damaturu a ranar Litinin. Za a yi Sallar Jana’izarsa a yau talata 14 ga Oktoba, 2025, a Fadar Sarkin Fika da ke garin Potiskum. Dakta Mohammed ya shahara wajen sadaukar da kai da sadaukarwa wajen inganta dimokuradiyya da shugabanci na gari a Jihar Yobe, in ji waɗanda suka san shi. Za a yi Sallar Jana’izarsa a yau talata 14 ga Oktoba, 2025, a fadar mai martaba sarkin Fika da ke garin Potiskum.
Mai bai wa shugaban kasar Iran shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta tausayawa a tsakanin matan duniya domin samar da damar gina rayuwa ta jin kai da ‘yan’adamtaka mai dorewa. Malama Zahra Behruz Azar ta gabatar da wannan shawarar ne dai a yayin taron kasa da kasa na mata da aka bude a kasar China. Haka nan ta kuma bayyana cewa; A wannan lokacin muna rayuwa ne a cikin karnin da ci gaba da fasahar kere-kere su ka sauya salon rayuwa, ta yadda kirkirarriyar fasaha ta zama mai matukar tasiri a cikin matakan da ake dauka, kamar kuma yadda Sakandami ( Robot) ya maye gurbin bil’adama a...
Rahotanni sun bayyana cewa wani ƙazamin faɗa ya barke tsakanin wata ƙabilar Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da ƙungiyar Hamas a yankin zirin Gaza bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila. A ranar Litinin da aka fara musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ne rahotanni suka ɓulla game da faɗan da ya ɓarke tsakanin mayaƙan Hamas da ƙabilar Doghmush a ranar Lahadi. Wani jami’in Hamas ya bayyana cewa an samu asarar rayuka daga kowane ɓangare a yayin musayar wutan daga misalin ƙarfe 9.30 na dare ranar Lahadi. Wani mazaunin yankin Sebra da ke Birnin Gaza, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa “Mayaƙan Hamas kimanin 200 ne suka zo aka fafata da su, har sai da suka...
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a ranar Litinin. Piwuna ya ce ASUU ta tsaya tsayin daka tare da sauran ƙungiyoyin Malamai kamar CONUA, da NAMDA, da SSANU, da NASU, wajen goyon bayan yajin aikin da ke gudana. Ya zargi Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da ƙoƙarin rarraba malamai ta hanyar yin alƙawarin biyan wasu ma’aikata albashi. “Ya na ƙoƙarin rarraba kan mu, amma kan mu a haɗe yake. Babu wanda...
Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara himma wajen aikin al’umma (CSR), tana taimakawa hukumomi masu ruwa da tsaki da al’ummomi domin karfafa zaman lafiya da tattalin arziki. A cewar Issa-Onilu, wannan nasara da aka samu a watan Satumba na nuna cewa hukumar Customs ba wai kawai tana cigaba da gyara ba ce, har tana kafa sabon ma’auni na kwarewa da ingantaccen aiki a tsarin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baqahea yayi gargadin game da barazanar da ake fuskanta na bazuwar fadan da ake yi a kan iyaka tsakanin kasar Afganistan da kuma kasar Pakistan, a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suke musayar wuta a wurare daban daban dake kusa da iyakokin kasashen. Yace babban abin da ke da muhimmanci a wajen mu shi ne batun tsaro da zaman lafiya a kasashen dake makwabtaka da su, kasashen Pakistan da Afghanistan yan uwan mu ne musulmi dake makwabtaka da mu, kuma ya yi amanna cewa duk wani kace-nace tsakanin kasashen biyu to zai iya fantsama zuwa wasu kasashe, Jamhuriyar musulunci ta Iran ta yi kira ga kasashen biyu da su koma teburin tattaunawa, kuma...
An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya. Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
Masar za ta shirya wani taron kasa da kasa kan zaman lafiya a birnin Sharm el-Sheikh da ke bakin Tekun Maliya a ranar Litinin, wanda Shugaba Abdel Fattah el-Sisi da takwaransa na Amurka, Donald Trump, za su jagoranta. Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta bayyana cewa taron zai tattaro shugabanni daga kasashe fiye da 20. Manufar taron ita ce “kawo karshen yakin Gaza, da karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya, da kuma fara wani sabon mataki na tsaro da kwanciyar hankali a yankin,” in ji sanarwar. A ranar Laraba Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da mataki na farko na wani shiri mai matakai 20 da ya gabatar a ranar...
Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da ta danganta da na karya da Amurka ke yi wa kasar cewa ta na da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, tana mai daukar wadannan zarge-zarge a matsayin wani makirci na siyasa da nuna kiyayya. A cewar ma’aikatar harkokin wajen Cuba, hukumomi “ba su da wani takamaiman bayani kan ‘yan kasar Cuba” da suka shiga ko kuma suke shiga cikin rikicin “da kansu” a cikin “dakarun sojan bangarorin biyu da ke rikici da juna” tsakanin Rasha da Ukraine. Tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, kotunan kasar Cuba sun saurari kararrakin laifuka tara da suka shafi ayyukan sojan haya, inda suka yanke wa wadanda ake tuhuma 26 hukuncin zaman gidan yari tsakanin...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar. Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi. Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata. “Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana. RN
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa. Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News. Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Ɗaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki. Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a...
Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.” Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna October 12, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Yi...
Abubuwan da ake bukata: Semovita (kamar kofi 3-4), Yis (Babban Cokali da rabi, idan kuna so ya tashi sosai), Suga (Babban cokali 2), Gishiri ( rabin cokali), Man gyada ko buta (Babban Cokali 2), Ruwa mai dumi (kusan 1–1½ kofi, gwargwadon yadda Semon ya sha) Yadda za a hada: Za a samu roba sai a zuba Semobita, yis, Sikari da Gishiri a kwano, a juya su da kyau, sannan a zuba ruwa, a zuba ruwan dumi a hankali a cikin hadin, a na gaurayawa har sai ya koma kulli. Sai a zuba man gyada ko Bota a ciki, a ci gaba da murzawa har kullun ya yi laushi ba ya manne ba. Sannan sai a rufe rubar da leda...
Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata. Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum. Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran...
Bayanan da suka fito daga kasar Indunusiya sun nuna cewa gwammnatin kasar ta ki bada visa ga tawagar wasan jiminastik din HKI da aka shirya za’a yi wasa a birnin Jakarta a wannan watan, domin nuna rashin amincewa da kisan kare dangi da HKI ke yi a yankin Gaza. Wannan matakin yana kara nuna irin yadda batun kisan kiyanshin gaza yayi tasiri sosai hatta a harkar wasanni, kasar dake da yawan musulmi tana aikewa da sako na siyasa ne ta hanyar takawa yan wasan isra’ila birki, da kuma neman goyon bayan duniya ga alummar falasdinu. An tsara cewa tawagar wasan Jemanastik din HKI ta za shiga gasar jiminastik na duniya da za’a yi a Jakarta daga ranar 19-25 ga wannan...
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da kyautar motoci ƙirar Hilux guda shida da babura 30 domin taimaka wa sojoji wajen yaƙi da ’yan bindiga a faɗin jihar. Gwamnan, ya miƙa motocin da baburan ga Kanal Hussaini Rabi’u Toro na rundunar sojoji ta takwas a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi. ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Ya ce wannan kyauta na cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da walwalar al’umma. “Tsaro shi ne babban abin da gwamnatina ta mayar da hankali a kai. Ba za mu yi wasa da harkar tsaro ba. “Za mu ci gaba da tallafa wa jami’an...
Uba ya ce dakarun sun ci gaba da bincike da fatattakar ƴan ta’addan don hana su sake samun damar motsi a yankin Arewa maso Gabas. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro Sojoji Sun Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Kayayyakin Gwamnati A Binuwe October 11, 2025 Tsaro Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba October 11, 2025 Tsaro Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara October 11, 2025
Mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, batun kifar da gwamnatin JMI bayan yakin kwanaki 12 ya kuma fita daga abinda makiya zasu iya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar yanakalto mataimakin shugaban kasa na farko yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, ya kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka dorawa kasar sun so su kifar da gwamnatin JMI a cikin kwanaki 3 zuwa 4 amma suka kasa. Ya ce hatta babban sakataren MDD Antonio Guterres ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da shi dangane daha. Ya kuma tabbatar da cewa makiyan JMI ba zasu iya tumbuke tsarin ba. Yasashen yamma musamman Amurka suna kokarin...
Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza. Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi. Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin. An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen...
Aƙalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar ’yan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi. Wani mazaunin yankin mai suna Ɗanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa. “Kashe Sule ya tayar da hankulan al’umma, inda manoma suka ɗauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,” in ji shi. Ya ƙara da cewa makiyayan sun sha faɗa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riƙa wucewa da shanunsu ta...
A cewarta, shirin ya taimaka wajen noman shinkafa da ta kai kimanin tan 99,452, wacce kuma kudinta ya kai kimanin Naira biliyan 13.527 tare kuma da noman rogo da ya kai kimanin tan 87,237, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 3.925, musamman domin a kara samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar. Sai dai, ta bayyana cewa; har yanzu a jihar ba a samar da wani cikakken tsari a hukumance ba, a kan tsarin na shirin na CAF wanda hakan ke haifar wa da shirin koma baya a jihar. Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a fannin bunkasa aikin noma, domin samun riba a jihar da su bayar da hadin...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wani Shirin zaman lafiya da ya hada da dakatar da kisan kiyashi a Gaza Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan duk wani mataki ko wani yunkuri da ya hada da kawo karshen yakin kisan kiyashi a Gaza, janyewar sojojin mamayar Isra’ila, shigar da kayan agajin jin kai, sakin fursunonin Falastinawa, da kuma tabbatar da dukkanin hakkokin Falasdinawa. Haka kuma ta kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan halastacciyar gwagwarmayar al’ummar Falastinu samun tabbatar da ‘yancin kai, ta yi amfani da dukkanin karfinta na diflomasiyya a cikin shekaru biyun da suka gabata, musamman...
Shugabannin Faransa, Jamus, da Biritaniya: Sun kuduri aniyar farfado da tattaunawa da Iran Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya sun bayyana aniyarsu ta farfado da shawarwari da Iran da Amurka dangane da shirin makamashin nukiliyar Iran da nufin cimma cikakkiyar yarjejeniya mai dorewa. A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, kasashen uku sun yi la’akari da Shirin kunna yarjejeniyar fahimtar juna. A baya dai Faransa da Birtaniya da Jamus sun sanar da cewa za su ci gaba da neman hanyar diflomasiyya don warware rikicin, amma Iran ta tabbatar da cewa ba ta son ci gaba da tattaunawa a halin yanzu idan dai har za a kakaba mata takunkumi. A gefe guda kuma shugabannin kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus sun...
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Doguwa. Hukumar ta miƙa su ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu. ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno Kwamandan hukumar na Jihar Kano, Bala Bawa Bodinga ne, ya bayyana hakan yayin da yake magana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar a ranar Juma’a. Ya ce an kama mutanen ne da sanyin safiyar ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihin bayaai. Jami’an hukumar daga...
“Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki. “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi. Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya. Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, a gefen wani taro a kasar Tajakisatan da yake halatta a kasar ya bayyana ce firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya fada masa cewa ya isar da sakonsa ga gwamnatin JMI kan cewa yana son a warware matsalolin da ke tsakaninsa da JMI cikin lumana ba tare da tashin hankali ba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana shugaba shugaban yana son yazama mai tsaga tsakani a rikicin da JMI take yi da HKI da kuma hukumar maikula da makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA, a dai dai lokacinda yake kiyaye dangantakarsa ta diblomasiyya da kasashen biyu. Putin ya kara da cewa ya sami sakonni daga HKI kan cewa mu fadawa Tehran HKI...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi October 10, 2025 Tattalin Arziki Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama October 3, 2025 Tattalin Arziki Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho October 3, 2025
A yayin da ake yawan samun ɓarnar dorinar ruwa a garuruwan Daɗin Kowa da Kupto da Malleri da Wade a yankunan Ƙananan hukumomin Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe ta kai ga samun asarar amfanin gona da rayuka. Hakan ne ya sa Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Yamaltu/ Deba a Jihar Gombe Inuwa Garba ya gabatar da ƙudiri a gaban zauren Majalisar Wakilai ta tarayya domin neman ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarnar dorinar ruwa. ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya Inda ya ce dorinar na yi wa manoma ɓarna sosai da ke janyo asarar rayuka, dukiyoyi da lalacewar...
Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na...
Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Gaza Mohammad Al-Moughayyir, ya ce sojojin Isra’ila sun janye daga yankuna da dama a cikin birnin Gaza da arewacin zirin da kuma wasu yankunan kudancin yankin. A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, Motocin Isra’ila sun janye daga kudancin birnin da tsakiyar birnin zuwa yankunan gabashi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...
Ministan albarkatun mai na Jamhuriyar Nijar Sahabi Oumarou, ya gana da Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijar. A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan muhimamn batutuwa da suka shafi alakoki da ke tsakanin kasashe biyu da kuma yadda za a kara inganta su. Sannan kuma sun yi musayar ra’ayi kan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fuskar cin moriyar juna. Jamhriyar Nijar da Iran suna da kyakkawar alaka ta diflomasiyya, kamar yadda kuma suna yarjeniyoyi da dama da ayyukan hadin gwiwa a fagage daban-daban na diflomasiyya, cinikayya da bunkasa harkoki tattalin arziki da kimiyya da fasaha. Bangarorin biyu sun jaddada wajabcin ci gaba da tuntubar juna domin aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyi da aka rattaba hannu a kansu a...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kwato makamai da kudade daga hannunsu. Daga cikin abubuwan da aka samu nasarar kwatowar har da bindigogi na gida guda huɗu, makamai masu hatsari da kuma tsabar kuɗi Naira 546,000 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansa. Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC An kama waɗanda ake zargin ne a cikin jerin samame da aka gudanar daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, a sassa daban-daban na jihar. Samamen ya haɗa jami’ai daga sashen ’yan sanda na Anchau, Hukumar Kula da Tsaro...
Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da tsare tsare da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a hukumance, kamar yadda ofishin Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a yau Juma’a. Wannan dai na zuwa ne bayan ci gaba da tsaikon da aka samu na tsawon kwana daya biyo bayan amincewar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu a ranar Alhamis. Duk da cewa an amince da matakin farko na yarjejeniyar, amma dai Isra’ila ba ta dakatar da hare-harenta a kan al’ummar yankin zirin Gaza, inda a cikin kasa da sa’oi 24 ta kashe Falastinawa akalla 70 da kuma jikkata wasu da dama a yankuna daban-daban na zirin Gaza. Tun da farko hukumar yada labaran Isra’ila ta bayar da...
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwar Shugaban Kasa ga mutane 175. Daga ciki har da wadanda aka yi wa afuwar bayan mutuwa ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da ɗan gwagwarmayar kwato ’yancin kan Najeriya, Herbert Macaulay. An dauki wannan mataki ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Gwamnatin Kano ta shirya ɗaurin auren ma’aurata 2,000 Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misis Anastasia...
A yayin yanke hukuncin, kotu ta bayyana cewa: “Na farko (INEC) da na biyu (Farfesa Mahmood Yakubu) an yanke musu hukuncin tura su gidan gyaran hali saboda rashin bin hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Osogbo, Jihar Osun, ta bayar a shari’a mai lamba FHC/OS/CS/194/2024 a ranar 17 ga 5 Fabrairu, 2025.” Kotu ta kuma umarci Sufeton ‘yansanda na ƙasa da ya kama Yakubu tare da tabbatar da fara shari’ar hukuncin raina kotu cikin kwanaki bakwai daga ranar da aka yanke hukuncin. Bugu da ƙari, kotu ta ci tarar INEC da Yakubu Naira 100,000 domin biyan masu shigar da ƙarar saboda raina umarnin kotu. Masu shigar da ƙarar sun haɗa da Action Alliance, Farfesa Julius Adebowale, Injiniya Olowookere Alabi, Barrista...
An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro. Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma. Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin. Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27. A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin...
Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin kudin da mai shekara 40 dan kwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya ke da shi. Ta ce yana da dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 daga kudin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari. Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da kwantiragin da ya kai dalar Amurka miliya 18. Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi. da...
Bankin Duniya ya ce har yanzu talauci na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar. A wajen ƙaddamar da rahoton ci gaban da aka samu a Abuja, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 139 ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci a shekarar 2025. Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe Ya ce duk da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ɗan bunƙasa, kuma gwamnati tana samun ƙarin kuɗaɗen shiga, yawancin jama’a har yanzu na fama da tsadar...
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar iran Mohammad Eslami da manyan jami’a daga hukumar rasatom ta hadin guiwar ayyukan makamashin nukiliya sun gana a birnin Tehran kuma sun tattauna kan yadda za su yi aiki tare a bangaren shirin ta na nukiliya na zaman lafiya, Nikolai Spassky ya kawo ziyara iran ne a birnin Tehran tun bayan ziyarar da Eslami ya kai birnin mosko a ranar 24 ga watan satumba, inda bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, na yin aiki tare wajen gina karamar tashar nukiliya iran. Haka zalika bangarorin biyu sun tattauna kan yarjejeniyar da aka kula lokacin da Eslami ya kai ziyara da ya hada da yin aiki tare a cibiyar nukiliyar iran...
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci. Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar. SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu Mai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Laraba cewa dole ne a rahoton bai duba yanayin tsarin auna talauci na duniya ba. “Duk da cewa Najeriya na daraja...
Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Sun ce za su gudanar da tattaki a cikin jami’o’i, tare da ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, sannan za su yi wa manema labarai jawabi domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu. Sun zargi gwamnati da rashin adalci wajen rabon Naira biliyan 50 na alawus-alawus, ƙin...

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025Daga Birnin SinKasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata October 7, 2025
Jaridar Daily Mail ta kasar Burtaniya ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana gargadin Amurka kan abinda ya kira, makamai masu linzami masu keta nahiyoyi wadanda JMI take ginawa barazana ce ga Amurka. Ya ce makaman suna iya isa biranen Amurka daga cikin har gidan Trump da ke ‘Mar-a-Lago’, a bakin ruwa na Palm Beach a jihar Florida. Daily mail ta nakalto Natanyahu yana fadar haka a hirar da ta hada shi da wani dan jirada mai suna Ben Shapiro. Ba tare da bada wata hujja ko dalili ba, Natanyahu ya ci gaba da cewa, makaman wadanda suke iya zuwa wurare masu nisan kilomita 800 zasu kai biranen washington da kuma NewYork har da kuma gidan shugaba Trump dake...
Alkaluman da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin wato China Railway ya gabatar, sun nuna cewa, ana sa ran jigilar fasinjoji kimanin miliyan 21 da dubu 750, ta jiragen kasa a kasar Sin a yau Laraba. Kana tun daga ranar 29 ga watan Satumban da ya gabata, wato ranar da aka kaddamar da aikin jigilar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye, a lokacin hutun bikin tunawa da kafuwar kasa da na Zhong-Qiu, zuwa jiya Talata, an riga an kwashe fasinjoji fiye da miliyan 160 ta jiragen kasa a kasar Sin.Yau ce ranar karshe a hutun na wannan karo, don haka ake sa ran ganin karuwar zirga-zirgar mutane da suke kokarin komawa gidajensu daga wuraren da suka yi bulaguro. Hakan ne...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025
ShareTweetSendShareMASU ALAKA LabaraiGwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu October 8, 2025Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Labarai‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa October 8, 2025
Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 sun tara Naira biliyan 546.71 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025. Sai dai hukumar ta ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wuta ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban. Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.25. kazalika, NERC ta ce...
Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta. Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara. ‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’ Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen. “Mun samu kiran...