Masu sharhi na wasanni sun bayyana cewa wasan na yau zai kasance mai cike da fasaha da kwarewa, musamman ganin cewa kungiyoyin biyu na da ‘yan wasa matasa masu zafin guiwa kamar Vinicius Jr., Jude Bellingham, da Lamine Yamal, wadanda ke son rubuta sunayensu cikin jerin manyan taurarin da suka taba buga El Classico.

Dukkan idanu yanzu sun karkata zuwa Madrid, inda ake jiran ganin wanda zai yi nasara a wannan karon.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu October 25, 2025 Wasanni Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle October 25, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Dalilin yawaitar juyin mulki a Afirka ta Yamma

Masana harkokin siyasa, jakadu da ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana cewa rashin shugabanci nagari da son mulki na dogon lokaci su ne manyan dalilan da ke haddasa yawaitar juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma.

Wannan na zuwa ne bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, wanda ya jefa ƙasar cikin rudani.

Gwamnatin Benin ta ce ta shawo kan lamarin bayan wasu sojoji sun bayyana a talabijin na ƙasar cewa sun kifar da Shugaba Patrice Talon. Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan juyin mulki a ƙasar Guinea-Bissau.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da kama sojoji kusan 12, ciki har da shugabannin yunƙurin da bai yi nasara ba. Talon, tsohon ɗan kasuwa mai shekaru 67, na shirin miƙa mulki a watan Afrilu mai zuwa bayan shekaru 10 a kan karagar mulki da ake ganin ya kawo ci gaban tattalin arziki da kuma ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi.

Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin Yadda muka daƙile yunƙurin juyin mulki a Benin — Sojin Saman Najeriya

Sojojin da suka kira kansu Kwamitin Soja na Sake Tsarawa (CMR) sun bayyana a talabijin cewa sun yanke hukuncin cire Talon daga mulki.

Sai dai daga baya fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Talon yana cikin koshin lafiya, ya ƙ bayyana masu yunƙurin a matsayin “ƙananan mutane da suka mamaye talabijin kawai.”

Ra’ayin masana

Jakadan Najeriya a ƙasashen yankin, Ambasada Suleiman Ɗahiru, ya ce juyin mulki na yawaita ne saboda raunin dimokuradiyya da kuma rashin nagartar shugabanci.

“Dimokuradiyya ba ta kafa tushe yadda ya kamata a Afirka ta Yamma. Shugabanni da aka zaɓa ba sa tafiyar da ƙasashensu yadda ya dace, hakan ya haifar da ƙin yarda daga jama’a,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa zaɓe ya rasa amincewa a ƙasashe da dama, inda shugabanni ke ƙin sauka daga mulki. Ya kawo misali da Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92 ya ci zaɓe, da Gambiya, inda shugabanni ke nuna rashin niyyar sauka daga mulki.

Suleiman Ɗahiru ya ce sai shugabanni sun yi mulki da gaskiya da adalci, in ba haka ba, juyin mulki zai ci gaba da dawowa.

Ƙalubalen ECOWAS

Tsohon jakadan Najeriya, M.K Ibrahim, ya bayyana cewa yawaitar juyin mulki babban koma baya ne ga yankin da kuma ƙungiyar ECOWAS.

Ya ce tun bayan kafa ECOWAS a 1975, an samu aƙalla juyin mulki 45 a yankin, sai dai tsakanin 2000 zuwa 2008 ne kawai aka samu zaman lafiya ba tare da juyin mulki ba.

Ibrahim ya ce yunƙurin da bai yi nasara ba a Benin ya sake bayyana raunin dimokuradiyya a yankin. Yanzu ƙasashe huɗu na ECOWAS ke ƙarƙashin mulkin soja, kuma idan Benin ta faɗi, da za a ce sun zama biyar.

Ya ce Najeriya na da nauyi na musamman wajen tabbatar da ci gaba da rayuwar ECOWAS, duk da matsalolinta na siyasa da tattalin arziki.

Ra’ayoyi kan matakan ECOWAS

Ibrahim ya bayyana cewa akwai ra’ayoyi biyu a cikin ƙungiyar:
– Wasu na ganin dole a tsaya kan ka’idojin dimokuraɗiyyar da nagartar shugabanci, ko da hakan zai sa ƙasashe su fice daga ECOWAS.
– Wasu kuma na ganin ka’idojin sun yi tsauri, suna ba da shawarar tattaunawa maimakon fitar da ƙasa nan take.

Sai dai Ibrahim ya bayyana matsayinsa: “ECOWAS ba za ta ci gaba ba ta hanyar juyin mulki. Dimokuraɗiyya da nagartar shugabanci ne kawai za su tabbatar da haɗin kai da ci gaba.”

Dalilan yawaitar juyin mulki

Ya ce raunin dimokuraɗiyyar, talauci, rashin tsaro da matsalolin Sahel na daga cikin manyan dalilan da ke sa jama’a su rungumi alkawarin sojoji duk da rashin tabbas.“Ba za a iya cewa akwai wata ƙasa a Afirka da ta tsallake barazanar juyin mulki ba,” in ji shi.

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Joshua Odeyemi, Baba Martins, Dalhatu Liman (Abuja) & Salim Umar Ibrahim (Kano)

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky
  • Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025
  • Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago
  • Saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya soya qwaqwalwarta 
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Jamhuriyar Benin – Soyinka
  • Trump Ya Yi Gefe Da Kasashen Turai Dangane Da Tattaunawa Kan Rikicin Ukraine
  • ASUU-SSU Ta Zargi VC Da KaryDokokin Jami’ar Jihar Sakkwato
  • An kama tsohon fursuna ya je fashi da bindiga AK-47
  • Dalilin yawaitar juyin mulki a Afirka ta Yamma