Aminiya:
2025-10-24@18:23:25 GMT

Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike

Published: 24th, October 2025 GMT

Ministan Babban Birnin Tarayya , Nyesom Wike, ya yi gargadin cewa irin yadda gwamnonin jam’iyyar PDP ke tafiyar da al’amuranta a yanzu, zai iya sanadin rushewar jam’iyyar.

Wike, ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Abuja ranar Juma’a, inda ya zargi gwamnonin PDP da gaza magance rikicin jam’iyyar yadda ya kamata.

An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai
Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027

Rahotanni sun nuna cewa akwai rashin jituwa tsakanin Wike da gwamnonin PDP.

Jam’iyyar na shirin gudanar da babban taronta na kasa a watan Nuwamba a birnin Ibadanna  Jihar Oyo, amma wasu rahotanni na cewar magoya bayan Wike na ƙoƙarin hana gudanar da taron.

A kwanakin baya, Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Samuel Anyanwu, ya zargi Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar naKasa (NWC) da yin amfani da sa hannunsa na bogi wajen aike wa INEc wasiƙa don sanar da shirin gudanar da taron.

Sai dai wasu shugabannin jam’iyyar sun ce Anyanwu yana aiki ne bisa umarnin Wike.

A yayin tattaunawar da ya yi da ’yan jarida, Wike ya ce: “Ban faɗa tun farko cewa tarkon da kuke saka wa kanku zai kama ku ba? Na faɗa tun da wuri, irin yadda waɗannan gwamnonin ke tafiyar da jam’iyyar, za su kashe ta ne.

“Kuna gudanar da taron jam’iyya, kuna kiran mutane manyan jam’iyya, amma kun bar ni saboda ba gwamna ba ne, ta yaya za ku ci gaba a haka?”

Wike ya kuma nesanta kansa daga masu goyon bayan tsohon Ministan Harkoki na Musamman, Tanimu Turaki, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

“Ban san wani abu game da Tanimu Turaki kan zama shugaban jam’iyya ba. Wataƙila zai zama shugaban wani bangare daban ne, ba PDP dana sani ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa tun da farko ya yi hasashen wasu ’ya’yan jam’iyyar za su fice daga cikinta.

“Tun farko na faɗa cewa idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, PDP za ta rika yin asara. Ana tafiyar da abubuwa bisa kuskure, kuma yanzu kowa yana gani. Abin kunya ne,” in ji shi.

“Duk abin da na faɗa a da yanzu yana faruwa,” a cewar Wike.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamnonin PDP Siyasa zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Amurka Ya Ce: Za Su Dauki Matakin Soji Kan Kasar Venezuela Nan Gaba Kadan

Shugaban kasar Amurka Trump ya ce: Za su dauki matakin soji kan kasar Venezuela nan ba da jimawa ba

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da cewa kasarsa za ta iya fara yaki da “masu safarar miyagun kwayoyi nan ba da jimawa ba,” yana mai cewa, “Za su dauki mataki ta hanyar kutsawa ta kasa a kasar Venezuela,” yana mai nuni da yiwuwar shiga tsakani na soja ko ayyukan leken asiri.

A martanin da ya mayar, Shugaba Trump daga baya ya musanta rahotannin cewa: Jiragen yakin Amurka sun yi shawagi a kusa da kan iyakar Venezuela, yana mai jaddada cewa: “Ba gaskiya ba ne cewa: Amurka ta aika da jiragen yakin sama kusa da Venezuela.”

Trump ya shaida wa manema labarai a Fadar White House cewa: “Rahotanni daga kafofin watsa labarai game da aika jiragen yakin sama na B-1 zuwa kan iyakar Venezuela ba su dace da gaskiya ba.”

Trump ya kara da cewa: Gwamnatinsa ba za ta nemi Majalisar Dokoki ta “yi shelar yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ba; za su kashe su kawai.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Iraki Ta Yi Allah Wadai Da Mamaye Yankin Yammacin Kogin Jordan Na Falasdinu October 24, 2025 ‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu October 24, 2025  Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada October 24, 2025 Gaza: Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani  Zai Ci Gaba  Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko  yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ayatullahi Khatami Ya Ce: Shugaban Amurka Dan Ta’adda Ne                                                                               
  • Shugaban Amurka Ya Ce: Za Su Dauki Matakin Soji Kan Kasar Venezuela Nan Gaba Kadan
  • Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027
  • Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC
  • Babban Lauyan Jihar Kwara Ya Tabbatar da Gudanar da Adalci da Kare Hakkokin Mace
  • Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio
  • Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a fashewar tanka a Neja
  • Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II
  • Labarin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ƙarya ne – Sarkin Musulmi