Aminiya:
2025-10-27@13:55:37 GMT

Sule Lamiɗo na neman takarar Shugaban PDP na Ƙasa

Published: 27th, October 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana kudirinsa na sayen tikitin neman zama sabon Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa.

Tsohon ministan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa kudurinsa na ganin an dawo da martabar dimokuraɗiyya da kuma farfaɗo da darajar jam’iyyar yadda take da, ba zai taɓa yankewa ba.

Tsohon gwamnan na Jigawa na cikin sahun farko na wadanda aka kafa jam’iyyar ta PDP da su a Nijeriya, kuma na gaba-gaba a takarar neman zama sabon shugaban jam’iyyar ta PDP daga Arewa maso Yamma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauke Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Babban Hafsan Tsaron Kasa.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sunday Dare, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, ya fitar a ranar Jumma’a.

An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike

A cewar sanarwar, an nada Janar Olufemi Oluyede, wanda shi ne Shugaban Sojin Ƙasa, a matsayin Sabon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa.

An kuma naɗa Manjo Janar W. Shaibu a matsayin Shugaban Sojin Ƙasa, Air Vice Marshal S.K. Aneke a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Sama, da Rear Admiral I. Abbas a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Ruwa.

Manjo Janar E.A.P. Undiendeye, wanda shi ne Shugaban Sashen Leken Asirin Tsaro (Defence Intelligence), zai ci gaba da rike mukaminsa.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan sauyi na cikin shirin gwamnati na inganta tsaron a Najeriya.

Shugaba Tinubu, ya gode wa tsohon Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, da sauran tsoffin hafsoshi bisa gudunmawa da jagorancin da suka yi.

Ya kuma bukaci sabbin hafsoshin da su nuna ƙwarewa, jajircewa, da haɗin kai domin inganta tsaro a Najeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa
  • Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL
  • Farfesa Muhammed Khalid Othman Ya Zama Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Ta Dutsinma
  • Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Dakarun IRGC Ya Ce: Yakin Kwanaki 12 Kan Iran Ya Canza Tunanin Makiya
  • Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri
  • Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya dalilin sauya hafsoshin tsaro — ADC
  • Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi
  • Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu
  • Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike