Gaza Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Akan Yara Da Matan Har Zuriya Mai Zuwa
Published: 24th, October 2025 GMT
MDD ta bayyana cewa a tsakanin kowadanne mutanen Gaza 4, daya daga cikinsu yana fama da yunwa.
Mai Magana da yawun kungiyar Agaji ta tarayyar turai, May Musa Sayegh, ta yi ta’aliki akan wannan adadin na masu fama da yunwa a Gaza, inda ta ce; Wannan shi ne hakikanin abinda yake faruwa a kasa, kuma ya shafi mata manya da ‘yan mata da kuma kananan yara masu yawa.
May Musa Sayegh ta fada wa tashar talabijin din aljazira cewa; Sakamakon hare-hare na tsawon shekaru biyu da kuma rashin samun damar shigar da kayan agaji,musamman a arewacin Gaza aka fada cikin wannan halin.
Sayegh ta kuma ce; ta fuskar kiwon lafiya, al’amurra suna kara tabarbarewa, domin mutane suna rayuwa cikin bakin talauci, ga shi kuma ba a kai musu kayan agaji mafi karanci na bukatun yau da kullum.
Haka nan kuma ta yi ishara da yadda cutuka suke yaduwa saboda karancin ruwa da kuma rashin magani, da hakan yake haddasa asarar rayukan mata masu ciki da kuma kananan yara.
Bugu da kari,Sayegh ta ce idan har ba a shigar da taimako cikin yankin da gaggawa ba, kuma ya zama da yawa wanda zai ishi mutane, to wannan matsalar za ta ci gaba da wanzuwa.
A ranar 10 ga watan Oktoba ne aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce a kowace rana HKI take karyawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Lashe Kambun Duniya Na Kokawar Gargajiya October 24, 2025 Pezeshkian: Iran za ta gwammace takunkumi a kan mika wuya October 24, 2025 Trump: Amurka na shirin kai hare-hare a Venezuela October 24, 2025 Ivory Coast: Ayyukan ma’adinai na fuskantar tsaiko yayin da Ouattara ke neman wa’adi na 4 October 24, 2025 Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi October 24, 2025 Larabawan Yankin Tekun Fasha Sun Caccaki Sabon Shirin Isra’ila A Kan Yammacin Kogin Jordan October 24, 2025 Albanese: Wajibi Ne A Kawo Karshen Gwamnatin Mamaya A Falasdinu October 23, 2025 Rasha: Shugaba Putin Ya Duba Atisayen Rundunar Nukiliyar Kasar October 23, 2025 Shugaban Amurka Ya Soke Shirin Ganawa Da Takwaransa Na Rasha October 23, 2025 Venezuela Ta Sanar Da Mallakar Makamai Masu Linzami Samfurin “ Igla-s” 5,000 Domin Kare Kanta October 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MِِِِDD: Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya
Wakiliyar musamman ta majalisar dinkin duniya kan yankin falasdinu da aka mamaye Francesca Albanese ya bayyana irin halin da ake ciki a yankunan falasdinu da isra’ila ta mamaye a matsayin babban bala’I, ta ce kuma shi ne kisan kare dangi na farko da ya tada hankali duniya sosai.
Da take bayani wajen rufe taron da aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a jiya lahadi ta bayyana cewa kusan komai ya lalace a yankin, wanda hakan ke nuna kusan rushewar harkokin siyasa da tarbiyar alumma,
Wannan ba shi ne kisan kare dangi na farko a tarihin dan Adam ba, wannan shi ne kusan karo na 3 na kisan kare dangi idan bai zama na 4 ko na 5 ba da ya faru a tsawon rayuwata, amma wannan shi ne kisan kare dangi da ya farkar da alummar duniya kuma ta mayar da martani akai, falasdinawa sun bamu damar mu ga yadda doka take a hannu masu karfi.
Babbar kotun duniya mai hukumta laifukan yaki tuni ta riga ta bayyana a fili cewa Isra’ila ta kawo karshen mamaya, kuma ta janye sojojinta ta kuma rusa matsugunnan yahudawa yan share wuri zauna, da kuma dakatar da lalalata muhimmman gine-gine na falasdinawa, wannan shi ne Adalcin da ake bukata .
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Duk Wani Rikici December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025 Macron Na Faransa Ya Yi Wa Najeriya Alkawalin Taimakawa Akan Matsalolin Tsaro December 8, 2025 Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka Teke Fuskanta December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci