El-Clasico: Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2
Published: 26th, October 2025 GMT
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta doke babbar abokiya hamayyarta, Barcelona da ci 2 da 1 a filin wasa na Bernabeau.
Wasan tsakanin manyan ƙungiyoyin biyu shi ne wasa mafi girma na hamayya a duniya.
Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a KanoMadrid ta karɓi baƙuncin Barcelona a gasar Laliga a wasan mako na 10.
Wasan ya ƙayatar, inda kowace ƙungiya ta nuna bajinta tare da murza leda yadda ya kamata.
Ɗan wasan gaban Real Madrid, Kylian Mbappe ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 22, yayin da Fermin Lopez ya warware wa Barcelona a minti na 38.
Kafin tafiya hutun rabin lokaci, ɗan wasan tsakiyar Real Madrid, Jude Bellingham, ya sake jefa mata ƙwallo ta biyu a raga, a minti na 43.
Yanzu haka Madrid na ci gaba da jan ragamar teburin gasar da maki 27 daga wasanni 10, inda ta lashe wasa tara ta kuma yi rashin nasara a wasa ɗaya.
Barcelona kuwa, tana mataki na biyu da maki 22 daga wasanni 10, inda ta yi rashin nasara a wasanni biyu, tare da yin kunnen doki a wasa ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barcelona Wasan Hamayya
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin Iyakar Thailand da Cambodia Ya Tilasta wa Dubban Mutane Barin Muhallansu
Jami’ai sun ce mutane sama da dubu 500 ne kawo yanzu aka tursasawa barin muhallansu a Thailand da kuma Cambodia a yayin da rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari.
Rundunar sojin Thailand ta ce Cambodia ta harba mata dubban makaman roka tun bayan da suka soma rikici da juna.
Dubban mutane ne suke guduwa domin tserewa lugudan makaman roka da ake harbawa daga Cambodia.
Kazalika Thailand ma na ci gaba da kai wa Cambodia hare-hare ta sama.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana kyautata tsammanin zai gana da shugabannin kasashen biyu ta wayar tarho, wanda ya matsa musu lamba aka cimma kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yulin da ya gabata.
To sai dai ministan harkokin wajen Thailand ya gargadi Amurka akan amfani da wata barazana ko haraji domin tursasa komawa teburin sulhu don cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
bbc