Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL
Published: 26th, October 2025 GMT
Aikin, wanda ke wakiltar tashar fitar da ɗanyen fetur ta farko da kamfanin Afirka mai zaman kansa ya bunƙasa a ƙasar, yana nuna babban jarin da ya wuce dala miliyan 400 a matakin farko, inda ake sa ran kuɗin zai ci gaba da bunƙasa har ya haura dala biliyan 1.3.
GEIL, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Anthony Olusegun Adegbulugbe, wani sanannen malami kuma ƙwararren masani a fannin tsare-tsaren makamashi, yana da ƙwarewa mai sosai a tsawon shekaru masu yawa.
Farfesa Adegbulugbe ya kasancewa yana riƙa muƙami biyu na shugaban kwamitin gudanarwa da kuma shugaban Kamfanin Green Energy International, yana kawo haɗin kai na ilimi da jagorancin masana’antu na ainihi. Dogon tarihinsa na ba da gudummawa ga manufofin makamashi da kuma fafutuka don magance matsalolin makamashi na cikin gida ya bayyana a cikin ayyukan kamfanin GEIL, wanda ya haɗa da tashar wutar lantarki mai ƙarfin 20MW (za a iya faɗaɗa zuwa 40MW) da tashar iskar gas mai nauyin 12 miliyan ta Otakikpo Midstream Ltd (FOML), waɗanda ke ƙara inganta harkokin makamashi a Nijeriya.
An yaba wa ƙwararrun ma’aikatan kamfanin GEIL na gida da haɗin gwiwarsu da hukumomin da ke kula da doka saboda saurin aiwatarwa da nasara na wannan babban aikin ingantaccen tsarin ƙasa da ƙasa.
Bisa ga wannan nasara, kamfanin Green Energy International Limited ya kasance a matsayin jagora a fannin makamashi na Nijeriya, yana nuna ƙarfin ƙasa wajen bayar da kayan aikin fitar mai na gida masu tasiri sosai. Tashar Otakikpo ta tsaya a matsayin shaida ga ƙudirin Nijeriya na faɗaɗa kayan aikin makamashi, zurfafa kuɗaɗe shiga da kuma ƙarfafa tsaron makamashi na ƙasa, wanda ya sanya GEIL ya dace da samun yabo a matsayin gwarzon kamfann bunƙasa abubuwan gida a masana’antar mai da gas.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, ya rantsar da Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN), a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) na shida da aka tabbatar da shi.
An gudanar da wannan gajeren bikin rantsarwa ne a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas? An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a FilatoBayan rantsarwar, Shugaba Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC da ya yi aiki da gaskiya da amana, ba tare da wata matsala ba.
“Naɗa ka da kuma tabbatar da kai da Majalisar Dattawa ta yi, alama ce ta ƙwarewarka da amincewar da bangarorin zartaswa da na dokoki suka nuna gare ka.
“Wannan babbar nasara alama ce ta fara tafiya mai ƙalubale amma mai albarka, kuma ina da tabbacin za ka ɗauki wannan nauyi da cikakkiyar gaskiya, sadaukarwa da ƙaunar ƙasa,” in ji Shugaba Tinubu.
Shugaban ƙasa ya bayyana cewa Najeriya ta fara tafarkin dimokuraɗiyya tun daga 1999, tare da ci gaba mai ma’ana wajen ƙarfafa hukumomi da tsare-tsare, inda ya ce: “Dimokuraɗiyyar mu ta yi nisa cikin shekaru 25. Mun ƙarfafa hukumomin dimokuraɗiyya, musamman tsarin zabe, ta hanyar kirkire-kirkire da gyare-gyare.
“Muna ci gaba da koyon darussa, kuma mun inganta sosai fiye da yadda muke shekaru da suka wuce. Yanzu dole ne mu ci gaba da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya a cikin al’umma mai rikitarwa da sassa da dama.
“Tsarin zabe muhimmin ɓangare ne na dimokuraɗiyya wanda ke ba jama’a damar zaɓar shugabanninsu da tsara makomarsu. Don tabbatar da ci gaban dimokuraɗiyya, dole ne a tabbatar da ingancin tsarin zabe,” in ji shugaban.
Tinubu ya ce zaben gwamna da za a gudanar a Jihar Anambra a ranar 8 ga Nuwamba, 2025, zai zama zakaran gwajin dafin jagorancin sabuwar hukumar zabe.
“Yana da matuƙar muhimmanci a tabbatar da cewa zabukanmu suna da kyau, adalci da inganci. Dole ne mu ci gaba da inganta tsarin zabe, mu magance matsalolin da suka gabata, mu kuma kawo sabbin hanyoyi don yau da gobe.
“Babu tsarin zaben da ba shi da matsala, amma tun da zabe muhimmin ginshiƙi ne ga makomar ƙasa, dole ne a ci gaba da ƙarfafa hukumomin zabe, a tabbatar da cewa suna da ƙarfi, juriya, kuma an kare su daga matsalolin da za a iya kauce wa.
“Saboda haka, ina ba ka umarni, Farfesa Amupitan, yayin da ka ɗauki wannan nauyi mai muhimmanci, da ka kare ingancin tsarin zabukanmu, da kuma ƙarfafa ƙarfin hukumar INEC.”
Bikin rantsarwa ya biyo bayan tabbatar da naɗa Amupitan da majalisar dattawa ta yi a ranar 16 ga Oktoba.
Amupitan ya gaji Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci INEC daga 2015 zuwa 2025.
Da yake jawabi ga ’yan jarida bayan bikin, sabon shugaban na INEC ya yi alkawarin kare kundin tsarin mulki da dokokin Najeriya dangane da tsarin zabe.
Ya kuma yi alkawarin yin aiki tare da masu ruwa da tsaki don nasarar zabe a ƙasa.
Ya ce, “Zan kare kundin tsarin mulki da dokokin Najeriya dangane da tsarin zabe, kuma kamar yadda Shugaban Ƙasa ya ce, an ba ni umarni kai tsaye da na tabbatar da zabe mai inganci, adalci da nagarta.”