NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas?
Published: 24th, October 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare.
Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati.
Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da dabaru irin na soji da kuma kayan yaki na zamani. Wannan lamari ya jawo tambaya daga al’umma: shin wannan karin hare-hare alama ce ta dawowar kungiyar Boko Haram da ISWAP ne, ko kuma rashin isassun kayan aiki da dabarun soji ne ke jawo hakan?
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su.
A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada cewa gudanar da PoS ba tare da rajista ba ya saɓa wa Dokar Kamfanoni ta 2020 da kuma ka’idojin Babban Bankin Najeriya (CBN).
Hukumar ta kuma zargi wasu kamfanonin fasahar kudi (fintech) da daukar wakilai ba tare da rajista ba, tana bayyana wannan dabi’a a matsayin da sakaci kulawa da kuma barazana ga daidaiton tsarin kuɗi na ƙasar.
Ta ce hakan na jefa miliyoyin ’yan Najeriya, ciki har da ’yan kasuwa ƙanana da masu aiki a karkara, cikin haɗarin tattalin arziki da asarar jari.
Ɗa da mahaifi sun mutu a cikin rijiya a Kano Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi“Duk fintech da ke ba da damar ayyukan da ba bisa ƙa’ida ba za a saka su cikin jerin waɗanda ake sa wa ido, sannan za a kai rahotonsu ga CBN. Duk masu PoS an umurce su da su yi rajista nan da nan. Bin doka wajibi ne.
“Daga ranar 1 ga Janairu, 2026, ba wani mai PoS da zai ci gaba da aiki a Najeriya ba tare da cikakken rajista ba,” in ji CAC.
Wannan daiba shi ne karo na farko da aka yi kira kan buƙatar tsaurara dokokin sa ido kan harkar PoS ba.
An sha yin kira ga CBN da ya ɗauki matakan gaggawa wajen daƙile yawaitar damfara da ke addabar harkar PoS a faɗin ƙasar.