An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a Kano
Published: 26th, October 2025 GMT
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutum 25 da ake zargi da shirya auren jinsi a samamen da ta kai wani wurin shagali a jihar.
A cewar hukumar, an kama mutanen ne da yammacin Asabar a wani wurin taro da ke kan titin Hotoro Bypass a ƙaramar hukumar Tarauni.
Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno NSCDC ta yi alhinin mutuwar Kwamishinan Tsaron GombeMataimakin Kwamanda Janar na Hukumar Hisbah mai kula da ayyuka na musamman, Sheikh Dokta Mujahid Aminuddeen Abubakar, ne ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa samamen na zuwa ne bayan bayanan sirri da hukumar ta samu daga wani mai kishin al’umma.
Ya bayyana cewa bayanan sirrin sun nuna cewa wani mai suna Abubakar Idris yana shirin auren wani matashi, lamarin da ya sa jami’an Hisbah suka bazama zuwa wurin da taron ke gudana.
Ya ƙara da cewa daga cikin wadanda aka kama akwai maza 18 da aka bayyana a matsayin ’yan daudu, da kuma mata 7 daga unguwanni daban-daban ciki har da Sheka, Yar Gaya da Kofar Nasarawa.
Dokta Mujahid ya ce a halin yanzu duk ababen zargin suna hannun hukumar, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Ya yi kira ga iyaye da su kula wajen inganta tarbiyyar ’ya’yansu, tare da roƙon jama’a da su rika sanar da hukumar Hisbah ko hukumomin tsaro idan sun ga wani abin da ke da ɗaukar hankali.
Mataimakin kwamandan ya sake jaddada ƙudirin hukumar na ci gaba da tabbatar da ɗabi’a ta gari da kare mutuncin Kano a matsayin jihar da aka sani kan ginshiƙin ladabi da ƙa’idojin addinin Musulunci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
Zanga-zanga ta ɓarke a yankin Numan da ke Jihar Adamawa, kan zargin sojoji da kashe wasu mata a garin Lamurde.
Mata sun fito zanga-zangar ne sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin kabilu Bachama da Chobo.
An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello TurjiA lokacin zanga-zangar an ruwaito cewar mata bakwai ne suka mutu sannan wasu 11 suka jikkata.
Shaidu sun ce sojoji sun buɗe musu wuta yayin da suke tare hanya, suna zargin rundunar da goyon bayan wata ƙabila.
Sai dai rundunar Sojin Najeriya ta musanta wannan zargi.
Ta ce dakarun sun yi artabu ne da wasu ‘yan bindiga a yankin, kuma ta ce mutuwar wasu mata biyu ya faru ne sakamakon buɗe wuta da ‘yan bindigar suka yi, ba wai sojoji suka harbe su ba.
Gwamnatin Jihar Adamawa, ta ayyana dokar hana fita na awa 24 a Lamurde domin daidaita al’amura da zaman lafiya.
A Numan, matan da suka sanya riga ɗauke da launin baƙi ne suka fara zanga-zangar a manyan tituna, inda suke neman yi wa waɗanda aka kashe adalci.
An riga an binne wasu daga cikin waɗanda suka rasu, lamarin da ya ƙara haifar da damuwa a tsakanin al’ummar yankin.
Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin, Kwamoti Laori, ya yi Allah-wadai da kisan, inda ya ce ya kamata a gudanar da bincike mai zurfi.
Ya buƙaci hukumomin tsaro da su ɗauki matakin da ya dace, tare da tabbatar da zaman lafiya ba tare da tauye haƙƙin ɗan Adam ba.
Mazauna yankin sun ce rigimar ta jefa mutane cikin tsoro, wanda hakan ya sa da dama suka tsare daga gidajensu.
Shugabannin al’umma a yankin, sun yi kira da a yi sulhu domin kaucewa ƙarin tashin hankali.