Matasa Dubu Ɗaya Za Su Samu Horon Fasahar Zamani A Nasarawa — Remi Tinubu
Published: 24th, October 2025 GMT
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa matasa dubu ɗaya (1,000) za su samu horo kan tsaron yanar gizo (cyber security) da fasahar binciken dijital (digital forensics) ta hanyar Cibiyoyin Koyon Fasahar Dijital ƙarƙashin Shirin Renewed Hope Initiative (RHI) a Jihar Nasarawa.
Uwargidan Shugaban Ƙasan ta bayyana haka ne yayin bikin kaddamarwa da miƙa Cibiyar Koyon Fasahar Dijital (Digital Learning Center) a Lafia da wasu jihohin ƙasar.
Sanata Oluremi Tinubu ta ce, shirin horon matasan wanda za a rika gudanarwa a kowane mako daga yanzu har zuwa watan Disamba na shekara mai zuwa, yana da nufin yakki da laifukan yanar gizo (cyber crimes) da kuma ƙarfafa matasa su samu ƙwarewa ta yadda za su dogara da kansu a rayuwa.
Uwargidan Shugaban Ƙasan ta yaba wa Daraktan Hukumar NITDA, Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, bisa ƙoƙarin gina cibiyoyi 15 na koyon fasahar dijital tare da haɗin gwiwar Renewed Hope Initiative, domin bunƙasa damar samun ilimi ta fasahar zamani a ƙasar.
A nasa jawabin, Daraktan Janar na NITDA, Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, ya bayyana cewa dijitalizashan (digitalization) muhimmin ginshiƙi ne a cikin manufofin sauyin gwamnati ta yanzu, don haka aka kafa cibiyoyi 296 na koyon fasahar dijital a fadin ƙasar.
Ya ƙara da cewa a bana, NITDA tana shirin ƙara cibiyoyi 148, wanda hakan zai kai adadin cibiyoyi zuwa 586 kafin shekarar 2027.
Shi ma Daraktan Janar na Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital ta Jihar Nasarawa (NASITDA), Sani Haruna Sani, ya bayyana cewa wannan cibiya za ta zama hedikwatar horo kan ilimin dijital, tsaron yanar gizo da kuma binciken forensics a jihar.
Ya yi kira ga matasan jihar da su amfana da wannan dama domin su ƙara kwarewa a fannin fasahar zamani, su taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin jihar da ƙasa baki ɗaya.
Aliyu Muraki, Lafia
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: nasarawa fasahar dijital
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Kwara Ta Ware Naira Biliyan 8 Don Biyan Haƙƙin Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya
Gwamnatin Jihar Kwara ta ware kimanin Naira Biliyan 8 da miliyan dari daya domin biyan haƙƙin fansho da giratuti na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka yi ritaya.
Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Dakta Hauwa Nuhu, ce ta bayyana haka a yayin taro da ma’aikatun gwamnati karo na uku, wanda aka gudanar a zauren taro na ma’aikatar kuɗi a Ilori.
A cewarta, za a raba Naira Biliyan biyar da miliyan dari shida ga tsoffin ma’aikatan jiha a matsayin giratuti, yayin da aka ware Naira Biliyan biyu da miliyan dari biyar domin tsoffin ma’aikatan kananan hukumomi.
Dakta Nuhu ta jaddada cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da biyan fansho da giratuti a hankali domin tabbatar da cewa sauran ayyukan ci gaban jama’a ba su tsaya ba.
Ta bayyana cewa adadin giratuti da fansho ya ninka saboda aiwatar da sabon tsarin albashi na Naira Dubu Talatin da Naira Dubu Saba’in, tare da daidaiton da aka yi ga masu ritaya.
Kwamishinar ta kuma tabbatar da cewa babu wani tsohon ma’aikacin karamar hukuma ddake bin gwamnati bashi, sai waɗanda suka ƙi bayyana a lokacin tantancewar da aka gudanar a dukkanin kananan hukumomi 16 na jihar.
Ali Muhammad Rabi’u