2025-10-26@21:43:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10753

«fasahar zamani na»:

    A ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1945, wato bayan da kasar Sin ta samu nasara a yakin kin harin mayakan Japan, kasar ta Sin ta karbi yankin Taiwan daga hannun Japanawa da suka yi rabin karni suna mamayar yankin, inda suke aiwatar da mulkin mallaka. Sa’an nan zuwa ranar 25 ga watan Oktoban bana, babban yankin kasar Sin ya gudanar da biki na musamman don tunawa da dawowar yankin Taiwan cikin harabar kasar. Dangane da batun, dimbin kafofin watsa labaru na kasashe daban daban suna ganin cewa, bikin da aka shirya ya nuna nasarar da Sinawa suka samu a yakin duniya na biyu, kana ya shaida cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, wanda ba za a iya...
    Matatar Dangote ta sanar da shirin ƙara ƙarfin sarrafa man fetur daga ganga 650,000 zuwa miliyan 1.4 a kowace rana, wanda zai sanya ta zama babbar matatar mai mafi girma a duniya. Shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Legas, yana mai cewa faɗaɗawar na nuna ƙwarin gwuiwa ga tattalin arziƙin Nijeriya da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na mayar da ƙasar cibiyar sarrafa mai ta duniya. Dangote ya ce aikin faɗaɗawar “tana nuna amincewa da ƙarfin Afrika wajen tsara makomar makamashinta,” yana mai yabawa gwamnati bisa manufofi irin su Naira-for-Crude Policy da One-Stop Shop Initiative, waɗanda suka ƙarfafa zuba jari a ɓangaren mai. Ya kuma tabbatar da cewa matsalolin da suka...
    A baya bayan nan, kundin da aka amince da shi yayin cikakken zama na hudu na kwamitin kolin JKS na 20, ya tanadi tsare-tsaren musamman na fadada bude kofofin kasar ga sassan waje, da dora muhimmancin gaske ga samar da sabon yanayin hadin gwiwar cimma moriyar juna. A halin yanzu, a hannu guda ana ganin zurfafar sabon zagayen juyin-juya-halin fasahohi, da sauyi a ci gaban masana’antu, a gabar da duniya ke bukatar bude kofa da rarraba gajiya sama da duk wani lokaci a baya. A daya hannun kuma, tsarin daukar matakan kashin kai da kariyar cinikayya na dada kamari, kuma duniya na fuskantar yanayin rashin daidaiton ci gaba da gibi a fannin jagoranci. A wannan yanayi mai sarkakiya da duniya...
    Alhaji Aliko Dangote, na shirin faɗaɗa matatar mansa domin ta riƙa tace gangar mai miliyan 1.4 a kowace rana. A halin yanzu, matatar tana tace gangar mai 650,000 a rana, amma Dangote, ya bayyana cewa suna shirin ƙara adadin cikin shekaru uku masu zuwa. Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki El-Clasico: Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2 Ya bayyana haka ne yayin wani taro da manema labarai a ranar Lahadi, inda ya ce faɗaɗa aikin zai sa matatar ta zama mafi girma a duniya. “Wannan shiri yana nuna yadda muke da cikakken shiri a Afirka da kuma dogaro da makomar Najeriya a ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu,” in ji shi. Ya bayyana...
    Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Frank Ogunojemite, ne ya sanya rattaba hannunsa a wasiƙar kamar yadda Jaridar PUNCH, ta samu kwafinta. Shugaba ya bayyana cewa, ya kafa hujjar buƙatar soke tsarin, kan ƙalubalen da take fuskanta, na kashe kuɗaɗe masu yawa, musamman wajen safarar mayan Kwantainonin da ake shigoa da su daga ƙasashen da ke a Afirka ta Yamma Ya ce, wannan tsarin ya sanya a yanzu, ana yiwa  masu safarar kaya zuwa cikin Tashar wani sabon cajin kuɗi da kuma jinkirin da suke samu, wajen shigar da kayan zuwa cikin Tashar. Ogunojemite ya buƙaci Hukumar da ta tabbatar da wanzar da tsarin a matsayin na bai ɗaya a ɗaukacin Tashishin Jiragen Ruwan ƙasar. “Muna gabatar da wannan buƙatar ce, domin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing October 26, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai October 26, 2025 Daga Birnin Sin Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya October 26, 2025
    Ya ƙara da cewa Basira ‘Yar Guda ta bayyana cewa za ta amince da aure ne kawai idan Idris ya mallaki gidansa na kansa, ba wanda yake haya ba. Wannan ne ya sa kotu ta dakatar da yanke hukunci domin bai wa Hisbah damar tabbatar da cewa an bi tsarin aure yadda ya dace da shari’ar Musulunci. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji October 26, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu October 26, 2025 Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025
    Gyaran da aka fara ya yi daidai Nambobi suna ba da labarin wani ɓangare na labarin,  amma suna bayyana lamarin ne kawai, amma suna bayyana lamarin gaba ɗaya. A shekarar 2023, FIRS ta samu Naira Tiri liyan12.36, abinya zarce kuɗaɗen da ake tsammanin shigowa daga gare ta, har ma wuce kashi 7 na kuɗaɗen shigar da ake sa ran da ake zata kawo, hakan kuma shi yasa mafi kayu ɗin kuɗaɗen shigar da aka samu a tarihin tara kuɗaɗen haraji. A shekarar 2024, an kuɗaɗen shigar suka ƙaru da—Naira Titiliyan 21.7, ba kamar na shekarar 2023 ba , inda aka nsamu Naira Tiriliyan19.7. Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar Gwamnan Bauchi...
    Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin tafiya kasar Koriya ta Kudu, domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabanni karo na 32, na kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar, an gudanar da wani taron tattaunawa, mai taken “Shugabancin duniya da samun wadata tare a yankin Asiya da Pasifik” a nan birnin Beijing, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da jami’ar Yonsei  da gidan talabijin na YTN na Koriya ta Kudu suka shirya tare.   Yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce “CMG na fatan yin hadin gwiwa mai zurfi tare da kasashen yankin...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta doke babbar abokiya hamayyarta, Barcelona da ci 2 da 1 a filin wasa na Bernabeau. Wasan tsakanin manyan ƙungiyoyin biyu shi ne wasa mafi girma na hamayya a duniya. Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a Kano Madrid ta karɓi baƙuncin Barcelona a gasar Laliga a wasan mako na 10. Wasan ya ƙayatar, inda kowace ƙungiya ta nuna bajinta tare da murza leda yadda ya kamata. Ɗan wasan gaban Real Madrid, Kylian Mbappe ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 22, yayin da Fermin Lopez ya warware wa Barcelona a minti na 38. Kafin tafiya hutun rabin lokaci, ɗan...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunwa ta diflomasiyya da Amurka domin cimma “mafita kan batun nukiliya cikin mutunta juna. “Iran ta sha sanar da cewa ba ta taba yin watsi da diflomasiyya ba kuma,” in ji Araghchi a wata hira da akayi da shi. “Ba za mu yi sulhu kan abinda ya kasance hakkin mutanen Iran ba kuma ba za mu lamunci mamaye da cin zarafi a kan mutanen Iran ba; duk da haka, a shirye muke mu fuskanci kowace mafita mai hikima,” in ji Araghchi. Ya sake nanata cewa Iran ba ta bukatar makamin nukiliya. Ya ce Tehran ta shiga tattaunawa da Washington game da shirin makamashin nukiliyarta don ba...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya October 26, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan October 25, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur October 25, 2025
    A Jamhuriyar Kamaru a gobe Litini aka tsara  sanar da sakamakon babban zaben shugaban kasar da akayi a ranar Lahadi 12 ga wata. Saidai rahotonnin sun ce an shiga zaman dar-dar a sassa daban daban gabanin sanar da sakamakon zaben. Tuni gwamnatin Amurka ta shawarci yan kasarta da ke Kamaru da su yi taka-tsantsan tare da sa ido kan abubuwan da ke faruwa. Tunda farko Ministan harkokin cikin gidan Kamaru, Paul Atanga Nji ya zargi jam’iyyun hamayya na kasar da yunkurin tayar da hargitsi a daidai lokacin da ake jiran sanar da sakamako zaben a hukumance. Wannan na zuwa ne bayan ƴan sandan kasar sun kama wasu fitattun ƴan siyasa masu alaka da babban abokin karawar Paul Biya, wato Issa...
    A birnin Paris, an gudanar da wata zanga-zanga a filin jirgin saman Roissy-Charles-de-Gaulle game da shigar da makamai da kayan aikin soja na Faransa zuwa Isra’ila. An shirya zanga-zangar ne bisa kiran wasu kungiyoyi da nufin bayyana rawar da Faransa ke takawa wajen samar wa sojojin Isra’ila makamai da kayan soji, musamman ta babban filin jirgin saman kasa da kasa na Roissy-Charles-de-Gaulle. A cikin sanarwar manema labarai, da suka fitar masu shirya zanga zangar sun yi Allah wadai da jigilar kayan aikin sojan inda suka nemi a dakatar da duk kayan da Faransa ke fitarwa wadanda za su iya taimakawa wajen kai hare-haren sojojin Isra’ila. Wannan yunkurin ya zo ne bayan da gidan yanar gizon bincike na Faransa mai suna...
    Kungiyar gwagwamaryar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa ba za ta bari Isra’ila ta samu wata hujja ta ci gaba da yaki a Gaza ba. Khalil al-Hayyah jigo a kungiyar ta Hamas, ya nuna gazawar gwamnatin Isra’ila na cimma burinta a Gaza kuma ya bayyana cewa kungiyar tana mutunta dukkan alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ba kuma ba za ta bari makiya su sami hujjar ci gaba da yakin ba. al-Hayyah, shugaban ofishin siyasa na Hamas a Gaza, ya bayyana a wata hira da tashar Al Jazeera cewa gwamnatin Isra’ila ta gaza cimma duk wani burinta a lokacin yakin kuma Hamas za ta yi duk mai yiwuwa don hana sake barkewar yaki. Da...
    A Ivory Coastana ci gaba da kirga kuri’u bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya Asabar. An kira sama da masu jefa kuri’a miliyan 8 zuwa rumfunan zabe a rumfunan zabe sama da 25,000 a fadin kasar. A kasar da ta fuskanci mummunan yakin basasa, zaman lafiya yana daya daga cikin manyan abubuwan da jama’a ke fata. ‘Yan takara biyar ne suka fafata a wannan zaben, ciki har da Alassane Ouattara, mai shekara 83 wanda ke neman wa’adi na hudu. Duk da cewa an cire shugabannin ‘yan adawa daga zaben, masu lura da al’amura sun yi imanin cewa shugaban da ke kan mulki ba tantama zai iya lashe zaben. A ranar Asabar da yamma, shugaban hukumar zaben kasar...
    Sai dai ya yabawa masu ba da agajin gaggawa, da jami’an tsaro da kuma ‘yan sa-kai da suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da ba su agaji, yana mai cewa ɗaukin gaggawan da suka kai ya taimaka wajen rage munin ibtila’in. A yayin da take addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, ƙungiyar Gwamnonin Arewan ta bada tabbacin cewa za ta ci gaba da haɗa hannu da hukumomin tarayya dana jihohin da abin ya shafa don ƙarfafa tsarin rigakafi da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma.   ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin...
    A kwanan nan, wata manufa da aka zartas a yayin wani taron kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta janyo hankalin al’ummun duniya, wato yadda kasar Sin take neman gaggauta dogaro da kai wajen kirkiro sabbin fasahohi, da zama mai jagorantar ci gaban masana’antun zamani a duniya. Inda dimbin kafofin yada labaru na kasashe daban daban ke ganin cewa, manufar ta nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora a bangaren raya kasa ta wata ingantacciyar hanya, da bunkasa fannin kimiyya da fasaha, wadda ita ma ta zame wa sauran kasashe abin koya. Hakika, a wannan zamani da muke ciki, kusan dukkan kasashe suna sa lura kan aikin raya sabbin masana’antu. Saboda ra’ayi na kariyar cinikayya ya haifar da...
    Wata tanka ɗauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lambata zuwa Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja, lamarin da ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin. An gano cewa tankar, wadda ta taso daga Legas tana kan hanyarta na zuwa Kano, ta kife ne da sassafe a garin Takalafiya da ke Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja. Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode Wani mazaunin garin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya shaida wa Aminiya cews lamarin ya faru kimanin kilomita biyu daga garin Lapai. Ya ce kwanan nan aka gyara hanyar NNPCL, amma hanyar ta fara lalacewa...
      Masu sharhi na wasanni sun bayyana cewa wasan na yau zai kasance mai cike da fasaha da kwarewa, musamman ganin cewa kungiyoyin biyu na da ‘yan wasa matasa masu zafin guiwa kamar Vinicius Jr., Jude Bellingham, da Lamine Yamal, wadanda ke son rubuta sunayensu cikin jerin manyan taurarin da suka taba buga El Classico. Dukkan idanu yanzu sun karkata zuwa Madrid, inda ake jiran ganin wanda zai yi nasara a wannan karon. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu October 25, 2025 Wasanni Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya...
    Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i.  Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya  Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.5, inda aka raba biliyan ɗaya ga mutane 701 a faɗin jihar.  Gwamna Raɗɗa...
    Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, ya amince da buƙatar ƙirƙiro sabbin jihohi guda shida. Wannan mataki na cikin abin da aka cimma a ƙarshen taron kwana biyu da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu. Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum A cewar kwamitin, an tattauna kan buƙatu 69, ciki har da buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙananan hukumomi 278. Daga cikin buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi...
    Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru 40, ba kawai magana ce ta fafutuka ba, har ila yau kalubale ne ga shugabanni.   Matakin Dasuki ya kasance wani muhimmin lamari a farfajiyar siyasar Najeriya, inda ’yan siyasa kalilan ke ja da baya daga mukaman su. Sanarwar sa an fassara ta sosai a matsayin wakilcin  gwagwarmayar adalci tsakanin tsararraki wanda ya taimaka wajen jagoranta, wanda ke nufin rage gibin da ke tsakanin tsofaffi...
    Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa matsalar kashe-kashen da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar nan ba ta da alaƙa da addini, illa dai ayyukan miyagu da ke kashe Musulmi da Kirista ba tare da la’akari da bambancin addini ba. Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a matsayin bako mai jawabi a taron cika shekaru 35 da kafuwar Cocin Anglican da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna. NSCDC ta yi alhinin mutuwar Kwamishinan Tsaron Gombe An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a Kano Tsohon Ministan ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su dawo daga rakiyar mutanen da ke amfani da addini wajen...
    Waɗannan matsalolin, sun sanya ake yin jigilar  kayan ta kan hanya, a manyan motoci, wanda hakan ya sanya masu ruwa da tsaki a fannin ke ci gaba da kokawa, saboda kuɗaɗen da suke kashewa masu yawa, wajen jigilar kayansu wanda hakan ya saɓawa manufar ta kafa Tashodhin  Jiragen Ruwan ta kantudu. Injiniya Kayode Opeifa Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa na ƙasa ya tabbatar da waɗannan matsalolin a taron 2025 Ƙungiyar ‘Yan Jarida Wakilai  da ke ɗauko rahotannin ɓangaren sufuri TCAN, da aka gudanar a jihar Legas. A cewar Kayode, ƙalubalen rashin tsaro, a jihar Neja, hakan ya tilasta Hukumar dakatar da jigilar kayan ta hanyar amfani da Jirgin ƙasa zuwa Kaduna. Sai dai ya bayyana cewa gwamnonin jihohin...
    Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya fadawa shugaban Amurka Trump cewa ya ci gaba da rayuwar cikin mafarkinsa! A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Isra’ila ta “Knesset”, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, amma kalmomi biyu kacal da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Iran, Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, ya furta sun isa su zame a matsayinsa mayar da martani. Ya zo cikin Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa: Alfaharin Shugaban Amurka cewa: “Hakika sun yi luguden wuta kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran tare da ruguza su, tabbas wannan da’awa ce kawai, amma Amurkawa su ci gaba da rayuwa cikin wannan ruɗunsu!” Martani mai ƙarfi...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Sakon wasikar da Iran, Rasha, da China suka aika ga Majalisar Dinkin Duniya alama ce ta hadin kai Shugaban Majalisar shawarar Musuluncin ya bayyana wasiƙar da ma’aikatun harkokin waje na Iran, Rasha, da China suka aika wa Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin tsaro a matsayin wata alama ta haɗin kai mai mahimmanci tsakanin waɗannan ƙasashe uku, yana mai cewa, “Da karewar kuduri mai lamba 2231, wa’adin Darakta Janar na IAEA na tabbatarwa da sa ido kan aiwatar da shirin makamashin nukiliya na Iran ya ƙare.” Mohammad Baqer Qalibaf ya ce a wani zaman jama’a na Majalisar Shawarar Musulunci a ranar (26 ga Oktoba) da kuma a jawabinsa ga Majalisar ya bayyana...
    Tsohon kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) ya bayyana cewa: Suna da isassun makamai masu linzami masu cin zango daban-daban Tsohon kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Mohammad Ali Ja’afari, ya bayyana cewa: Iran ba ta da wani takunkumi kan adadin makamai masu linzami, kuma wannan karfin ya hada da nau’ikan makamai masu linzami daban-daban masu cin iyakoki daban-daban. Ya kara da cewa: Karfin kasar a wannan fanni yana da fadi kuma ba shi da iyaka. A wata hira da manema labarai da aka watsa jiya, Asabar, Manjo Janar Ja’afari ya yi magana kan batutuwan yanki, na kasa da kasa, da na cikin gida, ciki har da ci gaba kan bangaren ‘yan gwagwarmaya da...
    Memba a Majalisar Tarayyar Turai ya bayyana cewa: Zaman lafiya na gaske yana buƙatar ɗaukar matakin hukunta Isra’ila Dan Majalisar Dokokin Turai ta Ireland (MEP) Barry Andrews ya jaddada cewa: Daukan matakin hukunta haramtacciyar kasar Isra’ila kan munanan laifukan da ta aikata a Zirin Gaza ita ce hanya daya tilo da za a cimma zaman lafiya na gaskiya da dorewa, yana mai kira ga Tarayyar Turai da ta ci gaba da zabar sanya takunkumi kan Isra’ila. Jawabin Andrews ya zo ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu na kasar Turkiyya, wanda ya yi daidai da taron Tarayyar Turai da aka gudanar a Brussels ranar Alhamis da ta gabata, wanda ya tattauna makomar dangantakar Tarayyar Turai da Isra’ila...
    Kungiyar Kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga Türkiyya zuwa arewacin Iraki Kungiyar kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga cikin kasar Turkiyya zuwa arewacin Iraki a yau Lahadi. Kafafen yada labarai sun ambato wata sanarwa daga kungiyar ‘yan tawayen kurdawar tana cewa: “Ta janye dukkan mayakanta daga cikin kasar Turkiyya zuwa yankunan arewacin kasar Iraki. A watan Fabrairun da ya gabata ne, Abdullah Ojalan, wanda ya kafa kungiyar Ma’aikata ta Kurdistan (PKK) a Turkiyya, ya yi kira da a rusa kungiyar, yana mai kira ga mayakan kungiyar da su ajiye makamansu su koma ga daukar matakin siyasa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up...
    “Yayin da ake gudanar da samamen bisa ga bayanan sirri daga wasu mazauna garin Farin Ruwa da ke karamar hukumar Shanono, jami’an hadin gwiwa na rundunar yaki da ta’addanci ta rundunar da kuma jami’an rundunar da ke Shanono, sun gudanar da samamen na kwarewa a ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 02:00 na dare. Hakan ta sa, an samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne,” in ji sanarwar.   Kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Farin Ruwa, yana mai bayyana yadda suka bayar da bayanan sirrin a matsayin muhimmin abu ga nasarar aikin. Ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutum 25 da ake zargi da shirya auren jinsi a samamen da ta kai wani wurin shagali a jihar. A cewar hukumar, an kama mutanen ne da yammacin Asabar a wani wurin taro da ke kan titin Hotoro Bypass a ƙaramar hukumar Tarauni. Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno NSCDC ta yi alhinin mutuwar Kwamishinan Tsaron Gombe Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar Hisbah mai kula da ayyuka na musamman, Sheikh Dokta Mujahid Aminuddeen Abubakar, ne ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a ranar Lahadi. Ya bayyana cewa samamen na zuwa ne bayan bayanan sirri da hukumar ta samu daga wani mai kishin al’umma. Ya bayyana cewa bayanan sirrin...
    Ya ƙara da cewa Kaduna ita ce jihar da ta cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa a yarjejeniyar Malabo kan saka hannun jari a harkar noma. Shugaban AUDA–NEPAD a Nijeriya, Honarabul Jabir Abdullahi Tsauni, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna bisa samar da kuɗaɗen haɗin gwiwa da suka bai wa shirin damar faɗaɗa zuwa dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar. A cewar Tsauni, an horar da ƙanana manoma 345 kan kyawawan hanyoyin noma da kuma dabarun noma masu jituwa da yanayin sauyin yanayi, ciki har da noman lambu na gida irin su tumatir, barkono mai zaƙi, masara, wake, da waken soya. Komashinan noma na Jihar Kaduna, Murtala Dabo, ya bayyana cewa wannan shiri ya nuna yadda Kaduna ke da niyyar mayar...
      Wannan nasara mai ban mamaki ta sa kungiyar Niger Tornadoes ta koma matsayi na biyu a teburin gasar, inda yanzu take da maki 17 a kasan Nasarawa United. Hakazalika, sakamakon ya bar Kano Pillars a cikin mawuyacin hali a gasar yayin da ta ke matsayi na 19 da maki 8 kacal. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus October 25, 2025
    Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Gombe, ta bayyana alhini bisa rasuwar Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (mai ritaya). Haka kuma hukumar ta bayyana jimami kan da ɗan sandan da ke tsaron kwamishinan, Sajan Adamu Husaini, da direbansu, wadanda suka rasu a wani mummunan hadarin mota da ya afku ranar Juma’a. Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa  A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar, Kwamandan hukumar, Jibrin Idris, ya ce rasuwar babban rashi ce ba ga iyalan mamatan kawai ba, har ma ga Gwamnatin Jihar Gombe da al’ummar...
    Aikin, wanda ke wakiltar tashar fitar da ɗanyen fetur ta farko da kamfanin Afirka mai zaman kansa ya bunƙasa a ƙasar, yana nuna babban jarin da ya wuce dala miliyan 400 a matakin farko, inda ake sa ran kuɗin zai ci gaba da bunƙasa har ya haura dala biliyan 1.3. GEIL, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Anthony Olusegun Adegbulugbe, wani sanannen malami kuma ƙwararren masani a fannin tsare-tsaren makamashi, yana da ƙwarewa mai sosai a tsawon shekaru masu yawa. Yana aiki a matsayin shugaban jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Jihar Osun, ya kuma kasance babban mai ba da shawara kan makamashi ga tsohon shugaba ƙasa, Olusegun Obasanjo. Haka kuma ya kasance shugaban shirin “National Gas to Power” na Nijeriya kuma ya...
    Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun daƙile harin da ’yan ta’addan ISWAP suka kai a garin Gamborun Ngala da ke kan iyakar Najeriya da ƙasar Kamaru. Rahotanni daga rundunar sun nuna cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 6:15 na yammacin ranar Asabar, inda aka ji ƙarar harbe-harbe masu ƙarfi a sassa daban-daban na garin. ABU ta musanta zargin ƙera makamin nukiliya a ɓoye An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa  Sai dai a cewar majiyoyi, sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka shiga fafatawa da ’yan ta’addan, kuma suka fatattake su ba tare da wata asara a ɓangaren dakarun ba. Wakilinmu ya ruwaito cewa babu wani soja ko...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayar da tallafin Naira miliyan biyu ga iyalan SC Bashir Adamu Jibrin, jami’in hukumar sibil difens (NSCDC) da ya rasu a bakin aiki a kasuwar Shuwarin da ke ƙaramar hukumar Kiyawa. Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ne ya miƙa tallafin ga matar marigayin a ofishinsa, inda ya ce wannan taimako na nufin tallafa wa iyalan marigayin tare da taimaka musu wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu. Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum ABU ta musanta zargin ƙera makamin nukiliya a ɓoye Ya shawarci matar marigayin da ta yi amfani da kuɗaɗen wajen kula da ilimi da walwalar ’ya’yanta, tare da jaddada cewa gwamnatin Jigawa za ta ci gaba da...
    A gobe Litinin ne za a bude taron kungiyar tattalin arziki ta “Eco” a nan birnin Tehran,kamar yadda mataimakin ministan harkokin cikin gida na Iran Ali Zaini Wand ya sanar. Taron dai za a yi shi ne a matakin ministocin harkokin cikin gida domin Shata hanyoyin aiki a tare a tsakaninsu, bayan da aka dauki shekaru 15, ba a gudanar da shi ba. Ali Zaidani ya kuma yi ishara da cewa taron na wannan karon zai mayar da hankali ne akan hanyoyin bunkasa alaka da kasashen makwabta,musamma bisa la’akari da cewa gundumomin Iran da suke aka iyaka suna da kyakkyawar alaka da kasashen makwabta. Bugu da kari  taron na kungiyar “Eco” zai yi kokarin kawar da kalubalen da ake fuskata...
    Kafar watsa labaru ta “Afircanews” ta bayyana cewa, babu wani cikakken dalili da aka gabatar dangane da sauye-sauyen, tare da kuma kore jita-jitar da aka rika watsawa akan yunkurin juyin Mulki a kasar a watan Satumba, dda ya kai ga tsare sojoji 20 daga ciki har da Birgediya janar da kuma kanar. Mai Magana da yawun shugaban kasar ta Nigeria, ya bayyana cewa; shugaba Ahamd Tinubu ya salami manyan jami’an sojoji da su ka hada babban hafsan hafsoshi Emmanuel Ogalla, shugaban sojan ruwa, da Hassan Abubakar, shugaban sojan sama. Shugaba Ahmad Tinubu ya nada Olufemi Oluyedi, tsohon hafsan hafsoshin soja a matsayin sabon ministan tsaro.  Sabon shugaban sojan kasa shi ne Manjo janar W. Shaibu Shugaban sojan Sama kuma shi...
    Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran  Ali Larijani ya bayyana cewa; Bayan da aka dauki shekaru biyu ana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi, wanda mutane 70,000 su ka yi shahada, wasu fiye da 100,000 su ka jikkata, suna son a rufe wannan laifin da taron zaman lafiya. Ali Larijani ya kara da cewa; Sun kashe al’ummar Falasdinu, sun hana shi abinci da ruwa, yanzu kuma suna son bayyana kawukansu a matsayin masu ceto da Falasdinawa, don haka wannan taron ba komai ba ne sai wasan kwaikwaiyo. Taron da aka yi a Sherm-Sheikh na Masar an yi shi ne a karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump wanda kasarsa ce ta kasance a gaba wajen bayar da makamai ga...
    Yana magana ko jawabi cikin hankali, amma kuma shawarwarin da yake badawa suna da matuƙar amfani wajen kawo gyaran wurare da dama. Mai ilimi, tsara yadda za’a ɓullo ma al’amura, mutunci ga kuma kwarjini da ƙwarewa An haife Kalu 5 ga Mayu, 1971, a Agbamuzu, a ƙaramar hukumar Bende ta Jihar Abia State, tarihin rayuwar Kalu ya fara ne daga aiki da kuma samun tallafin ƙaro ilimi. Yana da digirin digirgir PhD a tsarin al’umma da kuma karatun abinda da wayo ake koyonsa (Jami’ar Abuja), da kuma LL.M akan ta’addanci da taimakawa kan jin ƙai  (Distinction, daga Jami’ar Kalaba), da MBA daga Jami’ar Oɗford Brookes  (UK), da kuma LL.B (Hons.) daga Kalaba. Ya cigaba da karatu— halin yanzu yana karanta...
    A yau Asabar 25 ga wannan wata, ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar sun gudanar da liyafar murnar kebe ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan, a dakin taro na Diaoyutai dake birnin Beijing. Wakilan bangarori daban daban na yankin Taiwan da na babban yankin kasar Sin masu halartar bikin murnar cika shekaru 80 da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan da safiyar wannan rana sun halarci liyafar. Direktan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar...
    Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi. NASENI tana ba da ababen more rayuwa da tallafin manufofin, yayin da ɓangaren da ke kula da masana’antu, yana mai da hankali kan haɗin gwiwa, ƙirƙira da kasuwanci don kafa Nijeriya a matsayin cibiyar fasahar Afirka. Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya...
    “Ban taba tunanin zan zama taurariya a duniya ba.” Daga Yobe Zuwa Fagen Duniya An haife ta a Jihar Kano kuma ta tashi a Yobe, labarin Nafisa ba shi da wuya kamar yadda yake da ban sha’awa. Mahaifinta ya rasu tun tana jaririya, kuma mijin mahaifiyarta mai suna Alhaji Yusuf Umar Kaigama ya rene ta, wanda ya dasa mata dabi’u na tarbiyya da azama. Tana kuma ɗauke da tsatson sarautar zuriyar sarakuna biyu masu daraja ta masarautar Kano, wato Sarkin Kano Ibrahim Dabo da Sarki Abdullahi Maje Karofi. Amma bayan jinin sarautar da take ɗauke dasu, yunwar ta na neman ilimi ya sa ta zama daban. A yanki da matsalar staro ta yi katutu wanda kuma yake dakushe duk wani...
    Wakilan kasar Sin da na Amurka sun yi taro da safiyar yau Asabar don tattaunawa kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis da ta gabata, wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin, ya bayyana cewa, bangarorin biyu za su gudanar da shawarwari kan muhimman batutuwa game da huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, bisa muhimmiyar yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin da suka tattauna ta wayar tarho a wannan shekarar. Mataimakin firaministan kasar Sin kuma memba na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin He Lifeng ne ke jagorantar tawagar kasar ta Sin a tattaunawar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)...
    Jami’ar Tarayya ta Dutsinma ta zabi Farfesa Muhammed Khalid Othman a matsayin sabon Shugaban Jami’ar na dindindin, tare da amincewar Majalisar Gudanarwar Jami’ar. Da yake zantawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, Magatakardar Jami’ar, Dokta Musa Ajiya, ya bayyana cewa mai kula da jami’ar (Pro-Chancellor), Ali Abubakar-Jatau, ne ya sanar da nadin. A cewar Dokta Ajiya, Abubakar Jatau wanda shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa, ya bayyana hakan ne bayan taron na musamman karo na 36 da aka gudanar a daren Juma’a. Ya ce Farfesa Othman ya fito ne a matsayin wanda ya fi kowa cancanta bayan wani tsari na tantancewa mai tsauri kuma bisa gaskiya, a cikin mutane 17  da suka nemi mukamin 17. Ya ƙara da...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa Singapore a yau Asabar don ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar firaministan Singapore Lawrence Wong. Li ya bayyana cewa, a cikin shekaru 35 da suka gabata tun bayan kafa huldar diflomasiyya, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da kasancewa mai kyau da samun ci gaba, tare da zurfafa amincewa da juna a siyasance, da hadin gwiwa mai amfani da kuma mu’amala ta kut-da-kut tsakanin mutanensu, wanda ya kafa misali don koyo tare da hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare a tsakanin kasashe. Ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin aiki tare da Singapore don karfafa daidaita dabarun ci gaba, da fadada hadin gwiwa mai amfani ga dukkan...
    Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi. NASENI tana ba da ababen more rayuwa da tallafin manufofin, yayin da ɓangaren da ke kula da masana’antu, yana mai da hankali kan haɗin gwiwa, ƙirƙira da kasuwanci don kafa Nijeriya a matsayin cibiyar fasahar Afirka. Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD October 25, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15 October 25, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC October 25, 2025
    Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU,  ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta, cewa tana aikin ƙera makamin nukiliya a ɓoye a cikin jami’ar. A wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jami’ar, ƙarƙashin Malam Auwalu Umar, ya fitar, jami’ar ta bayyana cewa labaran da ake yaɗawa ba su da tushe balle makama. Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum ’Yan sanda sun taimaka wa ’yan daba rusa gidaje — Al’ummar Shendam “Mun lura da wani faifan bidiyo da na’urar AI ta ƙirƙira, wanda wasu ke yaɗawa suna iƙirarin cewa ABU na ƙera makamin nukiliya a ɓoye. Wannan ƙarya ce babu gaskiya a cikinta,” in ji...
    Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, ta karyata wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa jami’ar na da hannu wajen wani shiri na sirri kan hada makamin nukiliya a Nijeriya. A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar, ya fitar a ranar Asabar, jami’ar ta bayyana cewa wannan faifan bidiyon da aka samar ta hanyar na’urar kirkirar bidiyo, karya ne kuma an shirya shi ne don rikita jama’a da bata hakikanin manufar kasar wajen amfani da makamashin nukiliya. Umar ya jaddada cewa dukkan aiyukan nukiliyar Nijeriya ana gudanar da su ne bisa tsarin lumana da kuma bin ka’idodin kasa da kasa kamar yarjejeniyar NPT da Pelindaba Treaty, wadda ta...
    Gungun kogiyoyin bada agaji sun yi gargadin cewa yanayin da rayuwar ke gudana a yankin gaza ya zarce yadda ake tsammani, duk da abin da aka kira da tsagaita wuta, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana akalla falasdinawa 1.5 suka cikin bukatar gaggawa domin tsira da rayuwarsu. Duk da cika kwanaki 13 da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Gaza tsakanin Hamas da isra’ila, amma alumma suna cikin bala’I a yankin, duk da gargadin da ake yi akan haka,  sama dai kungiyoyin agaji 41 ne suka yi kira ga isra’ila ta janye killacewar da tayi wa yanki, kuma kotun duniya ta fitar da hukumce dole ne isra’ila ta bude kofofin shigar da kayan agaji zuwa yanki kuma ta tabbata...
    Matakatin shugaban Amurka Donald Trump na nada tsohon fira ministan birtaniya Tony Blair  a matsayin mai ruwa da tsaki cikin alamuran gaza bayan dakatar da bude wuta ya fuskancin turjiya daga kasashen larabawa da kuma na musulmi, Balair shi ne mutum daya da aka ayyana sunansa daga cikin mambobin kwamitin tabbatar da sulhu da trump ya bada shawara na sanya ido bayan kawo karshen yaki tsakanin bangarorin biyu. Akwai damuwa sosai da shakku kan kasancewar Blair daga cikin masu ruwa da tsaki a alamuran yankin, musamman bayan goyon bayan da ya nuna wajen kai wa iraki hari tare da tsohon shugaban Amurka na wancan lokacin a shekara ta 2003 ,a gefe daya kuma yana kare Isra’ila, jamai’an diplomasiyan larabawa sun...
    A yau Asabar al’ummar kasar Ivory Coast ke zaben shugaban kasa wanda ya raba kan kasar inda wasu ke son shugaba Alassane Ouattara ya yi tazarce, wasu kuma na ganin lokaci ne na samar da sabon shugabanci a kasar. Fargaba ta karu sosai tun bayan cire manyan ‘yan takara biyu na jam’iyyun hamayya – wato tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da Tidjane Thiam, wani kusa a fagen siyasa kuma abokin kawancen Ouattara kafin ya zama abokin hamayya. Rahotanni sun ce Shugaba Ouattara ya yi kira ga magoya bayansa su fito su zabe shi duk da yan kasar da dama na tunanin shi zai lashe zaben,  kafin zaben an samu rikici a sassan kasar da dama inda aka kama daruruwan mutane...
    Rahotanni sun bayyana cewa Tehran za ta karbi bakunci taron ministocin cikin gida na  kungiyar Eco a karon farko a cikin shekaru 15 da nufin karfafa tsaro  da kuma kara fadada yin aiki tare a bangarorin tattalin arzik,i aladu, da kuma harkokin diplomasiya a yankin. Jami’an iran sun tsinkayi irin alfanu da taron kwanaki 2 zai kawo da zai kunshi jerin tattaunawa tsakanin kasashen da sauran bangarori daban –daban. Wannan taron yana zuwa ne lokacin da kasashen dake mambobi a kungiyar suke fuskantar kalubale , da suka hada da rashin tsaro a iyakoki, da aikata muggan laifuffuka da aka tsara, da kuma rashin zaman tabbas a yankin, iran na nufin fadada ajendar ta hanyar yada aladu da amfani da diplomasiya...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15 October 25, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC October 25, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take October 24, 2025
    Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da lafiyar mutanen Mafa, mahaifar sa. Gwamnan dai a wasu ziyarce-ziyarcen da ya kai har sau biyu, ya ware ta, ya kuma yaba wa sadaukarwar da ta yi, tare da yaba mata kan yadda ta tsaya tare da jama’arsa duk kuwa it aba ‘yar asalin yankin ba ne. Kyautar kwazo da rikon amana da ta samu ya zo ne a lokacin da Gwamna Zulum, wanda ya...
    A gun cikakken zaman taro na hudu na kwamitin kolin JKS na 20 da aka gudanar tun daga ranar 20 zuwa 23 ga wannan wata a nan birnin Beijing, an yi bincike da zartas da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, inda aka gabatar da jagora da burika kan yadda za a raya kasar a wannan lokaci, kana an tsara taswirar bunkasa kasar Sin a shekaru 5 mazu zuwa. Ga duk duniya, shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar ba shiri na kasar Sin kawai ba ne, kuma ba kasar Sin ba ce wadda ta fara tsara shirin, amma kasar Sin ita kadai ta kiyaye aiwatar da irin shirin. Sirrin tafiyar da harkokin kasar...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa a harkar tsaron sararin samaniya, domin hana ’yan ta’adda na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare. Zulum, ya faɗi haka ne a ranar Juma’a a garin Mafa, bayan wani hari da Boko Haram suka kai. Sauke Hafsoshin Tsaro: Za a yi wa Janar-Janar 60 ritaya daga aiki ’Yan sanda sun taimaka wa ’yan daba rusa gidaje — Al’ummar Shendam Ya ce, “Babban abin da nake son magana a kai shi ne amfani da jirage marasa matuƙa. An shaida min cewa sun yi amfani da su a Dikwa, kuma hakan abu ne mai tayar da hankali.” Gwamnan ya bayyana cewa yawaitar irin waɗannan jirage a...
    Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin halartar taron shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pacific (APEC) karo na 32 a Koriya ta Kudu da kuma ziyarar aiki a kasar Koriya ta Kudu, an kaddamar da nuna muhimman shirye-shiryen talabijin da fina-finai na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a membobin APEC. Za a watsa shirye-shiryen fiye da goma a manyan kafofin watsa labarai 22 a kasashe 14 na yankin Asiya da tekun Pacific, ciki har da Australia, Kanada, Chile, Indonesia, Koriya ta Kudu, Peru, Rasha, Thailand, da Amurka.   Babban darektan CMG Shen Haixiong, ya fada a cikin wani sakon bidiyo cewa, ana fatan wadannan shirye-shiryen talabijin da fina-finai za su...
    “Muna godiya ga sadaukarwar da sojoji da hukumomin tsaro ke yi. Wannan wasa tsakanin tsoffin ’yan wasan Barcelona da tsoffin ’yan wasan Afirka shaida ce ta nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu wajen dawo da zaman lafiya,” in ji shi. Tsoffin ’yan wasan Barcelona sun isa Nijeriya domin buga wasa da tsoffin ’yan wasan Afirka a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoba, 2025. Yayin da Matawalle ke tarbarsu a ofishinsa, ya miƙa saƙon maraba da fatan alheri ga tawagar a madadin Gwamnatin Tarayya da al’ummar Nijeriya, inda ya yi musu fatanalheri. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan...
    Aƙidar Dr Bello abu ne mai saƙin gaske kuma akwai hikima a ciki sosai. Shi ne kuma samar da ingantacciyar kiwon lafiya wand aba wai sai kana da kuɗi mai yawa ba. Tsarinsa shi ne haɗa yi wa mutane aiki, ilimantar da su tared fda kuma tsugunar da su. Wannan mataki ne da yake tabbatar da an samun cikin gaggawa da kuma sauƙin gaske.. Daga Legas zuwa Kano, daga Ondo zuwa Kuros Riba, kungiyar CFDF tana tafiya da kayan aiki na tafi da gidanka da kuma rundunar likitoci masu tiyata na sa kai, masu aikin jinya, da ma’aikatan jinya. Kowace manufa asibiti ce mai motsi – duba marasa lafiya, yin hadaddun tiyata, da bayar da shawarwari da tallafin abinci mai...
    Rundunar Sojin Najeriya za ta fuskanci babban sauyi wanda zai tilasta wa manyan sojoji yin ritaya daga aikinsu. Rahotanni sun bayyana cewar akalla Janar-Janar 60 ne ake sa ran za su yi ritaya sakamakon sabbin sauye-sauye da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Hafsoshin Tsaro. ’Yan sanda sun taimaka wa ’yan daba rusa gidaje — Al’ummar Shendam Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya dalilin sauya hafsoshin tsaro — ADC Sanarwar da aka fitar a ranar Juma’a ta tabbatar da sauke Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Babban Hafsan Tsaro tare da wasu hafsoshi. Janar Laftanar Olufemi Oluyede, wanda a baya shi ne Babban Hafsan Sojin Kasa, shi ne yanzu sabon Babban Hafsan Tsaro. Janar Meja Waidi Shaibu shi ne...
    “Gudanar da harkokin kuɗaɗe ba bayar da taimako ba ne, haƙƙi ne.”  Ƙoƙarin Cike Gibi Tare Da Gina Makoma Mai Kyau Lokacin da OPay ya shiga fannin harkokin kuɗaɗe na zamani a Nijeriya, ƙalubalen ya kasance bayyane suke, kusan rabin yawan mutanen Nijeriya ba su da damar samun shiga harkokin kuɗaɗe. Waɗanda suka kafa kamfanin sun gano cewa yawancin ‘yan Nijeriya sun yin isa da bankuna, tsarin yana haifar da jinkiri, kuma tsarin yana da barazana mai yawa. OPay ta kasance mai sauƙin gudanarwa, wani tsarin kuɗi na wayar hannu da ya dace da rayuwar yau da kullum ba tare da tangarda ba. Daga biyan kuɗi ta walat zuwa biyan kuɗin kayayyakin more rayuwa, daga sayan katin waya zuwa mu’amaloli...
    Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, wanda Kwamishinan Ruwa, Alhaji Aminu Dodo Iya, ya wakilta, ya jaddada cewa sarautun gargajiya su ne ginshiƙin zaman lafiya da ci-gaban al’umma. Ya ce shugabannin gargajiya na taka rawa wajen haɗa kan jama’a da gwamnati, tare da tabbatar da ɗorewar cigaba a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales October 25, 2025 Manyan Labarai Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 Labarai Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa October 25, 2025
    Ya ƙara da cewa cibiyar Centre for Energy Research and Training (CERT) ta  jami’ar ABU, wadda aka kafa tun 1976, tana aiki tare da IAEA da kuma ƙasashe kamar Amurka, da Rasha da China, kuma ba ta taɓa gudanar da wani shiri na makamin nukiliya ba. A cewarsa, “ABU tana ci gaba da sadaukar da kai wajen inganta kimiyya da fasaha don ci gaban ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta hanya mai amfani da jama’a.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 ...
    Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo Wannan inganci ba wai alama kawai ba ce. Tun daga shekarar 2023, hukumar ta sauƙaƙa sama da Naira biliyan 10 na mayar da kuɗin masu amfani don sulhu kai tsaye, mai iya bin sawu wanda ke nuna cewa dawainiya da gaskiya za a iya auna ta da kuɗi, ba wai da alkawari kawai ba. Jarumta a Zamanin Intanet Wataƙila mafi girman ƙarfin gwiwar FCCPC ya bayyana ne a shekarar 2025 lokacin da ta ɗora tarar Dalar Amurka miliyan 22 kan Meta Platforms saboda ayyukan amfani da bayanai ta...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Bai kamata a yi mummunan amfani da kwamitin tsaron ba ko kuma a yi amfani da shi don dalilai na siyasa Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya bayyana cewa: An gwada Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya sosai ta hanyar ayyukan ta’addanci da kuma amfani da dabarunta na siyasa. Ya ce: “Dole ne kwamitin tsaro ya cika nauyin da ke kansa da mutunci, inganci, kuma ba tare da son kai ba. Babu wani memba, komai karfi da zai iya amfani da wannan cibiyar ba bisa ka’ida ba ko kuma ya yi amfani da shi don dalilai na siyasa ko na bangare guda.” A jawabinsa a Majalisar...
    Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Yaƙin da aka ɗora wa Iran ya canza daidaiton da ke tsakanin Sahayonayya da Amurka Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Hussein Ta’ib, ya ce: Yaƙin kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyya ta ɗora wa Iran, ba wai kawai bai cimma komai ga Isra’ila ba ne, har ma ya canza daidaiton dabarun Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila gaba ɗaya. A lokacin taron tattaunawa na 31 na ƙungiyar Jaruman Musulunci a Qom, Hussein Ta’ib ya ce: “Dakarun kare juyin juya halin Musulunci da sojojin Iran sun kalubalanci masu girman kai inda suka kai wani mataki cikin saurin na zarce lissafin...
    Mataimakin babban kwamandan rundunar sojin Iran kan hadin gwiwa ya jaddada cewa: Sojojin Iran a shirye suke su fuskanci kowace barazana Mataimakin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Iran kan Hadin Gwiwa, Rear Admiral Habibullah Sayyari, ya ce: An zabi Sojojin Iran daga cikin mafi kyawun matasa a kasar kuma suna shirye su fuskanci kowace barazana. A gefen bikin bude gasar cin kofin duniya ta 4 ta sojojin masu harba kibau (SIZM 2025), wadda rundunar sojin sama ta shirya a kungiyar masu harbi a ranar Juma’a da yamma, Rear Admiral Sayyari ya yi magana da manema labarai game da matakin shirye-shiryen Sojojin da kuma rawar da wasanni ke takawa wajen inganta karfinsu. Ya jaddada cewa, “Wasanni suna da matukar muhimmanci ga lafiyar...
    Shugaban kasar Venezuela yayi tsokaci kan matakin sojin Amurka yana mai cewa Amurka tana son ƙirƙiro yaƙi a yankin Shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro ya zargi Amurka da yunkurin tayar da sabon yaki a kan kasarsa, bayan rahotannin da ke cewa; Amurka na gudanar da shirin soja na kai hari kan wuraren samar da hodar iblis a Venezuela. Maduro ya ce a cikin wani jawabi da ya gabatar ta gidan talabijin: “Suna kirkirar yaki ne domin tabbatar da ta’addancin da suke yi wa Venezuela… Suna son mayar da batun miyagun kwayoyi ya zama hujjar sabon mamayar sojoji a Latin Amurka.” Ya kara da cewa gwamnatinsa “ba za ta bari wani karfi na kasashen waje ya keta ikon Venezuela ba,” yana...
    Bangarorin Falasdinawa sun amince a birnin Alkahira kan yadda za a tafiyar da Gaza a nan gaba Bangarorin Falasdinawa da suka yi taro a birnin Alkahira a ranar Juma’a sun sanar da amincewarsu kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi gudanar da yankin Gaza da kuma ci gaba da tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, da kuma abu mafi muhimmanci na kafa kwamitin da za a mika masa ikon wucin gadi na tafitar da al’amuran Falasdinawa a Gaza. Wata sanarwa da bangarorin suka fitar a karshen tarukansu a babban birnin Masar ta bayyana cewa, bisa gayyatar Jamhuriyar Larabawa ta Masar, karkashin jagorancin Shugaba Abdul Fattah el-Sisi, da kuma ci gaba da kokarin ‘yan uwa masu shiga tsakani a Masar, Qatar, da...
    Sauyin shugabannin tsaro dai ya nuna matakin da Tinubu ke ɗauka wajen sake fasalin tsaro, amma kuma ya buɗe sabon babi na tattaunawa kan yadda ake kula da tsofaffin hafsoshin da suka ba ƙasa hidima tsawon shekaru. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 Manyan Labarai Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe October 25, 2025
    Mazauna unguwar Tudun Wada da ke garin Shendam a Jihar Filato sun zargi wasu jami’an ’yan sanda da ba wa ’yan daba kariya wajen rusa gidajensu. Shaidu sun ce sama da ’yan sanda 100 ɗauke da makamai ne suka isa yankin da misalin karfe 5 na safiyar Laraba, suka ba wa wasu ’yan daba kariya yayin da suke lalata gine-ginen jama’a Lamarin ya jawo zanga-zangar da mazauna yankin, ciki har da mata da yara, suka gudanar don nuna adawa da abin da suka kira “cin zarafi daga jami’an tsaro.” Mazaunan sun bayyana cewa rushewar gidajen ta faru ne da haɗin gwiwar iyalan Fuanter duk da cewa ana shari’a a gaban kotun ɗaukaka ƙara kan mallakar filayen. Sun ce suna da...
    Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa su na nazarin dokoki guda 69 da kuma buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙudirin ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278 bisa ga tsarin kundin mulkin 1999. Barau, wanda shi ne shugaban Kwamitin Bita na Tsarin Mulki a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ne a taron haɗin gwuiwa da kwamitocin majalisar dattawa da kwamitocin majalisar wakilai kan gyare-gyaren dokokin tsarin mulki da suka gudanar a Lagos. Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu Firimiyar Nijeriya: Barau FC Ta Samu Nasarar Farko A Tarihinta Ya jaddada cewa an dauki lokaci mai tsawo wajen tattaunawa da al’umma da masu ruwa-da-tsaki da ƙungiyoyi daban-daban, domin kawo waɗannan ƙuduri...
    Najeriya na fama da ɗaya daga cikin mafi munin matsalar jinƙai ta yunwa, talauci, da rashin abinci mai gina jiki. Rahoton Yanayin Ci-Gaban Nijeriya da Bankin Duniya ya fitar a watan Oktoba, ya nuna mutane miliyan 139 a ƙasar na rayuwa cikin talauci a shekarar 2025. Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da rahoton, da cewa sauye-sauyen da ta yi a fannin tattalin arziki na haifar da sakamako mai kyau. Aminiya ta gudanar da bincike don gano gaskiyar halin da ’yan Nijeriya ke ciki a birane da ƙauyuka. Wakilinmu ya samu damar shiga cibiyoyin kula da masu fama da rashin abinci mai gina jiki da Ƙungiyar Likitoci ta Duniya (MSF) ke tallafawa a Kano da Maiduguri, inda ya gano mummunan tasirin...
    Rashin Biyan Yan-fansho Bisa Lokaci Ta tabbata a lokacin mulkin Kwankwaso, “yan fansho a Kano, kan jira tsawon Watanni zuwa Shekaru ba tare da an biya su hakkokinsu na barin aiki ba. Haka ɗan-jummai Ganduje, yakan dan fara biyan hakkokin “yan fanshon, sai kuma a ga ya watsar. Sai a dauki tsawon lokaci yana ɓaɓatun za a ci gaba da biya, amma sai a ji shiru. Sai aka wayi gari karɓar fansho, musamman giratuti, ya zama tamkar tafiya Lahira, yau ne? Gobe ne? Babu wata cikakkiyar amsa!. Haƙiƙa kwata-kwata babu tausai, mutane sun kwashe akasarin Shekarunsu na haihuwa suna masu hidimtawa ƙasa dare da rana, cikin yanayi na sanyi, ruwan sama da garjin rana, dole ne su fito, su aje...
    Mahalifinsa, Chief Thomas Osen Ekpemupolo, da mahaifiyarsa, Mrs. Ewe Ekpemupolo, sun rayu cikin al’umma mai arziƙin mai a lokacin da ake tsaka da nema a yi wa yankinsu adalci. Daga cikin wannan rikicewar ya taso mutum wanda daga baya zai zama ɗan gwagwarmayar Niger Delta don neman daraja, adalci, da samun ikon gashin kai. Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta Sojoji Sun Lalata Matatun Mai 20 A Yankin Niger Delta A tsakiyar shekarun 1990, arzikin mai na Nijeriya yana samu wadata a wasu wurare amma ya zama ana barin al’ummomi masu arziƙin mai cikin talauci, gurɓawa, da kuma rashin muryar magana. Ga matashin Tompolo, yin shiru wannan bai zama zaɓi ba.   Gwagwarmaya Da...
    Shugaban gwamnatin kasar Lebanon Nawwaf Salam ya bayyana cewa: Tun da ya kafa gwamnati yake aiki da dukkanin hanyoyi domin yin matsin lamba akan HKI ta daina keta hurumin kasar, sannan kuma ta janye daga wuraren da ta shiga, tare da sakin fursunonin da take rike da su.” Nawwaf Salami ya kara da cewa; Bude kafar diplomasiyya da aiki da ita a wannan fage, bai bayar da wani sakamako ba, watakila kuma zai dauki lokaci mai tsawo a nan gaba.” Shugaban gwamnatin kasar ta Lebanon ya kuma ce; A yanzu muna cikin halin yaki ne da “Isra’ila”, wani lokaci ya yi tsanani, wani lokacin kuma ya yi sauki,illa iyaka muna kokarin ganin an kawo karshen hakan.” Dangane da batun bude...
    Shugaba Gustavo Petro ya ce, ba wai kawai ba ya wata mu’amala ta kasuwanci da Amurka ba ne, ba shi ma da koda dala kwaya daya a cikin wani asusu na bankunan Amurkan balle a ce an rufe shi. Gustavo ya kara da cewa; ko kadan ba zai taba rusunawa a gaban Amurka ba, ba kuma zai ja da baya ba. A jiya Juma’a da marece ne dai Baitulmalin Amurka ya sanar da kakaba wa shugaban kasar ta Columbia takunkumi. Gustavo ya kuma ci gaba da cewa; Yadda yake fada da yaduwar muggan kwayoyi na shekaru masu tsawo, shi ne ya sa Amurkan ta dauki wannan irin matakin akansa alhali kasarsa Columbia tana taimakawa wajen hana Amurkawan shan hodar Iblis....
    Kungiyar kwallon kafa ta “Futsal” ta matan Iran ta zura kwallaye 14-0 a wasan da ya hada ta da takwararta ta kasar Bahrain mai masaukin baki. A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka bude wasannin nahiyar Asiya na kwallon kafar Futsal a kasar Bahrain. A wasan farkon, kungiyar ta Iran ta sami nasara akan takwararta ta Hong kong ta hanyar zura kwallaye shida. Wasa na biyu da Iran din ta yi shi ne da kungiyar kasar Bahrain, da ta sami galaba da kwallaye 14 da 0. ‘Yan wasan na Iran sun kunshi Fatima Shukrani, Niyayash Rahmani, Dhanaz Bakiri, Haidis Yari da kuma Narjis Amir Muhsini. Ya zuwa yanzu dai kungiyar kwallon Futsal ta Iran tana da maki...
    Babban magatakardar MDD Antonio Gutrress ya bayyana cewa majalisar tana da bukatuwa da a yi kwaskwarima da gyare-gyare. Gutrress dai ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin cika shekaru 80 da kafuwar MDD. Gutrress ya kuma ce, tare da cewa ayyukan da Majalisar take aiwatarsa suna da matukar muhimmanci,amma kuma halarcinta yana tangal-tangal, sannan kuma ya kara da cewa an dade ana sauraron a yi ma ta kwaskwarima.  A wani sashe na jawabin nashi, ya zargi wasu daga cikin mambobin MDD da cewa a lokuta da dama suna yin abubuwan da suke cin karo da dokokin majalisar, da hakan yake sa ake yin shakku akan ita kanta majalisar ta dinkin duniya. Har ila yau, Guterres ya ce; Majalisar...
    Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Lebanon ta sanar da shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani sanadiyyar harin da HKI ta kai wa wata mota a garin Zudhar dake gundumar Nabadhiyya. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da laabrin cewa a jiya  Juma’a sojojin HKI sun bude wuta a cikin Lebanon daga kan iyakar ‘alhamamis”. Bude wutar da manyan bindigogi ya kuma shafi kudancin birnin al-khayam. Har ila yau birnin na alkhayam ya fuskanci wasu hare-hare daga HKI da ta yi amfani da jiragen sama marasa matuki. HKI tana ci gaba da keta tsagaita wutar yaki da aka yi tun a 27 ga watan Aprilu 2024. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
    Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Gombe, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), ya rasu a hatsarin mota. Gwamnatin Jihar Gombe ce, ta sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Watsa Labarai, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a ranar Juma’a. Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya dalilin sauya hafsoshin tsaro — ADC Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin Duguri Sanarwar ta ruwaito cewa Bello ya rasu a kan hanyar Malam Sidi zuwa Gombe, bayan aukuwar wani mummunan hatsarin mota. “Gwamnatin Jihar Gombe na cikin jimamin sanar da rasuwar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), sakamakon a hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Malam Sidi...
      Guo ya kara da cewa, “Abubuwan da gwamnatin Amurka take aikatawa suna da yiwuwar haifar da rashin fahimta da dora laifi ga wanda bai ji ba bai gani ba, kuma kwata-kwata ba su dace ba. Kasar Sin tana kira ga Amurka ta dakatar da kai hare-haren shafin intanet kan muhimman kayayyakin more rayuwa na kasarta nan take. Bugu da kari, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don kare ‘yancin kanta na shafin intanet da kuma tsaronta yadda ya kamata.” (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan October 24, 2025 Daga Birnin Sin...
    Shirin Inganta Noma da Kula da Sauyin Yanayi na Soil Values, tare da haɗin gwiwar Kungiyar Dillalan Kayayyakin Aikin Gona ta Kasa (NAIDA) ta Arewa maso Yamma, ya ƙaddamar da sabon tsari domin sauƙaƙa samun kayayyakin gona ga ƙananan manoma a yankunan Arewacin Najeriya, da ake kira “one-stop shop a turance. Jami’ar shirin ta kasa Misis Medina Ayuba Fagbemi, ta bayyana cewa za a samar da shagunan tafi-da-gidanka guda tara da za su kai kayayyaki zuwa sama da al’ummomi 20 a jihohin Kano, Jigawa da Bauchi, inda ake sa ran shirin zai amfanar da kusan ƙananan manoma 7,000. Ta ce tsarin zai taimaka wajen kusantar da ingantattun iri, taki da magungunan kashe kwari ga manoma, tare da samar da...
    Ya bayyana cewa sarakuna suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba, musamman a fannin ilimi, inda ya ce zai tabbatar yara sun koma makaranta. Haka kuma, ya ce zai goyi bayan gwamnati a ɓangaren kiwon lafiya da tsaro, domin inganta rayuwar jama’a. Sabon Sarkin, wanda kuma shi ne shugaban hukumar kula da ilimi a matakin farko (SUBEB) ta Jihar Bauchi, ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga Allah da Gwamna Bala Muhammad saboda wannan dama da ya samu. Ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru domin ci gaban masarautarsa da Jihar Bauchi gaba ɗaya, tare da kira ga jama’ar Duguri da su haɗa kai wajen gina masarautar. “Mu mutanen Duguri a shirye muke mu taimaka wa gwamnati a duk abin...
    Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) za ta jagoranci kwamitin, domin ita ce ke da ikon tattara bayanan ma’adinai na ƙasa baki ɗaya.  “NGSA ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kaduna bisa gaskiya da bayyana bayanai, tare da yin kira da a gudanar da binciken tabbatarwa mai zaman kansa,” in ji shi. Ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwar zai ƙara goyon bayan masu zuba jari a sashen ma’adinai na Nijeriya, tare da faɗaɗa bayanan kimiyyar ƙasa, wanda zai taimaka wajen haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa ta hanyar albarkatun ma’adananta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri October 24, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya October...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa October 24, 2025 Daga Birnin Sin An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan October 24, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15  October 24, 2025
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Jigawa 774, inda ya tabbatar da kudurin gwamnatinsa na yaki da rashin abinci mai gina jiki da inganta yalwar abinci a fadin jihar. An gudanar da kaddamarwar ne yayin ziyarar Mrs. Uju Rochas-Anwuka, mai bai wa Shugaban Kasa shawara ta musamman kan lafiya ( Karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), wacce ta je Jigawa domin kaddamar da shirin Nutrition 774 da ke karkashin shirin sabunta kudurori na Renewed Hope Agenda. Gwamna Namadi ya bayyana cewa Jigawa ta kasance gaba a yaki da matsalar, tare da kafa shiri na musamman da aka yi wa lakabi da Masaki tun a 2020 domin fadakar da al’umma a...
    Jam’iyyar ADC ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana wa ’yan Najeriya ainihin dalilin da ya sa ya sauya hafsoshin tsaron ƙasa ba zato ba tsammani. Aminiya ta ruwaito yadda shugaban ƙasa ya sauya hafsoshin tsaron da ya naɗa shekaru biyu da suka wuce. Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin Duguri ’Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce jam’iyyar ta damu ganin yadda aka yi sauyin ba zato ba tsammani bayan jita-jitar yunƙurin juyin mulki. “Ko da yake shugaban ƙasa yana da ikon yin irin waɗannan sauye-sauye, amma mum damu da wannan mataki biyo bayan...
    Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa wannan zaman sulhu da ɓarayin daji da ake yi al’umma ce take yi ba wai gwamnati ba, ita gwamnati tana iya yin sulhu da ɗan bindigar da ya tuba ya yarda da zaman lafiya kuma ya ajiye mukaminsa. A cewarsa, rawar da gwamnati take iya takawa shi ne, ta ƙarfafa zaman lafiya, sannan ta tabbatar an bi doka da oda a cikin al’umma. Ya ce abubuwa da gwamnati ke lura da su shi ne, al’umma ta mori zaman lafiya domin bunƙasar tattalin arziki da sauran su.  Tunda farko a jawabinsa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Hon. Nasiru Mu’azu Danmusa ya bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya rage ƙarfin harkokin rashin tsaro a Jihar Katsina....
    Bugu da kari, Han ya ce, zamanantar da aikin gona da raya yankunan karkara tana da matukar muhimmanci a cikin aikin zamanantarwa irin ta kasar Sin, saboda haka ya kamata a ba wannan bangare fifiko. Ya ce shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar na jaddada bukatar mai da raya harkoki masu alaka da aikin gona da raya yankin karkara da kyautata rayuwar manoma, a matsayin abu mai matukar muhimmanci, da tabbatar da bunkasar birane da yankin karkara na bai daya, da kuma hanzarta wajen inganta karfin kasar a fannin raya aikin gona.   A yayin taron, direktan hukumar raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin, Mr. Zheng Shanjie ya bayyana cewa, “kirkira da habaka sabbin abubuwa” na nufin habakawa...
    Ofishin kula da ayyukan binciken sararin samaniya na ’yan sama jannati, ya ce za a harba kumbon Shenzhou-21 a lokaci mai dacewa a kwanan nan. Yana mai cewa an riga an kai kumbo da rokar da za ta harba kumbon, zuwa wurin harbawa a yau Jumma’a. A cewar ofishin, an kai kumbon Shenzhou-21 da zai dauki ’yan sama jannati da kuma rokar Long March 2F Yao-21 mai dauke da kumbon zuwa wurin harbawa a yau Jumma’a. A halin yanzu, kayayyakin aiki a wurin harba kumbon suna cikin kyakkyawan yanayi. Kana za a gudanar da bincike daban daban da kuma gwaje-gwajen hadin gwiwa kamar yadda aka tsara kafin harbawa. Bisa shirin da aka tsara, za a harba kumbon a wani lokaci...
    Kasar Iran ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai ta sama kan yankunan kudancin Lebanon da kwarin Beka’a na kasar. Baqa’i ya bayyana hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kai a ranar Alhamis a yankunan kudancin da kwarin Beka’a na Lebanon, wadanda suka yi sanadiyyar shahada da kuma raunata wasu fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da dalibai a wata makaranta a kwarin Beka’a, tare da bayyana harin a matsayin “laifi na ta’addanci” kuma ya yi suka mai tsanani kan su. Baqa’i ya gabatar da alhini da...
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasashen Yamma sun taka dokokin kasa da kasa a batun Iran Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov ya soki matakan ƙasashen Yamma, ciki har da harin soji da suka kai wa Iran da kuma ƙoƙarinsu na sake Sanya mata takunkumi, yana mai cewa, “A wannan yanayin, ƙasashen Yamma sun taka dokokin ƙasa da ƙasa.” Jaridar Kommersant ta ruwaito cewa: Ryabkov ya yi waɗannan kalaman ne a lokacin wani shirin yanar gizo mai taken “Tarihi da Siyasar Yanzu na Manufofin Nukiliya na Rasha da Diflomasiyyar Jama’a a Bangaren Nukiliya,” wanda Cibiyar Makamashi da Tsaro ta shirya. Yayi nuni da cewa: “Yanayin Iran, ƙasashen Yamma sun taka dokokin ƙasa da ƙasa...
    Shugaban kasar Amurka Trump ya ce: Za su dauki matakin soji kan kasar Venezuela nan ba da jimawa ba Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da cewa kasarsa za ta iya fara yaki da “masu safarar miyagun kwayoyi nan ba da jimawa ba,” yana mai cewa, “Za su dauki mataki ta hanyar kutsawa ta kasa a kasar Venezuela,” yana mai nuni da yiwuwar shiga tsakani na soja ko ayyukan leken asiri. A martanin da ya mayar, Shugaba Trump daga baya ya musanta rahotannin cewa: Jiragen yakin Amurka sun yi shawagi a kusa da kan iyakar Venezuela, yana mai jaddada cewa: “Ba gaskiya ba ne cewa: Amurka ta aika da jiragen yakin sama kusa da Venezuela.” Trump ya shaida wa...
    Gwamnatin kasar Iraki ta yi Allah wadai da matakin da Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta dauka na mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da kuma gine-gine matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Iraki ta bayyana Allah wadai da amincewa da kudurorin biyu na Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta yi da su da nufin sanya kwace iko da mallakar yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma gudanar da matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba. Ma’aikatar ta ce a cikin wata sanarwa cewa: “Tana bayyana kakkausar suka da Iraki ta yi kan amincewar da Majalisar Dokokin Isra’ila ta yi da kudurorin biyu da nufin kwace iko da mallake yankin Yammacin...