Hamas : Ba za mu bari Isra’ila ta sami wata hujja ta ci gaba da yaki a Gaza ba
Published: 26th, October 2025 GMT
Kungiyar gwagwamaryar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa ba za ta bari Isra’ila ta samu wata hujja ta ci gaba da yaki a Gaza ba.
Khalil al-Hayyah jigo a kungiyar ta Hamas, ya nuna gazawar gwamnatin Isra’ila na cimma burinta a Gaza kuma ya bayyana cewa kungiyar tana mutunta dukkan alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ba kuma ba za ta bari makiya su sami hujjar ci gaba da yakin ba.
al-Hayyah, shugaban ofishin siyasa na Hamas a Gaza, ya bayyana a wata hira da tashar Al Jazeera cewa gwamnatin Isra’ila ta gaza cimma duk wani burinta a lokacin yakin kuma Hamas za ta yi duk mai yiwuwa don hana sake barkewar yaki.
Da yake magana kan matsayin gwamnatin Amurka na baya-bayan nan, ya bayyana cewa shugaban Amurka Donald Trump da sauran jami’ai a Washington sun tabbatar da kawo karshen yakin kuma dole ne a daidaita wannan tsari.
A cewar jami’in na Hamas, cikin awanni 72 da tsagaita wutar, an mika fursunonin Isra’ila 20 da gawawwaki 17 daga cikin jimillar fursunonin Isra’ila 28.
Ya kuma sanar da cewa za’a kara shiga yankunan don dawo da sauran gawawwakin.
Al-Hayyah ya jaddada cewa za a damka wa Kwamitin Gudanarwa na Gaza alhakin gudanar da harkokin yankin, kuma kungiyar ba ta da wata adawa da hakan.
Saidai a cewar wannan babban jami’in na Hamas, Isra’ila na ci gaba da hana shigar da kayayyaki da kayan agaji da ake bukata a zirin, a yayin da Hamas ta sanar da fara aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yan Ivory Coast na jiran sakamakon zaben shugaban kasa October 26, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Shugaban Amurka Zai Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rudu October 26, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Ce: Iran, Rasha Da China Sun Aike Da Sako Mai Muhimmanci October 26, 2025 Ja’afari: Iran Tana Da Isassun Makamai Masu Linzami Masu Cin Zangogi Daban-Daban October 26, 2025 Dan Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ya Ce: Dole Ne A Hakunta Isra’ila Kan Laifukan Da Ta Aikata October 26, 2025 Mayakan Kungiyar Kurdawa Ta PKK Sun Fice Daga Turkiyya Zuwa Iraki October 26, 2025 Iran Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kungiyar Tattalin Arziki TA “Eco” A Gobe Litinin October 26, 2025 Bahrain: Fursunoni 90 Suna Yajin Cin Abinci Saboda Neman ‘Yanci October 26, 2025 Shugaban Kasar Nigeria Ya Yi Sauye-sauye A Rundunonin Sojan Kasar October 26, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Taron Sherme-Sheikh Ne Saboda Kar Ta Zama Mai Shaidar Zur Akan Kisan Kiyashin Gaza October 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Kwallon Kafa Ta Futsal Ta Matan Iran Sun Sami Nasara Akan Kasar Bahrain
Kungiyar kwallon kafa ta “Futsal” ta matan Iran ta zura kwallaye 14-0 a wasan da ya hada ta da takwararta ta kasar Bahrain mai masaukin baki.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka bude wasannin nahiyar Asiya na kwallon kafar Futsal a kasar Bahrain. A wasan farkon, kungiyar ta Iran ta sami nasara akan takwararta ta Hong kong ta hanyar zura kwallaye shida.
Wasa na biyu da Iran din ta yi shi ne da kungiyar kasar Bahrain, da ta sami galaba da kwallaye 14 da 0.
‘Yan wasan na Iran sun kunshi Fatima Shukrani, Niyayash Rahmani, Dhanaz Bakiri, Haidis Yari da kuma Narjis Amir Muhsini.
Ya zuwa yanzu dai kungiyar kwallon Futsal ta Iran tana da maki 6 kuma ita ce a kang aba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Antonio Gutrress: MDD Tana Bukatuwa Da A Yi Ma Ta Kwaskwarima October 25, 2025 Lebanon: An Sami Shahidai 3 Sanadiyyar Hare-haren HKI A Kudancin Lebanon October 25, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Isra’ila Kan Kasar Lebanon October 24, 2025 Rasha Ta Jaddada Cewa: Kasashen Turai Sun Taka Doka Kan Batun Makamashin Nukiliyar Iran October 24, 2025 Ayatullahi Khatami Ya Ce: Shugaban Kasar Amurka Trump Dan Ta’adda Ne October 24, 2025 Shugaban Amurka Ya Ce: Za Su Dauki Matakin Soji Kan Kasar Venezuela Nan Gaba Kadan October 24, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Yi Allah Wadai Da Mamaye Yankin Yammacin Kogin Jordan Na Falasdinu October 24, 2025 ‘Yan Sandan Kasar Ghana Sun Tseratar Da ‘Yan Najeriya 57 Da Aka Yi Fasakwaurinsu October 24, 2025 Trump Ya Dakatar Da Tattaunawar Kasuwanci Da Kasar Canada October 24, 2025 Gaza: Tasirin Rashin Abinci Mai Gina Jiki Da Magani Zai Ci Gaba Har Zuriya Mai Zuwa October 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci