Jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana
Published: 22nd, October 2025 GMT
Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa a nahiyyar Afirka (CAF) ta fitar da sunayen ‘yan takarar da za su lashe kyautar CAF ta shekarar 2025 – rukunin maza.
Cikin wata sanarwa da CAF ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce an yi la’akari da rawar da ’yan wasa da masu horarwa suka taka wajen bunƙasa kwallon ƙafa a nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya.
Hukumar ta ce fitattun masu takarar sun ba da muhimmiyar gudunmawa a fagen tamaula wanda za a yi la’akari da rawar da suka taka a tsakanin ranar 6 ga Janairu zuwa 15 ga Oktoba, 2025.
Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi IIA cikin jerin ’yan wasan nahiyyar Afirka da ke takarar lashe gwarzon shekara na Hukumar CAF akwai sunan ɗan wasan gaban tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Victor Osimhen da ɗan wasan gaba na Masar da Liverpool Mohamed Salah, da kuma ɗan wasan baya na Morocco da Paris Saint-Germain, Achraf Hakimi.
Sauran ‘yan takarar sun haɗa da ɗan wasan tsakiya na Kamaru, Frank Anguissa, da Fiston Mayele na Congo, da Denis Bouanga na Gabon, da Serhou Guirassy na Guinea, da Oussama Lamlioui na Morocco, da ‘yan wasan Senegal biyu Iliman Ndiaye da Pape Matar Sarr.
“Tasirin ’yan wasa da masu horar da ‘yan wasa a wasan Afirka da na duniya ya karu sosai a tsawon lokacin da ake yin la’akari da ranar 6 ga Janairu zuwa 15 ga Oktoba 2025, kuma wadannan sunayen nade-nade na nuna wadanda suka ba da babbar gudunmawa ga kwallon kafa a nahiyar,” in ji CAF.
Hukumar ta ce, kwamitin ƙwararru da ya ƙunshi mambobin kwamitin fasaha da ci gaba na CAF, da ƙwararrun koci-koci, CAF Legends da kuma zababbun wakilan kafofin yada labarai, sun yanke shawarar zabar mutane 10 da za a zaba a kowane fanni bisa la’akari da irin rawar da suka taka a dukkan gasa.
Dan wasan Nijeriya, Stanley Nwabali, shi ma an zaɓe shi a matsayin mai tsaron gida na shekara, wanda zai fafata da Yassine Bonou na Morocco, Ronwen Williams na Afirka ta Kudu, Andre Onana na Kamaru, Edouard Mendy na Senegal a takarar mai tsaron gida mafi kyawu na shekara.
Sauran rukunan kyaututtukan sun haɗa da Gwarzon Dan Wasan Interclub, Koci Na Shekara, Gwarzon Matashin Dan Wasan Shekara, Gwarzon Dan Wasan Kasa, da Gwarzon Kulob.
Ga jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana:
Andre Frank Zambo-Anguissa (Cameroon/Napoli)
Fiston Mayele (DR Congo/Pyramids)
Mohamed Salah (Egypt/Liverpool)
Denis Bouanga (Gabon/Los Angeles FC)
Serhou Guirassy (Guinea/Borussia Dortmund)
Achraf Hakimi (Morocco/Paris Saint-Germain)
Oussama Lamlioui (Morocco/RS Berkane)
Victor Osimhen (Nigeria/Galatasaray)
Iliman Ndiaye (Senegal/Everton)
Pape Matar Sarr (Senegal/Tottenham Hotspur)
Ga jerin ’yan wasan da ke takarar gwarzon mai tsaron raga:
Andre Onana (Cameroon/Trabzonspor)
Vozinha (Cape Verde/Chaves)
Ahmed El Shenawy (Egypt/Pyramids)
Munir Mohamedi (Morocco/RS Berkane)
Yassine Bonou (Morocco/Al Hilal)
Stanley Nwabali (Nigeria/Chippa United)
Edouard Mendy (Senegal/Al Ahli)
Marc Diouf (Senegal/Tengueth)
Ronwen Williams (South Africa/Mamelodi Sundowns)
Aymen Dahmen (Tunisia/CS Sfaxien)
Ga jerin masu horaswa da ke takarar gwarzon koci na shekara:
Bubista (Cape Verde)
Hossam Hassan (Egypt)
Krunoslav Jurcic (Pyramids)
Sami Trabelsi (Tunisia)
Romuald Rakotondrabe (Madagascar CHAN)
Moine Chaabani (RS Berkane)
Tarik Sektioui (Morocco CHAN)
Mohamed Ouahbi (Morocco U-20)
Walid Regragui (Morocco)
Pape Thiaw (Senegal)
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: da ke takarar la akari da
এছাড়াও পড়ুন:
Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20 October 19, 2025
Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin October 19, 2025
Daga Birnin Sin Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka October 19, 2025