“Shirin gwamnan na aiwatar da sabon tsarin albashi duk da ƙalubalen tattalin arziki ya nuna tausayinsa, gaskiya, da girmama kimar ma’aikata,” in ji shugabannin kungiyoyin.

 

Kungiyoyin sun kuma yaba da kokarin gwamnatin wajen gyara da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya inda suka bayyana gyaran da sabunta azuzuwan karatu a dukkan kananan hukumomi 23, amincewa da tsarin ritaya bayan shekaru 65 ko shekaru 40 na aiki ga malamai, da kuma dawo da sama da naira miliyan 500 na ajiyar ( ENDWELL) da aka rike a baya, a matsayin muhimman nasarori.

 

Ma’aikatan sun kara jinjina wa dawowar tsarin biyan gudunmawar adashin gata na malaman makaranta wato (ENDWELL) na kowane wata, inda suka bayyana cewa tsarin yana taimakawa wajen inganta walwalar malamai da iyalansu. Haka kuma sun yaba da gyaran da gwamnati ta yi wajen biyan kudin kungiyoyi da kuma nasarar tantance ma’aikata wanda ya kara gaskiya da tsari a cikin aikin gwamnati.

 

A fannin lafiya, kungiyoyin sun yaba da sauye-sauyen da Gwamna Uba Sani ya aiwatar, ciki har da farfado da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 255 (PHCs), kafa cibiyoyin kwarewa guda 23 na PHC, da kuma shirin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 a duk shekara na tsawon shekaru biyar.

 

Haka kuma shugabannin ma’aikatan sun jinjina wa gwamnan bisa kaddamar da motocin bas masu aiki da iskar gas (CNG) guda 100 domin bayar da kyautar sufuri ga ma’aikata da dalibai, suna bayyana wannan shiri a matsayin wani mataki na taimakawa wajen rage radadin cire tallafin mai da sauƙaƙa rayuwar jama’a.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala October 24, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Tafka Ɓarna A Kasuwar Shuwaki, Ta Ƙona Fiye da Rumfuna 500 A Kano October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu October 24, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja

Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago.

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

“Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta kuma yi kira da a ƙara kulawa da tsaro, musamman wajen adanawa da jigilar kayan da ke iya kamawa da wuta cikin sauƙi.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025 Manyan Labarai An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba October 21, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna
  • DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026
  • Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 
  • Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja
  • Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447
  • Gwamna Bala Mohammed ya ƙirƙiri sabbin masarautu 13 a Bauchi
  • Uba Sani ya yi wa ma’aikatan manyan makarantu ƙarin kashi 70 a albashi
  • Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi