2025-10-17@11:48:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1910

«agajin gaggawa»:

    Majalisar Dattawan ta Najeriya  ta tabbatar da naɗin Farfesa Joash Amupitan, mai mukamin SAN, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a yammacin ranar Alhamis.  Tabbatar da Farfesa Amupitan, ta kasance ta hanyar kuri’ar murya da ‘yan majalisar suka gudanar bayan kammala tantance shi tare da amsa tambayoyi daga mambobin majalisar na tsawon kusan sa’o’i biyu. Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ne ya gabatar da sunan Amupitan, don maye gurbin tsohon shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya sauka daga mukamin makonni biyu da suka gabata. Amupitan, wanda ya samu rakiyar gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, da wasu jami’ai zuwa majalisar, ya gabatar da tarihin inda ya yi aiki kafin fara amsa tambayoyin ‘yan majalisar....
    Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki.   Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa.   Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar noma, inda ta ce, manoma mata da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da wadanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000.   Shemau ta kuma mika godiyarta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin kokarin da take yi na bunkasa noman mata a Jihar Zamfara.   Sauran hukumomin da kungiyoyin da suke tare da NAWIA...
    Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kafa ƙananan masana’antu a karamar hukumar Gagarawa. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon kayayyakin bunkasa tattalin arziki ga wasu daga cikin al’ummar Gagarawa. Malam Umar Namadi ya yi bayanin cewar, masana’antun za su hada da na sarrafa shinkafa da sauransu. Yana mai cewar hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa marasa aikin yi a yankin. Kazalika, Gwamnan yace gwamnatin jihar za ta ware kudi a kasafin kudin shekarar badi don gina hanyar mota daga Medu zuwa Dandidi zuwa Madaka, domin saukaka sufuri ga al’ummar yankin. Baya ga kaddamar da tallafin, Malam Umar Namadi, ya bude wasu ayyukan ci gaba ciki har da makarantar Tahfizul Qur’ani ta...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025
      “Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana ƙarshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.”   Lamarin ya jawo damuwa daga al’umma da shugabannin siyasa, yayin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙoƙari wajen gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi da tabbatar da zaman lafiya a yankin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025 Labarai Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku October 16, 2025 Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025
    Amupitan, wanda ya samu rakiyar gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, da wasu jami’ai zuwa majalisar, ya gabatar da tarihin inda ya yi aiki kafin fara amsa tambayoyin ‘yan majalisar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025
    Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Joash Ojo Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC, bayan tantancewa. Sabon shugaban Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC, Joash Ojo Amupitan dai ya halarci zauren  Majalisar Dattawan Najeriya domin zaman tantance shi a yau Alhamis ne. Amupitan ya halarci zauren Majalisar tare da rakiyar Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo da wasu jami’an gwamnati. Za a kafa kamfanin ƙera kayan sola a Kano Kashi 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEF Da misalin ƙarfe 12:50 na rana ne, mai baiwa shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Majalisar Dattawa (Majalisar Dattawa), Sanata Abubakar Lado ne ya shigar da sabon shugaban INEC zuwa zauren majalisar...
    Sabon shugaban Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC, Joash Ojo Amupitan ya halarci zauren  Majalisar Dattawan Najeriya domin zaman tantance shi. Amupitan ya halarci zauren Majalisar tare da rakiyar Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo da wasu jami’an gwamnati. Za a kafa kamfanin ƙera kayan sola a Kano Kashi 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEF Da misalin ƙarfe 12:50 na rana ne, mai baiwa shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Majalisar Dattawa (Majalisar Dattawa), Sanata Abubakar Lado ne ya shigar da sabon shugaban INEC zuwa zauren majalisar dattijai, kuma tuni ya zauna gabanin fara aikin tantance shi. An bar Amupitan ya shiga zauren majalisar ne bayan shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi...
    An fara tantancewar da misalin ƙarfe 12:55 na rana, inda ake sa ran Farfesa Amupitan zai gabatar da tarihinsa da kuma amsa tambayoyin da ‘yan majalisar za su yi masa, kafin yanke shawara kan tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban INEC. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025 Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025
    Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakanin kungiyar Hamas da Isra’ila, akalla Falasɗinawa uku sun rasa rayukansu a ranar Alhamis sakamakon hare-haren Isra’ila a Gaza, in ji majiyoyin lafiya a yankin. Wata hukumar gwamnatin Isra’ila ta ce zai yi wuya ta buɗe iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar don zirga-zirgar mutane. Za a kafa kamfanin ƙera kayan sola a Kano ’Yan sanda sun kama gungun masu fashi a kan hanyar Katsina zuwa Kano Tuni dai Ministan tsaron Isra’ila ya umarci rundunar sojin kasar da ta yi kwakkwaran shiri don murkushe Hamas muddin ta karya yarjejeniyar tsagaita wutar. A nata bangaren, Hamas ta mayar da gawarwakin wasu Isra’ilawa biyu da ta kama, amma ta amince cewa tana...
    Cikakkun bayanai za su biyo baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025 Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya bayyana cewa kashi 16 cikin 100 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu mai tsafta a gidajensu. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Chisom Adimorah ce, ta bayyana haka a ranar Laraba yayin bikin Ranar Wanke Hannu ta Duniya ta 2025, wanda Ma’aikatar Ruwa da Tsaftar Muhalli ta Tarayya ta shirya. DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose Adimorah, ta nuna damuwarta kan wannan matsala, inda ta ce duk mutane biyar cikin shida a Najeriya ba su da waje  da za su iya wanke hannunsu yadda ya kamata. Ta yi kira ga...
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya bayyana cewa kashi 16 cikin 100 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu mai tsafta a gidajensu. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Chisom Adimorah ce, ta bayyana haka a ranar Laraba yayin bikin Ranar Wanke Hannu ta Duniya ta 2025, wanda Ma’aikatar Ruwa da Tsaftar Muhalli ta Tarayya ta shirya. DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose Adimorah, ta nuna damuwarta kan wannan matsala, inda ta ce duk mutane biyar cikin shida a Najeriya ba su da waje  da za su iya wanke hannunsu yadda ya kamata. Ta yi kira ga...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce bai dace a ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, laifin rikicin da jam’iyyar PDP ke fama da shi ba. Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce shugabannin PDP ne suka haddasa matsalolinsu, ba Tinubu ko jam’iyyar APC ba. Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a A cewarsa, jam’iyyar PDP “ta mutu tun tuni,” kuma ba ya cikin waɗanda za su nemi farfaɗo da ita. Ya ƙara da cewa yawancin gwamnonin da suka rage a PDP na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki. “Ba daidai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai. Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba.   Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, duk da wannan sauƙin, ya kamata a yi taka-tsantsan saboda lissafi na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani da fahimtar ilimin fasaha, kimiyya da injiniya. Wannan ya sa ake tambaya ko cire lissafi daga wajabcin shiga manyan makarantu ba zai iya rage ingancin dalibai a nan gaba ba. NAJERIYA A YAU: Shin...
    Jam’iyyar ADC ta ce sauya sheƙar da wasu gwamnonin jihohi suka yi zuwa jam’iyya mai mulki ya nuna yadda Shugaba Bola Tinubu, ke ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya. A wata sanarwa da Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, ya fitar, ya ce jam’iyyun adawa ba su damu da abin da ya kira “cin amanar siyasa” da gwamnonin suka yi ba. Gwamna Inuwa ya naɗa sabbin shugabanni a ma’aikatar lafiya ta Gombe Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda Ya ce zaɓen 2027 ba zai zama takara tsakanin jam’iyyu kawai ba, sai dai ya zama gwagwarmaya tsakanin talakawan Najeriya da gwamnatin da ta jefa rayuwar...
    Yari ya bayyana cewa, matsalar tsaro a Arewa ta samo asali ne daga yadda ake amfani da albarkatun kasa da ke yankin ta hanyar da ba ta dace ba, yana kuma gargadin cewa bai kamata a dora laifi kawai a kan gwamnati ba.   “Kafafen sada zumunta suna shafar kowa mai kudi da talaka. Dole ne a tsara dokoki masu tsauri domin kare al’umma,” in ji shi   Sanata Yari ya jaddada cewa giɓin tattalin arziki tsakanin Arewa da Kudu yana kara faɗaɗa, don haka ya buƙaci al’ummar Arewa da su rungumi aikin yi, kirkire-kirkire da dogaro da kai, maimakon dogaro da taimako daga waje.   Doguwa kuwa ya kara da cewa Majalisar Tarayya tana shirye ta tallafa wa duk...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou October 15, 2025 Daga Birnin Sin Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar October 15, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles October 15, 2025
    Majalisar Dattawa za ta tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a ranar Alhamis, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Daraktan Yaɗa Labarai na Majalisar Tarayya, Bullah Audu Bi-Allah ne, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe A makon da ya gabata ne, Shugaba Tinubu, ya aike wa Majalisar Dattawa sunan Amupitam, domin ta tabbatar da naɗinsa. An karanta wasiƙar Tinubu yayin zaman majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio. A cikin wasiƙar da ya aike, Tinubu, ya ce: “Dangane...
    Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta lallasa abokiyar karawarta Benin da ci 4 da nema a wasan zagaye na 10 na neman tikitin zuwa gasar Kofin Duniya da suka buga a filin wasa na Godswill Akpabio dake birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.  Nijeriya ta jefa kwallayenta uku ta hannun dan wasan gaban Galatasaray Victor Osimhen, wannan nasarar ta janyo Nijeriya ta koma matsayi na biyu da maki 17 da kwallaye 6 a wasanni 10 da ta buga. A dayan wasan da aka buga a rukunin C Afirika Ta Kudu ta samu nasarar zuwa gasar Kofin Duniya na shekarar 2026 da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da Canada bayan ta doke kasar Rwanda da ci 3-0 a Polokwane....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abass Araqchi ya bayyana yadda wasu kasashen turai 3 suka yi amfani da yarjejeniyar JCPOA da kuma kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wajen mayar da kudurin kwamitin da aka soke shi a baya kan kasar iran, wanda ya fuskanci adawa daga kasashe da dama ciki har da mambobin biyu na dindindin a kwamitin sulhu a matsayin dokar da ta sabama doka kuma ba za ta yi tasiri a shari’a ba. Kasashen turai saboda matsin lambar Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA don haka wadannan kasashe basu da hurumin da za su ce wani abu kan jarjejeniyar,  tun da saboda su ne da Amurka dukkan yarjejeniyar ta wargaje Minista Araqchi ya bayyana cewa batun yankin...
    Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa. Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu. ’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF Lawan, wanda ya wakilci mazabar Bagwai/Shanono a Jihar Kano, yana cikin mutane 175 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa afuwa a ranar 9 ga watan Oktoba. An kama shi a shekarar 2021 bayan samun sa  da laifin karɓar cin hanci a 2012, domin cire sunan wani kamfani daga jerin...
    Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar da ta kafa asusun adashen gata na kiwon lafiya na jihar ya sahalewa asusun damar samo kudade daga wasu bangarori da ba na gwamnati ba. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan tsokaci lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a ofishin asusun da ke Dutse. Ya bayyana bukatar ganin asusun JICHIMA ya nemo kudade daga hannun masu taimakon al’umma da cibiyoyi da ‘yan siyasa da kwamitocin zakka da na waqafi domin bunkasa asusun, ta yadda zai biya bukatun kiwon lafiyar al’ummar jihar. Alhaji Usman Musari ya lura cewar fadada hanyoyin samun kudade ga...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadawa kungiyar Hamas su mika makamansu da radin kansu ko kuma zai kwance damararsu da karfi. Jaridar Daily Mails ta kasar Burtaniya ta nakalto shugaban yana fadarwa kafafen yada labarai a washinton a jiya Talata. Amma kungiyar Jihadul Islami daya daga cikin kungiyoyin da ke dauke da makamai a zirin gaza ta bakin mataimakin babban sakataren kungiyar Mohammad Al-Hindi a hirar da yayi da tashar talabijan ta Aljazeerah cewa kungiyoyi masu gwagwarmaya a gaza basu amince su mika makamansu a yarjeniyar sulhu na Trump ba kuma basu damu da barazanar shugaba Trump na kwance damarasu da karfi ba. Alhindi ya kara da cewa banda haka babu wata kalma ko guda a cikin yarjeniyar da...
    Wani babban jami’in kungiyar Hamas a gaza ya bayyana cewa HKI tana dakile kokarinda kungiyar take na nemo da kuma mayar da gawakin yahudawan Sahyoniya da suka halaka saboda barin wutan da sojojin ta suka  yi kan gaza, wanda ya kai ga mutuwar jami’ansu da suka bawa aikin kula da yahudawan. Don haka wannan ya sa suka rasa samun wadan nan jami’insu saboda sun mutu, sun kuma mutu tare da yahudawan da suke hannunsu. Kungiyar Hamas bata san a dai dai inda suke ba a lokacinda aka kashe su, don haka akwai bukatar lokaci kafin su gano wadannan mutane. Wasunsu sun karkashin burmudhin gine-gine a gaza wanda yake bukatar kwacesu kafin a kai ga gawakinsu. Don haka lai gwamnatin yahudawanne...
    Yansanda a kasar Italia sun kara da masu zanga zanga masu kuma goyon bayan Falasdinawa, don hana a gudanar da wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta HKI da kuma ta kasar Italia a filin wasa na Udine a jiya Talata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Italia ta aika yansanda fiye da 1000 guda, tare da jiragen sama masu saukar ungulu don hana masu zanga –zangar isa filin wasan. Labarin ya kara da cewa zanga-zangar wacce kwamitin masu goyon Falasdinawa ya shirya. Zanga-zangar don hana wasan ta ilimunation wato fidda goni na masuhalattar gasar duniya ta FIF 2026. Daga karshe  dai an yi gasar kuma kasar Italiya ta lallasa HKI da 3-0....
    Wasu kudurori guda 3 da ke dauke da bukatun kafa wasu hukumomi 3 sun samu karatu na biyu a zauren majalaisar dokokin jihar Jigawa. Kudurorin guda 3 sun hada da na kafa Hukumar Samar da Hanyoyin Mota a yankunan karkara, da na kafa Hukumar Samar da Kudade Domin Ayyukan Hanyoyin Mota a yankunan karkara da Kuma na Hukumar Bunkasa Kwazon Malamai ta jihar Jigawa. A lokacin ya ke gabatar da kudurorin domin neman goyon baya kan bukatar kafa hukumar bunkasa kwazon malamai, mataimakin shugaban masu rinjaye na majlaisar, Alhaji Sani Sale Zaburan ya ce gwamnatin jihar na da nufin inganta aikin koyarwa ta hanyar kafa hukumar da za ta rinka horas da malamai akai akai. Da su ke tattaunawa kan...
    ‘Yansanda sun kuma samu kuɗi Naira 92,460 da wasu abubuwan maye kamar giya da sauransu. “Wannan samame sakon gargaɗi ne ga duk masu hannu a fataucin miyagun ƙwayoyi,” in ji SP Adam. “Yaƙinmu da fataucin miyagun ƙwayoyi yana ci gaba, kuma muna kira ga jama’a su riƙa sanar da mu duk wani abin da suka gani na zargi.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara October 15, 2025 Manyan Labarai Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima October 15, 2025 Labarai Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria  October 14, 2025
    Iran ta kai hari a wani sansanin sojan Isra’ila na sirri da ke karkashin wata hasumiya a Tel Aviv Yankin Gray, wani dandali ne na bincike, ya bayyana samuwar wani maboyar sirri na sojan Isra’ila da ke karkashin wani hasumiya a Tel Aviv, wanda ake kyautata zaton yana cikin wadanda aka kaiwa hari da makami mai linzami na Iran yayin harin da aka kai ranar 13 ga watan Yuni. Bisa binciken da aka gudanar, dandalin ya gano wurin da wani wurin karkashin kasa da aka fi sani da “Site 81”, wani rukunin jami’an leken asiri na hadin gwiwar sojojin Amurka da Isra’ila da ke karkashin rukunin gidaje na Da Vinci a wata unguwa mai yawan jama’a a tsakiyar birnin Tel...
    Babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ya jaddada cewa: ‘Yantar da sauran fursunonin manufa ce da ba za ta fice daga muhimman abubuwan da suka aka sa a gaba ba Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Jihadul- Islami ta Falasdinu, Ziyad al-Nakhalah, ya tabbatar da cewa: Ba za a taba mantawa da manufar ‘yantar da sauran jajirtattun fursunonin Falasdinu daga gidajen yarin ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya ba saboda yana daga cikin muhimman abubuwan da ‘yan gwagwarmaya suka sa a gaba. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Today cewa: Kwamandan al-Nakhalah ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar litinin cewa: Tutocin gwagwarmaya suna ci gaba da wanzuwa a kasa...
      A nata bangare, Sima Bahous ta yabawa ci gaban da Sin ta samu wajen cike gibin fasahohi tsakanin jinsi, da ingiza ci gaban harkokin mata ta kowanne bangare da kare hakkoki da muradun mata.   Ta kuma yi kira ga kasa da kasa su hada hannu tare wajen karfafa gwiwar mata da ‘yan mata su samu ci gaba a zamanin amfani da fasahohi. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa  October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025 Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025 Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata October 14, 2025
      Ta ce shawarwari hudu da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, duk suna kira ne da a yi hadin gwiwa don tabbatar da daidaiton jinsi, ya zama bai daya cikin manyan batutuwa da ya dace a tattauna a duniya. Ana bukatar karin ayyuka, kuma ba shakka wannan taro yana da matukar muhimmanci.   A nata bangare kuwa, wakiliyar kasar Tanzaniya Juliana Kibonde, cewa ta yi, an saurari jawabin shugaba Xi Jinping, wanda ke da matukar muhimmanci ga kasashen Afirka. An kuma lura da yadda za a ba mata ikon ci gaba a fannoni kamar na fasaha, da siyasa da sauyin yanayi. Kazalika, shugaba Xi ya ambaci batun gibin dijital, kuma ana iya fahimtar cewa, wasu kasashe suna...
    Al’ummar yankin sun bayyana cewar matsalar tsaron ta gurgunta tattalin arzikin yankin musamman ayyukan noma wanda ya sa ɗaruruwan mutane da dama neman mafaka a sansanin gudun hijira a Sakkwato da makwabtan jihohi.   Dasuki ya bayyana cewar a ranar 12 ga Augusta 2025, ‘yan ta’adda sun shiga mazaɓar Fakku a karamar hukumar Kebbe tare da kashe mutane biyar da garkuwa da mutane 28 da satar shanu 37.   “Haka ma a ranar 15 ga Agusta, ‘yan bindigar  sun kai farmaki mazaɓar Sangi tare da tilastawa jama’a neman mafaka a Kuchi da Koko a jihar Kebbi. Bugu da kari a ranar 18 ga Agusta ‘yan ta’adda sun afkawa mazabar Ungushi tare da kisan mutane biyu da garkuwa da mutane bakwai...
    Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad ta yi maraba da sako Falasdinawa kusan 2000 daga gidajen yarin Isra’ila, tare da cewa jarumtakar mayakan gwagwarmaya da hadin kan al’ummar Falasdinu ne ya haifar da wannan babbar nasara. A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ziyad al-Nakhalah ya fitar ya bayyana cewa, wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta samo asali ne sakamakon jajircewa da tsayin daka da hadin kan al’ummar Falasdinu, wanda idan ba tare da hakan ba yarjejeniyar ba za ta taba cimma ruwa ba. Bayan shafe sama da shekaru biyu ana kai hare-hare ba kakkautawa wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatan Falasdinawa, gwamnatin Isra’ila bisa matsin lambar kasa da kasa ta amince da yarjejeniyar da Amurka ta kulla...
    SP Shiisu ya ce bincike na ci gaba domin gano musabbabin ɓarkewar rikicin. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ƙara haɗa kai da jami’an tsaro da kuma gaggawar bayar da rahoto idan suka lura da wani abin da zai iya janyo rikici, domin kauce wa zubar da jini. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi October 14, 2025 Manyan Labarai Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa October 14, 2025 Labarai ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara October...
    Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki. Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin da ma’akatan agajin suka shafe kimanin awa hudu ba su motsa ba saboda luguden bamabaman. Kwamandan hukumar soji da ke yankin ta bayyana cewa an kona motoci hudu tare da lalata wata a cikin tawagar kayan agajin, amma ba a samu asarar rayuka ba a harin da aka kai da jirage marasa matuka da manyan bindigogin atilare a garin Bilozerka. Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donal Trump a cikin majalisar dokokin HKI a jiya Litinin inda ya bayyana cewa HKI ta sami nasara a yakin da ta kaiwa JMI a cikin watan Yunin da ya gabata, sannan daga karshe ya ce akwai bukatar a cimma yarjeniya da JMI kan shirinta na makamashin Nukliya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na cewa jawabin Trump a majalisar Knesset jawabi ne wanda bai da wani kima. Musamman a lokacinda yake gabatar da ita a gababan yan ta’adda makasa. Ma’aikatar ta tunatarwa Trump har yanzun tana jirin randa za’a gabatar da shi a gaban kuliya kan kissahn Janar shahida Qasim Sulaimani, wanda...
    Duban dubatan mutane sun gudanar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da kuma yin tir da kokarin samar da huldar jakadanci da HKI a maida kome kamar ba abinda ya faru. Sun kuma bayyana tsagaita wutan da aka samar da Hamas tana tangal tangal saboda tun farko ba’a gina shi kan yadda zata dore ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zanga suna cewa, wannan sulhun da kasashen yamma suka kulla da Hamas wani makirci ne na kara samun iko kasashen musulmi da ma wasu kasashen wadanda ban a musulmi ba. Sun kuma bayyana cewa, bayan shekaru biyu da kissan kiyashi sun samar da abinda suka kira sulhu ne na wani lokaci, amma zaman lafiya ba zata taba...
    Tsohuwar mai bai wa Basshar Asad na Syria shawara, Busaina Sha’aban ta kore gaskiyar labarin da aka rika watsawa na cewa ta yi wata ganawar sirri da jami’an kasashen Iran, Iraki da Lebanon tare da Basshar Asad. Busaina Sha’aban ta kuma ce ba ta yi managa da tsohon shugaban kasar ta Syria Basshar Asad ba akan labarun karya da aka watsa na cewa ya gana da jami’an dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran, ko kuma batun kafa sansanonin kungiyar al’ka’ida. Ta kuma kara da cewa a tsawon rayuwarta ba ta taba ganawa da Shahid janar Kassim Sulaimani ba,ko shugaban rundunar “Hashdussha’abi” na janar Shahid Abu Mahdi al-muhandis. Tsohuwar mai bai wa shugaban kasar ta Syria ta kuma ce;...
    “Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah Ya kawo dama ta afuwa, dole ne ya yi farin ciki. Ni da iyalina da masoyana mun yi murna ƙwarai,” in ji Lawan. “Na gode wa Allah da kuma Shugaba Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata a yaba masa.” Ya bayyana cewa rayuwa a gidan yari ta koya masa juriya da fahimtar cewa komai ƙaddara ce. “Tun kafin na bar kotu na sallama komai ga Allah. Na sani cewa duk inda mutum ya samu kansa, akwai darasi a ciki,” in ji shi. Bayan fitowarsa daga gidan yari, Faruk Lawan ya sauya tafiyarsa ta siyasa. Ya ce ya rabu da tafiyar Kwankwasiyya da aka san shi da ita, duk da cewa har...
    Rahotanni sun bayyana cewa wani ƙazamin faɗa ya barke tsakanin wata ƙabilar Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da ƙungiyar Hamas a yankin zirin Gaza bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila. A ranar Litinin da aka fara musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ne rahotanni suka ɓulla game da faɗan da ya ɓarke tsakanin mayaƙan Hamas da ƙabilar Doghmush a ranar Lahadi. Wani jami’in Hamas ya bayyana cewa an samu asarar rayuka daga kowane ɓangare a yayin musayar wutan daga misalin ƙarfe 9.30 na dare ranar Lahadi. Wani mazaunin yankin Sebra da ke Birnin Gaza, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa “Mayaƙan Hamas kimanin 200 ne suka zo aka fafata da su, har sai da suka...
    Sakataren Majalisar Koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana haka ne a  wani sako da ya walalfa a shafinsa na sadarwa dangane da sako fursunonin Falasdinawa da aka yi. Haka nan kuma ya ce: ‘Yan Sahayoniya sun ga hotunan gagarumin tarbar da aka yi wa Fursunonin Falasdinawan da hakan yake sake tabbatar da cewa; Kungiyar Hamas da gwagwarmaya suna da karbuwa da farin jini a tsakanin Falasdinwa bayan gushewar shekaru biyu na kazamin yaki. A jiya da safe ne dai al’ummar Falasdinu su ka tarbi Falasdinawan da aka HKI ta sako daga gidajen kurkukunta a karkashin yarjejeniyar kawo karshen yaki da ta kunshi musayar fursunoni. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up...
    Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye. Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na ƙuri’u a rumfunan zaɓe da dama. Sun buƙaci Shugaba Paul Biya, wanda ke neman wa’adin mulki na takwas a zaɓen da ya gaggauta miƙa saƙon taya murna ga Issa Bakary Tchiroma. “Muna kira ga shugaban ƙasa mai barin gado da ya gaggauta taya sabon shugaban ƙasa murna,” in ji ƙungiyar,” in ji wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Anicet Ekane da Djeukam Tchameni, suka fitar a...
      Dangane da gamsuwa kan nasarorin da Sin ta samu a bangaren raya harkokin mata, kaso 72.8 na masu bayar da amsa a nazarin daga kasashe maso tasowa, sun yaba da kokarin Sin na horar da mata sana’o’i da tallafawa raya harkokin da suka shafe su. Game da nasarorin da aka samu a kasar Sin wajen shigar mata cikin harkokin raya tattalin arziki da zaman takewa da al’adu, da ma gudunmuwar kasar ga raya harkokin mata a duniya, wadanda suka bayar da amsa daga nahiyoyin Afrika da Asia da kudancin Amurka, sun bayyana gamsuwa matuka.   Kafar yada labarai ta CGTN da jami’ar Renmin ta Sin ne suka gudanar da nazarin wanda ya shafi muhimman kasashe masu ci gaba da...
    Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara himma wajen aikin al’umma (CSR), tana taimakawa hukumomi masu ruwa da tsaki da al’ummomi domin karfafa zaman lafiya da tattalin arziki. A cewar Issa-Onilu, wannan nasara da aka samu a watan Satumba na nuna cewa hukumar Customs ba wai kawai tana cigaba da gyara ba ce, har tana kafa sabon ma’auni na kwarewa da ingantaccen aiki a tsarin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa...
    A yau litinin ne kungiyar Al-qassam brigades bangaren soji na kungiyar Hamas ta mika yahudawa guda 7 daga cikin guda 20 da ta kama su take rike da su ga hukumar kula da bada a gaji ta duniya a yankin Gaza Kungiyar hamas ta cika alkawarin da ta dauka na mika sauran mutane da take tsare da su  domin nuna gaskiyar aniyarta na kulla yarjejeniyar zaman lafiya da tsaro a yankin Gaza, duk da yake cewa Isra’ila ta kafa  tarihin cin amana da rashin cika alkawari kan duk wata yarjejeniya da aka kulla tsakaninta da alummar falasdinu. Wannan shi ne zangon farko na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma bayan shiga tsakani da aka yi a sharma El-shaikh...
    Shugaban kasar iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana a yau a wajen taron da yayi da gwamnoni jihohin kasar baki daya cewa jamhuriyar musulunci ta iran tana da karfin  juriewa duk wata matsin lamba kuma ba zata taba risunawa duk wani nuna karfi ko cin zarafi ba. Yace kasa kamar iran mai makwabta 16 ba abu ne mai sauki a kakaba mata takunkumi ba, idan muka kara gyara dangantakarmu da makwabtanmu cin sauki zamu iya shawo kan matsin lambar da muke fuskanta, Har ila yau ya kara da cewa ba zasu sa ido kan iyakokin ko wacce kasa ba, amma zamu rufe ido kan duk kasar da ta nemi shiga harkokin kasar ba tare da bata lokaci ba, Iran tasha nanata...
    Zamu kawo muku cikakken bayani idan sun bayyana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA October 13, 2025 Labarai Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi  October 13, 2025
    A hakila, sha’anin yawon shakatawa na fadada hanyoyin samun kudi ga mutanen Xinjiang.   Alkaluman da hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta Xinjiang ta samar sun shaida cewa, a yayin hutun bikin murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a kwanakin baya, yankin ya karbi baki masu yawon shakatawa sama da miliyan 18, adadin da ya karu da kashi 11.26% idan aka kwatanta da na bara, kudin da bakin suka kashe ya kai fiye da Yuan biliyan 25, kwatankwacin dalar Amurka sama da biliyan 3.5, wanda kuma ya karu da kashi 11.71%. Hakan ya nuna cewa, aikin yawon shakatawa na Xinjiang yana da makoma mai kyau.   A watan Mayu na wannan shekara, an fitar da “Shirin raya...
    Wani mummunan rikicin ƙabilanci a ƙaramar hukumar  Birniwa ta jihar Jigawa ya yi ajalin mutane biyu, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka. Kakakin ’yan sanda ta jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin Operation Salama sun garzaya wurin domin dawo da zaman lafiya tare da cafke wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a rikicin. Ganau sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wasu da ake zargin Fulani ne suka kai farmaki ƙauyen Dagaceri, inda suka ƙona gidaje tare da kai wa mazauna garin hari da kibau a lokacin da suke barci. Rahotanni sun ce gidaje da dama sun ƙone...
     Magu ayyukan ceto a gaza sun gano gawakin Falasdinawa fiye da 320 a karkashin burbushin gine-ginen da aka rusa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tun bayan fara yakin tufanul Aksa shekaru biyu da suka gabata Falasdinawa kimani fiye da 10,000 suka bace. Kuma a zatun mafi yawansu suna bisne a karkashin burbushi na gine-ginan da HKI ta rusa a kansu a zikin gaza. Asbitoci a gaza ya zuwa yansu sun bada sanarwan karban gawakin Falasdinawa 323 wadanda aka zakulo karkashin burbushin gine-gine. Da HKI ta rusa a kansu. Labarin ya kara da cewa a lissafin MDD ya zuwa tsagaita budewa juna wuta a gaza HKI ta rusa gidajen falasdinawa 430,000 a gaza. Banda haka akwai...
    Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta. Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako. Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista...
    Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta. Ya kara da cewa: Mutane 170,000 marasa lafiya da kuma wadanda suka jikkata na bukatar tafiya cikin gaggawa zuwa wajen Gaza domin neman magani. Al-Nasser Medical Complex ya kuma ce: Yara 5,500 na bukatar magani a wajen Gaza. Daraktan asibitin yara na Nasser Medical Complex, Dr. Ahmed Al-Farra, ya bayyana cewa, akwai yara 5,500 a zirin Gaza da ke bukatar agajin gaggawa a wajen yankin...
    Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa. Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama. A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin. Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi. Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce kasar Iran ta yi maraba a tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo karshen kisan kiyashi wa Falasdinawa, amma ya kara da cewa HKI ba abar amincewa bace, don haka tana iya yaudara da kuma kawo karshen tsagaaita budewa junan wutar gaba daya. Abu ne da saba yi don haka Falasdinawa su yi hattara. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa, Iran tana maraba da dukkan abinda zai kai ga kawo karshen kisan kiyashi a gaza, wanda ya dau shekaru 2 ana yi. Ministan ya jawo hankalin Hamas da sauran Falasdina kan amincewa da duk abin HKI...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Makaie ya tir da HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a kudancin kasar, Lebanon wanda ya sabawa da farko yarkeniyar tsagaita wutan da ta cimma da kungiyar Hizbulla a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 sannan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Baghaei ya bayyana cewa ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon a kai a kai, da kuma shirun da kasashen duniya suka yi duk sun sabawa dokokin kasa da kasa wadanda HKI da wadanda suke riya daukar nauyin kola da cewa an dabbaka yarjeniyar MDD na kuduri mai lamba 1107. Ya zargi kasashen Faransa da kuna Amurka wadanda suka gabatar da kansu a matsayin masu lamuni don aiwatar...
      Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) ta tabbatar da cewa ta dauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin inda aka aike da wani jirgin sama daga Legas domin jigilar tawagar zuwa Uyo, sai dai lamarin ya haifar da tsaiko a shirin da tawagar ta ke yi na tunkarar jamhuriyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0 October 9, 2025 Wasanni Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025 Wasanni Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni October 6, 2025
      ‘Yan sa’o’i kafin sanarwar da Jam’iyyar ta RN ta yi ne dai, tsohon Firaministansa Edouard Philippe ya ce yana goyon bayan shirya sabon zaben shugaban kasa a gaggauce.   Wannan matsin lamba dai kari ne kan wadda shugaban na Faransa ke fusakanta daga bangaren masu sassaucin ra’ayi, wadanda su kuma bukatarsu ita ce a zabi sabon Firaminista daga cikinsu.   Sai dai a iya cewa akwai ragowar fatan kawo karshen rudanin da siyasar Faransar ta shiga, la’akari da bayanan da suka ce a dazu an shiga tattaunawa tsakanin jagoran jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya Bruno Retailleau da Firaminista Lecournu, kwana guda bayan murabus din da ya yi. Yayin da kuma a gefe guda rahotanni suka ce a gobe...
      Ba abin mamaki ba ne cewa tsaro shi ne babban ƙalubalen da jihar Zamfara ta daɗe tana fama da shi. Daga Maradun zuwa Shinkafi, daga Anka zuwa Zurmi, matsalar ‘yan bindiga ta yi ƙatutu na tsawon shekaru.   Da yake karɓar mulki, Gwamna Dauda Lawal ya sanar da cewa “ba za a iya gina tattalin arziki ba idan tsoro ya mamaye ƙasa.”   Tun daga farkon watannin mulkinsa, ya kafa Kwamitin Tsaro na Musamman, wanda ke haɗa jami’an soja, ‘yan sanda, NSCDC da ‘yan sa-kai. Gwamnatin ta samar da motocin sintiri sama da 500, da kayan aikin zamani ga jami’an tsaro.   Har ila yau, an kafa Command and Control Centre a Gusau domin sa ido kan al’amuran tsaro...
    Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata. Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum. Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran...
    Bayanan da suka fito daga kasar Indunusiya sun nuna cewa gwammnatin kasar ta ki bada visa ga tawagar wasan jiminastik din HKI da aka shirya za’a yi wasa a birnin Jakarta a wannan watan, domin nuna rashin amincewa da kisan kare dangi da HKI ke yi a yankin Gaza. Wannan matakin yana kara nuna irin yadda batun kisan kiyanshin gaza yayi tasiri sosai hatta a harkar wasanni, kasar dake da yawan musulmi tana aikewa da sako na siyasa ne ta hanyar takawa yan wasan isra’ila birki, da kuma neman goyon bayan duniya ga alummar falasdinu. An tsara cewa tawagar wasan Jemanastik din HKI ta za shiga gasar jiminastik na duniya da za’a yi a Jakarta daga ranar 19-25 ga wannan...
      “Abin takaici ne ace Nijeriya tana karancin Mlaman makaranta da suka kai 194,876 a makarantun gwamnati a fadin tarayyar Nijeriya. Halin da makarantunmu na Sakandare suke ciki shi ma lamarin bata canza zane ba. Rashin isassun Malamai shi ma lamarin abin damuwa ne domin kuwa sannu a hankali hakan zai iya shafi samar da ingantaccen ilimi a makarantunmu kamar yadda sakamakon hakan ba zai haifar da da mai ido ba cewar, Amba”.   Don haka ya ja kunnen Nijeriya cewa rashin isassun Malaman zai iya kawo cikas wajen kokarin da Nijeriya ta ke yi na cimma muradin ci gaba na 4 (SDG 4) da ya kunshi ingantaccen ilimi ba tare da wani bambanci ba, tsakanin gwamnatoci uku ba tare...
    Bangarorin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan tsagaita bude wuta a Gaza Kungiyar Hamas, Jihad Islami, da kuma Popular Front mai fafatukar ‘yantar da Falasdinu, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a jiya Juma’a, inda suka bayyana matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, inda suka yi maraba da gwagwarmayar al’ummar Falastinu, musamman a Gaza wajen fuskantar laifukan yahudawan sahayoniyya. Kungiyoyin Hamas da na sauran kungiyoyin Falasdinu sun yaba da jarumtar gwagwarmayar da ta janyo hasara ga makiya, suna masu jaddada cewa: “Muradin jama’a da ‘yan gwagwarmaya ya fi duk wani yunkuri na murkushe su.” Har ila yau, sun jinjinawa “bangarori masu goyon bayansu a Yemen, Lebanon, Iran, da Iraki saboda goyon bayan...
    Yan sa’o’ii da janyewar sojojin HKI a wasu yankunan Gazaa aka fara gano gawakin Falasdinwa wadanda HKI ta kashe su a kan tituna da kuma karkashin burbushin gine-gine. Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza, ta bada danarwan gani gawakin shahidan Falasdinawa 17 a cikin dan karamin lokaci da janyewar sojojin yahudawa daga wasu yankuna  A Gaza. Ma’aikatar ta ce an kawo gawaki 17 da wasu 71 da suka ji rauni, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Zuwa yau jumma’a ma’aikatar ta bayyana cewa yawan mutanen da HKI ta kashe a gaza sun kai 67,211 da wasu 169,961 na wadanda suka ji rauni daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023. Labarin ya kara da cewa masu neman tallafin abinci...
    Falasdinawan da HKI ta kora daga gidajensu a birnin Gaza sun kama hanyar komawa gidajensu a birnin Gaza dake arewacin yankin Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa ya zuwa tsakiyar rana a yau jumm’a sojojin HKI sun janye makamansu daga babban titi wanda ya taso daga arewacin zirin Gaza zuwa kudancin yankin , wanda kuma ake kira Titin Rasheed. Sun janye zuwa inda aka amince zasu koma a wannan matakin na sabon yarjeniyar.  Hotunana daga yankin ya nuna falasdinawa gungu-gungu suna takawa da kafa zuwa arewacin zirin Gaza, daga inda sojojin yahudawan suka koresu a farkon watan da ya gabata, suka kuma hana kowa bin kan titin Rasheed. A wani bangare...
    Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na...
    Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Gaza Mohammad Al-Moughayyir, ya ce sojojin Isra’ila sun janye daga yankuna da dama a cikin birnin Gaza da arewacin zirin da kuma wasu yankunan kudancin yankin. A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, Motocin Isra’ila sun janye daga kudancin birnin da tsakiyar birnin zuwa yankunan gabashi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...
    Hukumar Bunkasa Ma’aikata ta Jihar Jigawa ta shirya taron karawa juna sani na kwana daya ga jami’an kula da dakunan karatu  a wani bangare na aikinta na daga darajar ma’aikata da ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu.   A jawabinsa na bude taron, Darakta Janar na MDI, Umar Farouk Wada, ya ce makasudin shirya taron shi ne don bunkasa kwarewa da sanin makamar aikin da ake da su ta yadda za a samar da ingantacciyar hidima kamar yadda Cibiyar ta tanadar.   Ya kuma bayyana cewa, za a ci gaba da gudanar da irin wannan horon ne domin a baya Cibiyar ta shirya bita ga nau’ukan ma’aikatu masu zaman kansu da na gwamnati.   Umar Farouk ya bayyana ɗakin karatu...
    Mai Magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar Palastinu a gwagwarmayar neman ‘yanci da mutunci. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mohajerani ta ce Iran za ta goyi bayan duk wani mataki ko wani shiri da zai kai ga dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza, da janyewar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila, da shigar da kayayyakin jin kai, da sakin fursunonin Falasdinu, da kuma tabbatar da hakkinsu na yau da kullun. Ta yi nuni da cewa goyon bayan Iran ga al’ummar Palasdinu “ba matsayi ne na siyasa kawai ba, a’a yana dogara ne akan  imani da ‘yancin al’ummar Palasdinu da kuma...
    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwar Shugaban Kasa ga mutane 175. Daga ciki har da wadanda aka yi wa afuwar bayan mutuwa ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da ɗan gwagwarmayar kwato ’yancin kan Najeriya, Herbert Macaulay. An dauki wannan mataki ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Gwamnatin Kano ta shirya ɗaurin auren ma’aurata 2,000 Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misis Anastasia...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025 October 9, 2025 Daga Birnin Sin Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza October 9, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar  October 9, 2025
    Rahotanni sun bayyana cewa, karar mai lamba FHC/OS/194/2024, ta nemi umarnin tilastawa INEC da shugabanta na lokacin da su sanya sunayen wasu jami’an Jam’iyyar AA a shafin hukumar na yanar gizo bayan an cire su.   Sai dai Udeze ya ci gaba da cewa, babu irin wannan hukunci ko umarnin kama shi (Yakubu), yana mai tabbatar da cewa, rahotannin ƙage ne kawai. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025 Labarai SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati October 9, 2025 Labarai An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba October 9, 2025
    Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa, sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita Najeriya. Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Yusif Bashir da motar asibiti ƙirar Toyota Land Cruiser mai lambar ONG-0777, bayan ya shigo da ita ta iyakar Babura da Jamhuriyar Nijar. Tahir, ya ce tuni hukumar ta fara shirye-shiryen miƙa sh ga rundunar ’yan sandan jihar, domin ci...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kira ga tsayar da sallah wani aiki ne na wajibi ga hukumomin da’awar addini da malamai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Kira ga tsayar da sallah da koyar da ita, da bayyana ma’anonin da ke cikinta, da riko da ita, wani aiki ne na wajibi da ya rataya a wuyan hukumomin da’awar addini da malamai da ma’abuta addini. Dole ne a yi amfani da hanyoyin zamani domin watsa wannan fanni. A cikin sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike ga zaman taron cibiyar karfafa tsayar da sallah karo na 32 ya bayyana cewa: Taron karfafa tsayar da sallah yana daya daga cikin mafi...
    Kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ta bayyana cewa: Abin da aka cimma na yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba kyauta ce daga kowa ba Kungiyar Jihadul-Islami ta Falastinu ta bayyana cewa: Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da makiya yahudawan sahayoniyya ba kyauta ce daga kowa ba. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar da safiyar yau Alhamis din nan, kungiyar Jihadul -Islami ta kara da cewa: Ko da yake ba su musanta yunkurin kasashen Larabawa da na kasa da kasa ba, amma suna jaddada gagarumin sadaukarwar da al’ummar Falastinu suka yi da kuma jajircewa da dogewa wajen kalubalantar makiyansu a fagen daga. Bayanin ya ci gaba da cewa: A wannan lokaci na tarihi, al’ummar Falasdinu ba za...
    An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro.   Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma.   Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin.   Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27.   A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin...
    Hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Kano ta sanar da fara aiki a hukumance da sabon kwamandan hukumar, Kwamanda Idris Mohammed Lawal.   Kwamanda Lawal ya karbi ragamar shugabancin hukumar ta Kano ne biyo bayan tura shi da hukumar FRSC ta yi a ranar 3 ga watan Oktoba.   Ya gaji kwamandan Corps MB Bature, wanda ya yi ritaya a kwanan baya bayan ya kamala shekarun sa a aikin gwamnati.   Kafin sabon mukamin nasa, Lawal ya taba zama shugaban aiyuka na shiyyar a hedikwatar hukumar FRSC shiyya daya da ke Kaduna.     A jawabinsa na farko, sabon Kwamandan sashin ya nuna godiya ga rundunar Corps Marshal da Hukumar FRSC bisa amincewarsu. Ya yi alkawarin sadaukar da aikin...
    Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Zamfara, Abdulrahman Muhammad Tumbido, ya yabawa gwamna Dauda Lawal bisa jajircewar sa wajen tallata jihar Zamfara a matsayin cibiyar zuba jari.   Kwamishinan, wanda ya bi sahun gwamna Lawal a wata tawaga ta hukuma zuwa bikin baje kolin kasuwanci da zuba jari na Canada–Africa da aka gudanar a Toronto, Canada, ya ce halartar gwamnan ya bude wa jihar sabbin damammaki na kasuwanci da bunkasar tattalin arziki.   A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar, Jamilu Bello, Tumbido ya fitar, ya tabbatar da cewa ma’aikatar kasuwanci da masana’antu za ta ci gaba da bin diddigin ayyukan hadin gwiwa da yarjejeniyoyin da aka kulla a wannan tafiya.   A cewarsa, Gwamna Lawal ya baje...
    Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara.     Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da  cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin.   Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun.   Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin...
    Falasdinawan da ke Gaza da Isra’ila ta shafe sama da shekara biyu tana kai wa hare-hare sun nuna jin dadi da farin ciki bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin kawo karshen yakin. Yayinda labarin yarjejeniyar ya yadu a cikin yankin da aka kewaye, mazauna Khan Younis a kudancin Gaza sun fito tituna suna murna da fatan wannan zai zama farko zaman lafiya daga hare-haren Isra’ila. Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya Majalisa ta yi watsi da zargin Amurka na yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya “Alhamdulillah da wannan dakatar da fada, karshen zubar da jini da kashe-kashe… duk Gaza na cikin farin ciki,” in ji Abdul Majeed Abd Rabbo, mazaunin...
    Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci. Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar. SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu Mai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Laraba cewa dole ne a rahoton bai duba yanayin tsarin auna talauci na duniya ba. “Duk da cewa Najeriya na daraja...
    ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinBabban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025Daga Birnin SinYawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025
    Dalibai da malaman Jami’o’i a kasar Burtania sun bar ajujuwansu don halattar ganganmi a cikin jami’o’insu, na goyon bayan al-ummar Falasdinu da kuma yin tir da gwamnatin kasar saboda goyon bayan da take bawa HKI a kissan kiyashi, wanda ya kai shekaru biyu kenan a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa  zanga zangar bata takaita a jami’o’in birnin London kadai ba, sai dai an gudanar da su a manya –manyan biranen kasar duk tare da gargadin jami’an yansandar kasar kan cewa an haramta zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kasar. Sauran biranen da aka gudanar da gangamin dai sun hada Glasgow, Manchester, Bristol, Sheffield da Edinburgh. Daliban da kuma malamansu suna rera taken “Yanci ga Falasdinu...
    Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta. Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara. ‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’ Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen. “Mun samu kiran...
    Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu Sarayal-Quds ta bayyana cewa: Fursunonin mamaya ba za su ga hasken rana ba har sai an sharuddan Falasdinawa Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu, sun jaddada cewa: Fursunonin mamayar Isra’ila ba za su ga hasken rana ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da musayar ra’ayi da yahudawan sahayoniyya da suka kuduri aniyar kawo karshen yakin Gaza. A cikin wata sanarwa da dakarun Sarayal-Quds suka fitar, sun jaddada cewa su da dukkanin bangarorin gwagwarmaya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen samar da hanyar kawo karshen yakin Gaza da kuma wahalhalun da Falasdinawan suke ciki. Har ila yau, sun tabbatar da cewa: “Makaman ‘yan gwagwarmaya makamai ne da aka...
    Falasdinawa 12 ne suka yi shahada a Gaza yayin da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan yankin a yau Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da zafafa matakan soji a zirin Gaza duk da kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na Isra’ila ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a zirin Gaza. Majiyoyin lafiya a asibitocin Gaza sun watsa rahoton cewa: Hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 12 da suka hada da hudu a birnin Gaza da bakwai a Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza, yayin da wani Bafalasdine daya ya yi shahada a yankin tsakiyar Falasdinu....
    Ya gargaɗi masu aikata laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci, inda ya bayyana cewa waɗanda aka kama tuni aka miƙa su kotu.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Labarai‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025LabaraiCika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya October 7, 2025
    Dubban mutanen kasar Moroko ne su ka fito kan titunan birnin Rabat domin yin Zanga-zangar nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu da HKI take yi wa kisan kiyashi. Mahalarta Zanga-zangar sun hada lauyoyi, dalibai, kungiyoyin fararen hula da sauran mutanen gari, suna dauke da tutar Falasdinu, tare da kuma da bayar da taken: “Yanci ga Falasdinu, da yin kira da a shigar da kayan agaji a cikin yankin na Gaza. Bugu da kari, masu Zanga-zangar sun yi gangami a bakin ginin majalisar dokokin kasar. Mutanen sun nuna rashin amincewarsu da  halin da mutanen Gaza suke ciki, tare da yin kira da a kawo karshensa. Mahalarta Zanga-zanagr dai sun fito ne daga biranen Tangier, Casbalanca da Feiz, da kuma wasu garuruwa...
    Hukumar kula da yan gudun hijirar a majalisar dinkin duniya ta jinjinawa kasar Iran game da kokarin da tayi wajen kulawa da miliyoyin yan gudun hijira kasar Afghanistan , da suka zauna a kasar na tsawon shekaru, Babban darakta na hukumar ta IOM shi ne yayi wannan bayani ga Mohammad Batgae mtaimakin ministan harkokin cikin gidan kasar iran a birnin janeva a jiya litinin, a wani taro da suka gudanar a bayan babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 76 da hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya take gudanarwa. Ana sa bangaren bathaei babban jami’I na kasar Iran ya bayyan yadda jamhuriyar musulunci suka bada kula ta musamman  ga dubban yan gudun hijiran kasar ta Afghanistan...
    Tun bayan harin 7 ga watan Oktoba, 2023, da mayaƙan Hamas suka kai wa Isra’ila wanda ya hallaka sojoji sama da 60 , Isra’ila ta fara luguden wuta a Gaza.Tun daga wannan lokacin, yankin ya zama wurin tashin hankali da yunwa, inda mutane da dama ke mutuwa a kowace rana.Tags: FalasɗinawaGazaHamasIsra'ilayaƙiShareTweetSendShare Sadiq Related Kasashen KetareMe Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa? 3 days agoKasashen KetareWadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa? 1 week agoKasashen KetareBirtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa 2 weeks ago
    Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
    Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
    Wani saksmkon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar dimokuradiyya ta Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Isra’ilawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin Gaza, tare da bayyana hadarin da fursunoni ke fuskanta. Wannan adadi na kashi 66% ya karu da kashi 13% a kan sakamakon da aka fitar a shekara guda da ta gabata lokacin da aka yi musu tambaya iri ɗaya. Sakamakon  ya kuma nuna cewa kashi 45% na Isra’ilawa sun yi imanin cewa ya kamata Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yi murabus nan da nan kafin karshen yakin, tare da dora masa alhakin abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Sakamakon ya nuna...
    Kungiyar Jihadul-Islami ta jaddada cewa: Za ta ci gaba da kare kasarsu da kuma neman kai wa ga dukkan hakkokin al’ummarsu Kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ta tabbatar a yau Litinin din nan cewa: Za ta ci gaba da daukar alkawarin kare al’ummarsu da wurarensu masu tsarki har sai sun kai ga samun ‘yancin kwato kasarsu, tare da cikakken hadin gwiwa da dukkanin dakarun gwagwarmayar Falastinawa karkashin jagorancin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ta bayyana cika shekaru 38 da gudanar da jihadi da kuma cika shekaru biyu da harin daukan fansa na “Ambaliyar Al-Aqsa”, kungiyar ta ce: Shekaru 38 da kaddamar da Harkar Jihadin Musulunci ta Falastinu ta zo daidai da cikar shekaru biyu na...
    Babban mai shiga tsakani na kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas Khalil Al-Hayya ya isa Masar, inda ya jagoranci tawagar da ake sa ran za ta fara tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Isra’ila, a cewar kungiyar. Hamas ta ce za a fara tattaunawar ce kan “hanyoyin tsagaita bude wuta, da janye sojojin mamaya, da musayar fursunoni.” yau Litinin ne aka tsara tawagar Isra’ila za ta isa wurin, kamar yadda ofishin Benjamin Netanyahu ya bayyana, a wani bangare na tattaunawar. Su ma wakilan Amurka, Masar da kuma Qatar zasu halarci tattaunawar a matsayinsu na masu shiga tsakani. A cewar majiyoyin diflomasiyya, tattaunawar tsakanin Isra’ila da Falasdinawa za ta gudana ne a birnin Sharm el-Sheikh. Ana sa ran tattaunawar za...
      Shugaba Mahama ya kuma yabawa kamfanin Greenhouse International Development Group saboda irin ayyukan da ya gudanar a kasar tun daga shekarar 2011 da ya shiga Ghana, ciki har da yankin masana’antu na Bright International Industrial Park da masana’antu da dama masu samar da kayayyaki a farashi mai rahusa ga ‘yan kasar da samar da gurabun ayyuka kimanin 10,000 tare da zuba jari a bangaren aikin gona da na gine-gine. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Talatar da ta shude ne dai aka ga gawar jakadan kasar Afirka Ta Kudu a kasar Faransa Nathi Matherhwa, da aka nuna cewa ya fado daga kan benen Hotel hawa na 22. Babban sufeton ‘yan sanan kasar ta Afirka Ta Kudu Fenni Masemola ya sanar da aikewa da tawagar masu bincike su biyar da za su hada karfi da takwarorinsu na Faransa domin gudanar da bincike akan musabbabin mutuwar jakadan. A ranar Litinin din makon da ya shude ne dai matar jakadan ta sanar da cewa ya bace, lamarin da ya bude kofar bincike da ta kai ga ganin gawarsa a kasan Hotel din Hyatt Regency a ranar Talata. Wani jami’in ‘yansanda Faransa ya fada wa manema labaru...
    Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi. Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan yahudawan kudin da sun kai Shakel miliyan 25 wanda shi ne kwatankwacin Dala miliyan 7.54, ta hannun lauyoyinsu. Haka nan kuma jaridar ta ce hukumar dake kula da haraji da ke karkahsin ma’aikatar shari’a ce ta aiwatar da raba kudin a matsayin abinda su ka kira diyyar ayyukan t’addanci.! Jaridar ta kuma ce tun a 2019 ne wadannan ‘yan sahayonioyar su ka bukaci a biya...
    Sanarwar ta ƙara da cewa: “A cikin baƙin ciki muke alhinin rasuwar Ambasada Muhammad Jabbi Maradun, fitaccen dattijon jiha kuma ɗan jiharmu ta Zamfara na gaskiya.   “An haifi Jakada Jabbi ne a ranar 12 ga Nuwamba a shakrar 1943, a Ƙaramar Hukumar Maradun.   “Ambasada Maradun ya taba zama jakadan Nijeriya a ƙasar Tunisia daga 1999 zuwa 2003.   “Ya yi fice a yunƙurin samar da jihar Zamfara.   “Bayan kafuwar jihar Zamfara, Ambasada Jabbi ya shiga gwamnatin soja ta farko a ƙarƙashin Kanar Jibril Bala Yakubu, inda ya riƙe muƙamin kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido.   “Ayyukan sa na siyasa sun haɗa da jam’iyyun GNPP, NPN, da NRC, kuma ya kasance mai ruwa da tsaki a...