Aminiya:
2025-12-09@18:57:57 GMT

An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai

Published: 24th, October 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan jihar Yobe ta ce ta cafke wani shugaban mazaba na jam’iyyar APC a karamar hukumar Karasuwa bisa zarginsa da hannu a kisan wata mata.

Rundunar ta ce ta samu nasarar ce a binciken da take yi kan wata gawar da aka gano a kusa da Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa a makon da ya gabata.

Gwamnan Neja ya ba dukkan iyalan wadanda suka kone a gobarar tankar mai N1m Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027

A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ’yan sanda daga sashin karamar hukumar Bade sun kama wani mutum mai suna Abdulmumini Garba, mai shekaru 60, dangane da mutuwar matar mai suna Falmata Abubakar, ‘yar shekara 45 da haihuwa.

Rahoton ya nuna cewa wanda ake zargin mazaunin Gasma ne a karamar hukumar Karasuwa, kuma yana rike da mukamai biyu: Sakataren APC na Mazava a Karasuwa da Sakataren Kasuwar Gwari a Gashuwa.

‘Yan sanda sun ce an kama Garba ne bayan gudanar da bincike mai zurfi da kuma kokarin leƙen asiri da suka yi a ranar 17 ga watan Oktoba, 2025.

Lokacin da ake masa tambayoyi, Garba ya amsa cewa shi ne ya kashe Falmata Abubakar a cikin motarsa, bayan samun sabani tsakaninsu.

An bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga bukatar marigayiyar na neman taimakon kuɗi don tallafa wa sana’arta, wanda ya rikide zuwa tashin hankali da ya haifar da mutuwarta.

Bayan mutuwar, wanda ake zargin ya ce ya jefar da gawar a daji da ke kusa da wajen da misalin ƙarfe 10 na dare, inda daga bisani aka gano gawar.

Rundunar ’yan sanda ta bayyana wannan ci gaba a matsayin shaida ta ƙwazo da dabarun tattara bayanai da suka taimaka wajen gano wanda ake zargi cikin gaggawa.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya jinjina wa jami’an sashin Bade bisa ƙwarewa da jajircewarsu, tare da jaddada aniyar rundunar na ganin an samu adalci.

CP Ado ya tabbatar wa da jama’a cewa za a kammala bincike cikin tsanaki, sannan a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baghaie ya yi tir da kashe fararen hula a garin Kalogi dake Jahar Kurdufan na Sudan.

Bugu da kari kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kawo karshen abinda yake faruwa a wannan kasar.

Kusan mutane 80 ne fararen hula da rabinsu kananan yara ne aka kashe a wasu jerin hare-hare da jiragen sama marasa matuki. Wuraren da aka kai wa harin dai sun hada makarantu na kananan yara da asibitoci.

Ana zargin kungiyar nan ta kai daukin gaggawa ( RSF) da kai wannan harin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Macron Na Faransa Ya Yi Wa Najeriya Alkawalin Taimakawa Akan Matsalolin Tsaro December 8, 2025 Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka  Teke Fuskanta December 8, 2025 Majid Majidi Na Iran Ya Sami Kyauyar Girmamawa Daga Cibiyar Fina-finai Na “Eurasia Dake Kasar Rasha December 8, 2025 Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa December 7, 2025 Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi) December 7, 2025 Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’ December 7, 2025 Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila December 7, 2025 Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167 December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kamfanin Mangal ya kori direba kan dauko yara 21 da aka kama a Kogi
  • ‘Yan Bindiga 18 Sun Muta a Wata Arangama da Rundunar Operation Fansan Yamma
  • An kama tsohon fursuna ya je fashi da bindiga AK-47
  • Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan
  • Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin
  • An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja
  • Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini
  • Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167