Sojoji sun tallafa wa mutanen Yobe da N23m bayan harin kuskure
Published: 18th, October 2025 GMT
Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta bai wa mutanen garin Buhari da ke Karamar Hukumar Yunusari a Jihar Yobe, tallafin Naira miliyan 23 tare da alƙawarin gina rijiyar ruwa mai amfani da hasken rana.
Wannan tallafi ya biyo bayan wani harin kuskure da jiragen yaƙin rundunar suka kai a watan Satumba 2021, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane takwas da jikkata wasu 30.
Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritay), wanda shi ne mai bai wa Gwamna Buni shawara kan harkokin tsaro, ya bayyana cewa wannan tallafi ya nuna tausayin gwamnati da rundunar sojan sama ga al’ummar garin.
Ya ce, tun bayan faruwar lamarin, gwamnan Yobe Mai Mala Buni da Gwamnatin Tarayya suna ƙoƙari wajen taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
A madadin Babban Hafsan Sojin Sama, Komando U.U. Idris na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), ya ce rundunar ta bayar da Naira miliyan 23 ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma naira dubu 500 ga kowane mutum daga cikin waɗanda suka jikkata.
Ya ƙara da cewa, rundunar ta yi wa wadanda suka rasu addu’a, tare da fatan Allah Ya kiyaye faruwar irin hakan a nan gaba.
A nasa jawabin, Alhaji Ali Lawan, wanda ya wakilci al’ummar garin Buhari, ya gode wa rundunar Sojin Sama bisa wannan taimako.
Ya kuma roƙi jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen yaƙar ’yan ta’adda, domin har yanzu yankin na fuskantar barazanar tsaro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hari
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe
Gwamnatin Yobe ta bayyana cewa aƙalla mutane 9,854 ne ke ɗauke da cutar AIDS a jihar, kuma dukkaninsu na karɓar maganin ceton rai.
Hukumar ta tabbatar da cewa waɗannan marasa lafiya suna rayuwa cikin ƙoshin lafiya, tare da rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Jihar Yobe (YOSACA), Dakta Jibril Adamu Damazai, ne ya bayyana cewa Yobe na da mafi ƙarancin adadin masu ɗauke da cutar a ƙasar nan da kashi 0.4%, inda ya danganta hakan da dabarun yaƙi da cutar da ake aiwatarwa a jihar.
“Ba mu tsaya a kan wannan nasara ba, muna ƙara ƙoƙari don rage yawan kamuwa da cutar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 120 wajen sayen kayan gwaji, abin da ya bai wa ƙungiyoyi damar gano mutanen da ba a san suna ɗauke da cutar ba a cikin al’umma, domin a ba su magani.
A cewarsa, Yobe na kan gaba wajen daidaita dabarun yaƙi da cutar AIDS, musamman ganin yadda ake samun sauye-sauye a kuɗaɗen da ake kashewa a duniya.
Dakta Damazai ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen samar da magungunan ƙwayar cutar HIV a cikin gida.
Ya yaba da jajircewar gwamna Mai Mala Buni, wanda ya ƙara kuɗaɗen da ake bai wa hukumar kula da cutar AIDS da kashi 400%, tare da samar da katafaren ofis na dindindin ga hukumar.